GAME DA

RAYUWAR IMAM HADI (A.S.)

 

HASKEN MADINA

 

δζΡ ΗαγΟνδΙ

 

Hakika wannan gwamna na Banu Abbas la ΰnanne ne… a wannan zamani namu babu wata halitta ta Allah mai dacin hali kamarsa…

A sanadiyyarsa dukkan abinda muke ciki ya afku…

Wadannan maganganu da wasunsu sun zama suna isowa ga kunnuwana daga littafin tarihin da ya gabata… maganganu ne da ke tare da kuka da ihu da juyayi… wanda harsunan mata da maza, yara da matasa, ke furta su, harsunan da kuka da ihu ya gajiyar da su… Sai suka zam suna fito da muryoyi masu yankewa marasa taushi… wanda hakan ya sa ni kuma na shiga cikin tunani mai zurfi a yayin da nake kokarin gano abinda ke faruwa… har zuwa lokacin da na kai inda tarihi ya bude mini. Shafinsa sai na sami kaina, a gaban masallaci a Madina, bakin ciki da bacin rai ya lullube shi ya kuma zauna a zukatan mutane tamkar wani dutse mai nauyi… wannan hali ya bayyana ga mutan Madina yayin da nake lura da fuskokinsu…
Wanda hawaye ya canja su… Sai na hangi wani tsoho a tsakaninsu yana zaune kusa da kofar masallacin… sai na taho inda yake, amma ina tunanin in yi magana da shi ko kada in yi… koda yake dai raina ya fi son in yi masa magana wato in tambaye shi… amma irin halin da suke ciki na bakin ciki ya sa ina shakkun tambayarsa… yayin da nake cikin wannan hali… Sai na ga tsohon yanai mini ishara da hannunsa, yana cewa: yaka da na ka fadi abinda ke tare da kai, kada ka yi shakku… idan kana da wata bukata… za mu biya maka ita in Allah ya yarda… maganarsa ta sa rai na yayi dadi… Sai na zauna kusa da shi, farin ciki ya lullube ni, a yayin nan… Sai na ce masa:-

Shin ba nan bane Madinatul Munawwara kuma wannan ba shine masallacin Annabi ba…?

Sai hawaye suka shiga zubo masa yana cewa: haka yake da na… Kuma Madina za ta ci gaba da zama Munawwarah (wato haskakakka) duk kuwa da kokarin da azzalumai ke yi tun tsawon lokaci domin su gusar da haskenta…

Na ga alamun cewa akwai wani abu na bakin ciki da ya afku gareku… wanda ya sanya ku cikin irin wannan hali da kuke a yanzu…

Sai tsohon ya mayar mini da amsa a halin yana mai bakin ciki ya ce: wani bakin gajimar ei daga Banu Abbas ne ya rufe mana hasken wata daga zuriyar Manzon

 Allah(S.A.W.A.) wanda da yake zaune a tsakanin mu, kuma dukkan gidajen Madina sun kasance suna amfana daga haskensa… babu wani fakiri a Madina face ya wadata shi... Kuma babu wani mara lafiya a Madina face ya sami Imam(A.S.) kusa da shi… ya kai masa ziyara har gidansa… Kuma hakika tausayinsa da kyautayinsa, ya game dukkan bangarorin rayuwarmu, yana taya mu farin ciki a duk lokacin farin cikinmu, yana kuma taimakon mu a duk lokacin da muka shiga wahala… ya kasance yana agaza wa babba da yaro a cikinmu… yana kuma daukan nauyin taimaka wa marayu da matan da mazajensu suka rasu… ya mallaki zukatanmu da ayyukansa…

Sai wannan tsoho yayi ishara da hanunsa zuwa masallacin Annabi… ya ci gaba da magana yana cewa: da wannan masallacin ya kasance makaranta ne wadda ke haskaka da hasken iliminsa… mutane sun koyi darusa na kyawawan dabiω daga wannan makarantar, kuma suka sami tarbiyya irin ta musulunci… malamai da masana fikihu da maruwaita, sun amfana daga iliminsa wanda ya samo daga iyayensa, wanda suka haskaka rayuwar bil Adam da hasken ilimi da imani…

Na ji mutane suna laΰntar wani mutum mai suna Abdullah bin Muhammad… Kuma sun sifanta shi da cewa mutumne mai dacin hali… sun Kuma ce shine ummul abaìsin wannan abinda ya faru…

