|
GAME DA RAYUWAR IMAM JAWAD (A.S.) |
||
|
ANNURI DAGA HASKEN ANNABCI
δζΡ γδ ήγΡ ΗαδΘζε
Tarihi ya kira ni zuwa ga kallon ababen da ya kunsa, sai na amsa kiransa na bi shi na shiga wani babban zauren kallo na zauna a bayan labule, wanda ba da dadewa ba aka yaye shi, me zan gani, sai ga ni ina ganin Imam Muhammad bin Ali Al-Jawad(A.S.), yayin nan yana yaro, a shekararsa ta takwas, sai na gan shi yana tafiya a gefen hanya kwarjininsa da daukakar sa sun sa na tsaya ina kallonsa, har na gaza sifanta shi kuma na kasa sifanta irin hasken da ke haskakowa daga fuskarsa to bayan dan lokaci sai ga yara da matasa suna gaggawar zuwa gareshi ta ko ina, ba komai ke tunkudo su zuwa gare shi ba, face tsanannin soyayyar da suke yi masa a birnin zuciyarsu Sai suka zagaye shi suna sauraran maganarsa kuma ga su sun nutse cikin lura da tunani yaya kuwa baza su zama haka ba, alhali suna gaban wanda yayi galaba a kan mutan zamanin sa a fagen ilimi da falala kuma babu kamili kamarsa a cikin mutanensa, ba kuma wanda darajarsa ta kai tasa faju`atan!! Sai ga wadannan yara da matasa sun fara gudu suna watsewa alhali sun razana wannan kuwa ya faru ne saboda Maamun. Wani masaraucin Banu Abbas ya fito cikin wata jamaΰ daga masu tsaronsa yana haye bisa dokinsa, yana kuma rike da tsuntsu a hanunsa wanda ake kira shaho sai ya ci gaba da tafiya har ya nufo inda Imam Muhammad bin Ali Al-Jawad(A.S.) yake, domin ba wanda ya saura a gurin sai shi kadai sai Mamun ya ce wa Imam Jawad:- Me ya sa baka gudu ba kamar yadda sauran yara suka aikata? Sai Imam Jawad(A.S.) ya ba shi amsa ya ce masa: Ni ba ni da zunubi ballantana in guje masa ba kuma hanya bace ta yi kunci ballantana in yalwata maka kai dai bi inda ka so Sai Maamun ya ce: kai wanene Sai Imam Jawad(A.S.) ya mayar masa ya ce:- Ni ne Muhammad bin Ali bin Musa bin Ja`far bin Muhammad bin Ali bin Husain bin Ali bin Abi Talib(A.S.) Sai Maamun ya ce masa:- Me ka sani na daga barin ilimi ? Sai Imam Jawad(A.S.) ya ce masa: Ka tambaye ni labarin Sammai Sai Maamun ya saki tsuntsu daga hannunsa tsuntsu ya tafi` can Sama yana shawagi a sararin samaniya yayin da tsuntsu ya dawo wajen Maamun. Yane rike da wani abu a bakinsa Sai Maamun ya boye abin, sannan sai ya komo wajen Imam ya ce masa:- Me kake da shi na labarin sama ? Sai Imam(A.S.) ya ba shi amsa, ya ce: Mahaifina ya ruwaito ruwaya daga iyayensa daga Annabi(S.A.W.A.) daga Jibrilu daga Ubangijin Talikai cewa: Tsakanin Sammai da iska akwai kogin gishiri wanda ruwa ke tasowa a ciki, a cikin wannan kogin akwai macizai masu koren ciki da rodi-rodin baya, tsuntsayen sarakuna da halifofi zasu farautansu za kuma a gwada zuryar Ahlu Baitin Annabi da su Maamun sai yayi mamakin amsar Imam Jawad(A.S.) sai ya ce masa: Hakika kai dan Imam Rida ne, kuma lallai kai daga Annabi kake Sai ya hawar da Imam kan doki Sannan ya tafi da shi fadarsa a wannan lokaci sai na ji wani hannu na taba ni a hankali, koda na juya sai naga da na Hamidu yana ce mani: Baba hakika Ka dade a cikin wannan hali na tunanin da kake, kuma tun dazu ka yi shiru bakai magana ba shin akwai wata matsala ce ? Sai na yi wa Hamidu mirmishi na ce masa: Ina yin tunani ne kan wasu abubuwa da suka faru tun da ga ni kamar ina ganinsu a gaba gareni yanzu haka ya mamakin irin wannan abu, ya kai da na, yayin da Maamun ya sadu da Imam Muhammad bin Ali Al-Jawad(A.S.) wanda a lokacin Imam Jawad yana da shekara takwas da haihuwa Baba, a ina ne Maamun ya sadu da Imam Jawad(A.S.)