GAME DA

RAYUWAR IMAM MAHDI (A.S.)

 

 

MUUTIZAR IMAM MAHDI (ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)

 

ใฺฬาษ วแวใวใ วแใๅฯํ

 

Hamidu… Wannan kuma meye…?

Na fadi wannan da ta`ajjubi yayin da na ga da na Hamidu yana sanye da tufafi na musulunci… sannan yana kokarin daukan takobi da hanunsa na dama…

Sai ya amsa mini tambayata ya ce:

Baba, ina so ne in yi irin shigar wadannan mutane Salihai, muminai, wadanda suke daukan takubbansu… su fita bayan gari a ranekun juma`a suna sauraran bayyanar Imam Mahdi(ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)… domin su zamo daga cikin rundunarsa da mataimakansa, a wajen kawar da zalunci da ja`irci a doron kasa… Kuma a cika ta da adalci da daidaitawa…

Maganar da na Hamidu ta sa na zurfafa cikin littafan tarihi… sai ga lamuran tarihin suna bayyana a gareni,

har na zama ina tunani ni kadai ina cewa:

Hakika duniya ta kasance tana jiran ketowar alfijir, kuma har yanzu duniya bata gushe ba tana, jira…irin alfijir din da ya keto yayi haske saboda hasken fuskarsa, ya kuma haskaka tun daga wurin haihuwarsa har ya zuwa sararin samaniya… mala iku kuma suka sauko suna shafa kansa da fuskarsa da sauran jikinsa da fukafukansu… hakika shine jinjirin nan da ya fito daga cikin mahaifiyarsa, daidai lokacin da jikinsa ya taba kasa sai yayi sujjada ga Allah… wannan abu kuwa ya sa mahaifiyarsa ta yi mamakin irin wannan dan da aka haifa da kaciyarsa, ga shi ta haife shi cikin tsabta da tsarki, ko digon jini bai digo ba a tare da shi, saboda haka mahaifiyarsa bata ga wata alama ta jinin biki ba… yayin da mahaifiyarsa take cikin wannan hali tana lura da danta, sai ta ga ya dago yatsansa (manuniya) zuwa sama sannan yayi atishawa… sai Ya ce:

“Alhamdu lillahi rabbil Alamin” godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai-ya ci gaba da cewa:[Wa sallallah ala Muhammad wa alihi… abdan zakiran lillah gaira mustankifin wa la mustakbirin]… Kuma  tsira da aminci su tabbata ga Muhammadu da zuriyarsa bawa mai ambaton Allah, ba tare da daga kai ko girman kai ba…

Wannan da shine Imam Hujja bin Hasan Al-Mahdi(ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)… Hakika mahaifinsa Imam

Hasan Al-Askari(A.S.) ya kasance ya samu umarni da cewa ya boye shi kuma ya suturce shi daga idanuwan makiya, da mahassada, da azzalumai, wadanda zasu yi dukan kokarinsu domin su ga sun kashe shi tun daga lokacin da aka haife shi, saboda ko dama can sun kasance suna jiran wannan lokaci sabili da yawan ruwayoyi da aka ruwaito daga Manzon Allah(S.A.W.A.) dangane da cewa shi Mahdi daga `ya`yan Imam Husain(A.S.) yake, kuma cewa zai bayyana domin ya cika kasa da adalci da daidaito bayan an cika ta da zalunci da ja`irci… kuma Allah Madaukakin sarki ya yi nufin ya kare shi daga makiya ba tare da sun same shi ba… to ganin cewa mahaifinsa yana jin tsoron kada maikansa su same shi… don haka haihuwarsa ta zama ta buya wa yawancin mutane… kamar yadda kuma Imam Sadik(A.S.) ya fada cewa: Hakika Imam Mahdi (wato sahibuz zaman) yana da wata buya wanda babu makawa daga gareta… saboda wani sababi wanda ba a yi iziznin ku san shi ba… kuma hikimar dake tattare da buyansa ba zata fito fili ba sai bayan bayyanarsa… to tun da Allah Ta`ala mai hikima ne cikin aikinsa, mun gaskata cewa dukkan ayyukansa yayi su ne bisa hikima, koda kuma mu bamu san hikimar ba…

Baba, na ga ka bace cikin tunani mai zurfi…?!

Hamidu ya fadi wannan magana ne a halin yana mamaki… sai na yi masa murmushi na ce: Me ya sa kake so ka yi irin shigarsu ya da na…?

Shin baka so ne ka zamo da gaske kana daga cikin sojoji da kuma mataimakan Imam Mahdi(ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)…?

Sai Hamidu ya amsa da sauri:

Ina so har birnin zuciyata, in zama soja kuma mai taimakon Imam Mahdi(A.S.).

To ta yaya zaka taimaka masa, kuma ta wanne hanya zaka zama sojansa…

Da wannan takobi zaka zama sojan Imam Mahdi, mai taimaka masa…?