Wannan gaskiya ce… an turo mana gwamna wato Abdullah bin Muhammad daga halifa Mutawakkil domin ya zama mai tsayar da Salla, kuma mai lura da shaΰnin yaki…yayin da Abdullah ya ga yadda mutane ke son Imam Ali bin Muhammad Al- Hadi(A.S.) da yadda suke daukaka shi,… Sai zuciyarsa ta zama ta cika da fushi da hassada… to tun daga lokacin ya zam yana nufin Imam da keta da cutarwa… to bai tsaya nan ba har sai da ya kai sukan Imam wajen halifa Mutwakkil… Sai ya gaya wa Mutawakkil cewa mutane suna daukaka Imam Ali Al-Hadi suna kuma ba shi kudade masu yawa… lallai Imam na sayen makamai domin yayi yaki da daula ya kifar da hukumar Banu Abbas…

To yayin da Imam ya sami labarin kai sukarsa da wannan lalatacce yayi… da irin makircin da ya kulla masa sai yayi kokatin kore wannan zargi da aka yi masa a wajen Mutawakkil, domin ya san raΰyin wadannan halifofin Banu Abbas dangane da Imaman Ahlul Bait(A.S.), ya kuma san irin matakan gaggawa na rashin adalci da sukan dauka akan Imaman zuriyar Manzo(S.A.W.A.)…to don haka sai ya rubuta takarda zuwa halifa Mutawakkil ya bayyana masa irin kiyayya da hassada wanda wannan gomna ke yi masa, a cikin wasikar, da kuma irin mugun halin da gwamnan ke nuna masa… Sai Imam ya gaya wa Mutawakkil gaskiyar lamarin ya kuma karyata abinda magulmata suka ce… bayan wannan sai muka ga sakamako wanda…

a zahirinsa kamar mai amfani ne ga Imam(A.S.), sabili da Mutawakkil ya aika wa Imam(A.S.) da wasika, yana cewa a cikinta:

“…hakika ni na san darajarka… kuma na gane irin zaluncin da Abdullah bin Muhammad yayi maka… saboda haka na tube shi daga shugabancin sallah da yaki, wanda na dora Shi… Kuma na nada Muhammad bin Fadl a maimakonsa… na Kuma umarce shi da ya mutunta ka… ya kuma ji umarninka…”

Amma fujΰtan!! Sai ga shi an zo bincike a gidan Imam Hadi(A.S.) wani mutun wai shi Yahya bin Harsama wanda Mutawakkil ya turo shi tare da wasu `yan sanda… suka shiga gidan Imam suna bincike kan makamai… amma basu sami komai ba face Kurΰnai da littafan adduòì wanda wannan bincike na nuna cewa zargin da Abdullah bin Muhammad yayi wa Imam a wajen Mutawakkil, yayi tasiri… saboda haka Mutawakkil ya wayi gari yana fargaba kan mulkinsa… to bayan Yahya ya bincika gidan Imam Hadi(A.S.) sai muka ji Yahya ya umarci Imam da ya taho tare da shi wato ya bi shi zuwa samurra… domin ya zama kusa da Mutawakkil don halifa ya rika lura da ayyukansa da kuma mutanen da ke zuwa wurinsa… saboda hakane Madina ke cikin tsananin…

fargaba… mutane sai suka zagaye Imam(A.S.) suna kuka suna ihu, suna kuma kokarin hana Yahya bin Harsama tafiya da Imam Hadi(A.S.)… Sai Yahya yayi ta kwantar musu da hankali… yana kawar musu da fargabar da ke tare da su… ya kuma rantse musu cewa ba a umarce shi da yayi wani abinda zai cutar da Imam Hadi(A.S.) ba… daga karshe Yahya da mutanensa suka samu dai suka bar Madina alhali sun tafi da Imam Ali Al-Hadi(A.S.) tare da su… to ga yanda Madina ta zamo kamar yadda ka gani, bayan sun tafi da shi(A.S.).

Tsoho sai ya kalli idanuna bayan ya gama maganarsa… kamar zai ce yana so ya ji daga gare ni… saidai kuma na kasa yin wata magana, domin kuwa hawaye sai kwarara yake ta yi a fuskata, na ga ba abinda zan yi sai kurum na fashe da kuka…

Mutawakkil ya kebe wani karamin gida ga Imam Ali bin Muhammad Al-Hadi(A.S.) a garin samurra… Sai Imam(A.S.) ya sauka a ciki, a Kewayensa kuma ga `yan leken asirin… Mutawakkil suna lura da dukkan motsin da yayi, suna kuma kirgen numfashinsa… Imam bai ko dade ba a samurra sai ya sake fadawa cikin wani zargin daga wasu makiyan Imaman Ahlul Bait(A.S.) domin sun kai sukarsa wajen halifa Mutawakkil cewa, yana tara makamai a gidansa, makaman da suke zuwa masa daga shirās kuma wai akwai wasu rubututtuka da ke gudana tsakanin Imam da shi`arsa… to ta wadannan hanyoyi kenan Imam yake so ya kai hari ga hukuma.