? A Bagdad A Bagdad dai ?! Da na Hamidu ya fadi wannan magana yana mamaki, sannan ya kara da cewai: Ni dai abinda na sani baba shine cewa Imam Jawad(A.S.) da yayi rayuwarsa ne a garin Madinatul Munauwara domin ita ce garin kakansa Manzon Allah(S.A.W.A.) Wannan haka yake da na saidai kaima ka san matsa yin Banu Umayya da Banu Abbas dangane da Ahlu Baitin Manzon Allah(S.A.W.A.), don haka ne Maamun ya aika a zo masa da Imam Jawad(A.S.) daga Madina zuwa Bagdad domin ya rika sa masa ido nan kusa da shi kuma saboda `yan leken asirin Maamun su rika ganin dukkan ayyukan Imam Jawad da kuma wadanda ke zuwa wurinsa yayin da Imam Jawad ya isa Bagdad (Bagdaza) Maamun bai nemi saduwa da shi tun farkon zuwansa ba a ΰ barinsa yayi har sai da rannan ya gamu da shi To mecece manufar Maamun da ya jinkirta saduwarsa da Imam Jawad(A.S.)? Akwai dalilai da dama ya da na, daga ciki akwai cewa Maamun yayi haka ne domin farko ya jira ya ga irin ayyukan da Imam zai yi da kuma irin mutanen da zai rika saduwa da su wani dalilin kuma shine cewa shi Maamun yayi nufin ya wulakanta Imam Jawad(A.S.) ne domin haka shugabannin nan sukai tai wa Imaman Ahlul Bait(A.S.) Maΰnar wannan ya mahaifina ita ce kenan Maamun ya kasance yana neman hanyar kashe Imam Jawad(A.S.) ne kamar yadda yayi wa mahaifinsa Imam Rida(A.S.) Haka yake da na to saidai akwai dalilai da dama da suka hana Maamun yayi saurin aiwatar da wannan manufa tasa sababi na farko shine cewa Maamun ya sami kansa cikin mawuyacin hali bayan kashe Imam Ali bin Musa Ar-Rida(A.S.) domin kuwa dukkan mutane sun tuhumce shi da haka kuma lamarinsa ya fito fili to don haka ya so ya nuna girmamawarsa da soyayyansa ga Imam Muhammad Al-Jawad(A.S.) to ta haka yake son ya sami dalilin da zai kaddamar ko ya lullube abinda ya aikata kuma ya nuna wa mutane kyakyawar niyyarsa dangane da Imaman Ahlul Bait(A.S.) gwargwadon iyawarsa sababi na biyu kuwa shine cewa Maamun ya so ya ga ko zai samu ya yaudari Imam Jawad(A.S.) sabili da ganin karancin shekarunsa, domin ko can dama Maamun yana da raΰyin cewa Imam Jawad(A.S.) baya da ilimin da ya cancanci ya zama Imam, Saboda haka yayi nufin ya sa Imam Jawad(A.S.) yayi mukabala da malamai wanda sakamakon mukabalar zai jawo zubar da mutuncin Imam Jawad(A.S.) a wajen mutane To abinda shi Maamun ya zata kenan Sai da na Hamidu, a halin yana mamaki sosai, ya ce: Baba wannan shugaban tunaninsa ya sha bamban da tunanin shugabannin Banu Umayya da Banu Abbas domin shi ya bayyana soyayya ga Imaman Ahlul Bait(A.S.). Ya kuma nuna musu girmamawa, saidai kuma a wani barin ya boye musu makirci da mugunta mai girma wato yana nufin ya karya mazhabar shiΰ ta hanyar