Baba akwai wani abu ne banda takobi…?

Hamidu yana fadin wannan magana a halin yana mamaki… Sai na amsa masa ina murmushi:… ai kai ma ka san cewa wannan zamanin namu zamani ne na jiragen yaki, da makamai masu linzami da tankokin yaki da sauransu, wato makamai iri-iri na kare dangi… to menene takobi zai yi a tsakanin wadannan makamai…?!

Hamidu sai yayi shiru na dan lokaci, sannan sai ya ce cikin al`ajabi: gaskiyarka ce baba…!! Amma kuma ai hadisai sun nuna cewa Imam Mahdi(A.S.) zai bayyana da takobin kakansa Imam Ali bin Abi Talib(A.S.)…?

Wannan daidai ne da na, saidai kuma akwai mu`ujizozi da zasu bayyana tare da bayyanar Imam Mahdi(A.S.) tamkar irin mu`ujizar Annabawa(A.S.)… misali a zamanin Annabi Musa(A.S.) sihiri ya zamanto wani abu ne mai muhimmanci a mulkin Fir`auna ga kuma irin rundunar yaki da yake da su… su muminai da suka yi Imani da Annabcin Musa bin Imran(A.S.), basu taba tunanin cewa Annabi Musa zai zo da mu`ujiza wadda za ta iya fuskantar sihiri da tsubbu ba, daga bisani kuma mu`ujizarsa ta zam ta dimautar da magoya bayan fir`auna… abinda ya faru shine sai Allah Ta`ala ya sa sandar Annabi Musa ta zama macijiya mai girma, ta kuma hadiye dukkan abinda masu sihirin Fir`auna suka zo da shi na sihiri, wannan abu kuwa ya sanya wadannan masu sihirin Fir`auna sun rasa abin yi da wannan mu`ujiza ta Annabi Musa(A.S.), har suka yi imani da Allah da kuma Annabicin Musa(A.S.)… Sannan daga mu`ujizozin Annabi Musa(A.S.) shine cewa Allah ya tsaga hanya a tsakiyan ruwa ga Annabi Musa(A.S.) da jama`arsa da suka yi imani da shi, suka tsallake kogi lafiya ba abinda ya same su, a yayin da Allah ya rufe wannan hanyar akan Fir`auna da mutanensa, suka mace a cikin ruwa… idan kuma

muka duba zamanin Annabi Isa(A.S.) zamu ga cewa… a lokacin jinya da Kuma likitanci shine ya fi shahara gami da bada labari kan gaibu… domin a zamanin zaka tarar cewa likita zai iya raya matacce wanda jikin sa bai yi sanyi ba, wato wanda ya mutu yanzu… Saboda haka sai Allah ya aiko Annabi Isa bin Maryam da ilimi wanda ya tsere nasu gaba daya, har yayi musu kalubale: yana cewa Ni ina warkar da makaho da kuturu-da sauran wadanda suka kamu da cututtuka wanda suka ki ci suka ki cinyewa… ba kuma da magani ba, a`a da shafa kawai, wato idan ya shafi mara lafiya da hannunsa shike nan… ya ci gaba da cewa: kuma ina raya matacce har da wanda ya diddige… kuma ina iya yin sifar tsuntsu da yumbu [Tabo] sai in hura shi sai ya zama tsuntsu mai rai da izinin Allah…

Ta wannan hanya ce Annabi Isa(A.S.) yayi galaba akan kafiran zamaninsa, duk da makaminsu… a yayin da Allah madaukaki ya aiko Annabinmu Muhammadu(S.A.W.A.), a zamaninsa kuma balaga da fasaha sun kai tsororuwarsu… saboda haka ne suka zama sune mu`ujizar Al-Kur`ani wanda mashahuran masana ilimin adabi na zamanin suka rasa ta cewa saboda ganin irin balaga da fasaha ta Al-Kur`ani, har suka sakankance cewa ba dama ace wani ne ya aiko da Al-Kur`ani idan ba Allah ba… to tun da yake Annabinmu Muhammadu(S.A.W.A.) shine karshen  Annabawa,

Kuma sakonsa shine karshen  sakonni… don haka ne Allah ya sanya Imamai Ma`asumai daga zuriyarsa, domin su zamo masu lura da sakon addinin musulunci kuma su zama masu kare shi… dada su zama masu yada iliminsa da tushensa a tsakanin mutane bayan Manzo Muhammadu(S.A.W.A.), Imam Ali bin Abi Talib(A.S.) sai ya zamo shine farkonsu (wato farkon Imamai) na darshensu kuwa shine Al-Hujja bin Hasan Al-Mahdi(A.S.) wanda ake sauraro… Hakika mun karanta tarihin Imamanmu(A.S.) masu shiryarwa… mun ga yadda suka sha nau`i nau`i na azaba, ba kuwa don komai ba sai domin su kare wannan sako na musulunci mai tarin albarka har suka bada rayukansu domin su fanshi wannan addinin… domin sune suke kan gaskiya, to wannan runduna ta gaskiya ita ta tsaya ta fuskanci runduna ta bata, a bayan rasuwar Ma`aiki mai daraja Muhammadu(S.A.W.A.)… kuma duk cikin wadannan Imamai babu wanda Allah ya Kaddara cewa zai buya face Imam Mahdi(ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)… la`alla a waccan lokacin shi`arsu da suka zama runduna ta gaskiya, basu zama sun ginu ta hanyar ilimi da zamantakewa ba, ta yadda zasu iya tsayawa su fuskanci jahilci da tsubbu da zalunci… don haka ne Imamai(A.S.) suka gamu da bala `o`I da masifu…