Cikin dare, yayin da Imam(A.S.) yake salloli yana kuma karanta ayoyin alkur`ani a cikin gidansa yana zaune kan yashi ya kuma mayar da hankalinsa zuwa ga Allah yana ibadarsa… a cikin irin wannan halin sai kawai ga mutanen halifa Mutawakkil sun kawo hari gidan Imam Hadi(A.S.) nan take suka shiga bincika gidan… daga bisani suka ja Imam Hadi(A.S.) suka tafi da shi zuwa wajen halifa Mutawakkil…

Yayin da aka shiga da Imam Hadi(A.S.) wajen Mutawakkil… a yayin nan shi kuwa Mutawakkil yana zaune yana shan giya, sai ya kashe kunnensa yana sauraron abinda mutanensa wadanda suka shigo da Imam ke gaya masa, yana kuma lura da Imam(A.S.) yana ganin irin haibarsa da kwarjininsa…

Suka ce wa Mutawakkil… mun same shi ne ya fuskanci alkibla yana sallah yana kuma addu`a… kuma mun bincika gidansa bamu samu komai ba… bayan sun fadi haka sai suka tsaya suna jiran umarni… sai Mutawakkil ya juya wajen Imam(A.S.) ya ce masa: taho nan ka zauna a gefena…

Imam Hadi(A.S.) ya je ya zauna kusa da Mutawakkil yayin da Mutawakkil ya mika masa kofin giya… sai Imam yayi gaggawa ya ce masa: Ka dauke min shanta… domin Wallahi tun da Allah ya yi ni giya bata taba shiga jini na da tsokar jiki na ba…!!

Sai Mutawakkil ya mayar da kofin giyar ya ajiye, Sannan ya ce wa Imam: to ka karanta mana kasida…

Sai Imam(A.S.) ya ce masa: ni ba mai yawan kasidu bane…

Sai Mutawakkil ya ce masa: wannan kam ba makawa sai ka yi…

Sai Imam ya fara kasida kamar haka, yana mai cewa:

«Sun kwana cikin benaye ana gadinsu,

Amma benaye basu yi musu amfani ba.

Sai aka sauke su bayan daukaka na benaye, Aka shigar da su ramuka, kaico masaukinsu yayi muni.

Mai shela ya kira su bayan an binne su, Ina kyambi da dinari da kayan kawa.

Ina fuskokin da da suke cikin ni`ima, Wanda dominsu da ake kirari da fadanci?

Sai kabari ya bude su bayan anyi tambaya, Ga fuskokin nan tsutsotsi na fadi-tashi akai.

Sun ci sun sha na tsawon zamani, sai suka wayi gari bayan sun ci, yau suma an cinye su.

Kuma sun dade suna gina gidaje domin su zauna, Amma ga su sun rabu da gidajen da iyalai, sun tafi.

Kuma sun dade suna tara dukiya suna boye ta, sai suka rarraba ta ga makiya, suka tafi. Gidajensu sun zama tamkar wanda akai musu hijira, Masu gidan kuma sun sauka cikin kaburbura».

Halifa Mutawakkil yayin da yake tuna ma`anar wadannan baitocin na kasida, sai hawaye suka rika zubo masa… to Imam yana kare wannan kasidar kenan sai Mutawakkil ya bada umarni a maida shi gidansa…

To saidai akwai wani lamari wanda ba dama ya buya ga wani mutum… lamarin kuma shine cewa Banu Abbas a duk lokacin da suka ji cewa zukatan mutane na tare da Ahlu Baitin Annabi(S.A.W.A.) sai fushinsu da kiyayyarsu ta dada tsananta a zukatansu… domin suna tsoron cewa asirinsu zai tonu, daga bisani kuma jama`a ta yi musu bore… sabili da haka halifan Banu Abbas ya sa guba wa Imam Hadi(A.S.), suka kashe shi a wani irin hali da suka boye hakikaninsa… wannan kuwa ya faru ne a ranar(3) ga watan Rajab a shekara ta 254 yayin nan yana da shekara 40 (arba`in) da haihuwa.

عنوان الکتاب