har sai da shi`ah suka zama sun hade sun zama tare suna yada ilimi, kuma suko zama cibiya wanda take watsa ilimi gabas da yamma aia sanadiyyar maruwaita da kuma amintattun mabiya Imamai… to da haka ne suka shiga kare karantarwar zuriyar Manzo(S.A.W.A.) ta yanda ya zama koda babu Imam Ma`asumi zasu iya ci gaba da aikin ilimi ballantana ga irin hadarorin dake fuskantar Imam a lokacin daga koina, kuma ta bangarori daban-daban,… don haka Allah ya kaddara wa Imam Mahdi(A.S.) buya wato gaiba, domin ya bayyana a lokacin da ya dace, ya cika kasa da adalci da daidaito… bayan ta zama an cika ta da zalinci da ja`irci…

Nagode baba… Saidai baka gaya mini irin daramat da zata bayyana tare da Imam Mahdi(A.S.) ba…?

-  Da ma tun da aikin Imam Mahdi(A.S.) shine ta cika wannan kasa da adalci da daidaito bayan an rigaya an cika ta da zalinci da ja`irci… Saboda haka datamarsa ta farko zata zamo cewa zai fito da wani  makami wanda a sanadiyyarsa dukkan makaman wannan zamanin ko na zamanin da zai biyo baya zasu gaza aiwatar da wani abu…

Kamar yadda masu sihirin Fir`auna suka gaza aiwatar da wani abu a gaban sandar Annabi Musa(A.S.)… Kamar yadda kuma Annabi Isa(A.S.) shima yayi galaba akan likitocin zamaninsa a sanadiyyar mu`ujizar sa, likitocin da suka kai makura a ilimin likitanci na waccan zamani… Har wa yau kuma, kamar yadda masana balaga da fasaha suma suka rasa ta cewa a gaban mu`ujizar Al-Kur`ani mai girma… wanda aka saukar wa Annabinmu Muhammad(S.A.W.A.), saboda haka ne hadisai ke cewa makamin Imam Mahdi(A.S.) ya san makiya Allah sai kawai ya kashe su… Kuma ya san mataimakan addinin Allah, sai ya bar su… Kuma dukkan sauran makamai da ake da su, zasu zama tamkar hoto ne a gabansa… to wannan ishara ce ga cewa Imam Mahdi zai yi amfani da makami wanda zai dakatar da dukkan sauran makamai da kuma dukkan sauran kayan yaki masu harbuwa… to da wannan sai rundunonin abokan gaba su gaza a gabansa da su da shuga banninsu, su zama cikin wani hali na tsoro da fargaba wanda tarihi bai taba sanin irinsa ba,… dangane kuma da takobin da Imam Mahdi(A.S.) zai bayyana da shi wannan takobin shine

wanda Jibrilu(A.S.) ya sauko da shi daga sama… ya ba wa Ali bin Abi Talib(A.S.) yayi amfani da shi a yakokin musulunci da suka rabe tsakanin karya da gaskiya, wanda bayan haka ya zama abin gado mai muhimmanci da Imamai suka yi ta gadonsa… to don haka Imam Mahdi(A.S.) zai dauki wannan takobi domin ya tabbatar da dangantakarsa ga Manzon Allah(S.A.W.A.), sabili da tsawon zamanin da ke tsakanin sa da mahaifinsa… tare da kuma cewa zai bayyana a sifa ta mutum mai shekara arba`in da hai huwa…hakanan saboda ya nuna cewa ya zo ne domin ya sabunta musulunci ba ya zo bane da sabon addini kamar yadda wasu mutane zasu yi da`awa… Kuma zai dau wannan takobi ne domin tubarruki, domin shine takobin da ya bude hanya ga musulunci, daga bisani ya raya jihadin kakansa Ali bin Abi Talib(A.S.) wanda dukkan rayuwarsa ta kasance sadaukarwa a tafarkin gaskiya…

Sai da na Hamidu ya fara ajiye takobin daga hannunsa, yana cewa: ashe kenan baba bamu bukatar wannan takobin idan Allah ya kaddara mu zama cikin runduna da mataimakan Imam Mahdi(ALLAH YA GAGGAUTA BAYYANARSA)

عنوان الکتاب