rusa akidar Imamanci a cikinta daga bisani ya samu ya sa tauraronta mai haske ya dushe wannan shine abinda Maamun ke neman aikata wa Imam Jawad(A.S.). Haka ne da na sabili da haka abu na farko da Maamun ya fara yi domin gusar da mummunan zato a kansa, shine ya aurar da `yarsa Ummul Fadl ga Imam Muhammad Al-Jawad(A.S.) har na kusa da Maamun (wato makarrabansa) suka soki wannan raΰyi nasa, suka taru a fadarsa suna zarginsa, suka ce: Yanzu ka aurar da `yarka abar kaunarka ga dan yaro wanda bai yi ilimi ba tukunna a addinin Allah kuma bai san halalinsa daga haram dinsa ba ? Ka yi hakuri tukunna har sai ya karanta Al-Kurΰni Ya kuma san halal daga haram tukunna Sai Maamun ya ce musa: Hakika ya fi ku ilimi ya kuma fi ku sanin hukunce-hukuncen Allah taΰla da sunnar manzonsa(S.A.W.A.) kuma ya fi ku karanta littafin Allah, ya kuma fi ku sanin bayyanannun ayoyin al-kurΰni da masu kama da juna, hakakuma ya fi ku sanin ayoyin da suka shafe hukuncin wasu da wadanda aka shafe hukuncinsu, haka kuma ya fi ku sanin zahirin Al-Kurΰni da kuma badininsa (wato waje da cikinsa), har wa yau ya fi ku sanin ayoyi masu hukunci gamammu da kuma masu kebabbun hukunci, daga karshe ya fi ku sanin abinda ayoyin al-kurΰni suka sauka akansa ya kuma fi ku sanin tawilinsu Ku tambaye shi, idan lamarin ya zama kamar Yadda kuka sifanta to na yarda da maganarku Sai suka fita daga fadarsa Sannan suka aika wa alkalin-alkalai Yahya bin Aksam suka nemi ya biya musu bukatarsu, sai suka kwadaitar da shi da kyaututtuka, sannan suka nemi yayi hila wa Imam Jawad(A.S.) yayi masa tambayoyi wanda bai san amsar su ba Anan ne sai dana Hamidu ya tambaye ni, dama can yana jiran ya ji sakamakon lamarin, kai ka ce yana zaune ne kan garwashin wuta saboda tsananin jira, sai ya ce mini: To menene Imam Jawad(A.S.) yayi dangane da dukkan wadannan abubuwa Baba ? Maamun da shi da Yahya bin Aksam suka kira Imam Jawad(A.S.) a gaban tarin jamaΰr mutane daga. Banu Abbas da wasunsu Sai Maamun ya kalli Yahya bin Aksam ya ce: ka tambaye shi ya kai Yahya, farko kan lamurran fikihu Sai Yahya ya juya zuwa wajen Imam Jawad(A.S.) yana tambayarsa, yace, Allah ya kiyaye ka, me zaka ce dangane da mai ihrami, wanda ya kashe abin farauta ? Sai Imam Jawad(A.S.) ya ce masa: Shin ya kashe shi a cikin haram ne ko kuwa a wajen haram? Shin yana sane ko kuwa bisa jahilci ne? Shin da gangan yayi, ko kuma kuskure ne? Shin shi wanda ke cikin ihramin bawa ne ko kuma da ne ? Yaro ne ko babba ? Karon farko ke nan ko ko aΰ shin abin farautar daga layin tsuntsaye ne ko kuwa wasunsu shin daga kananan tsuntsaye ne ko kuma daga manya? Yayi nadama ko kuma yana shirin sake aikawata ? Da dare ne a yayin nan tsuntsun na shekarsa (makwancinsa) ko kuma da rana ne a idon jamaΰ? Shi wannan wanda ke sanye da ihrami, shin ihramin haji ne ya daura ko kuma na Umara ? Sai aka ji Yahya yayi shiru, shirun da ya bayyana ga dukkan wadanda ke zaune a wurin, mutane kuma suka dimauce saboda mamakin maganar Imam Muhammad Al-Jawad(A.S.), to sai Maamun yayi ishara ga Imam Jawad(A.S.) da cewa ya bayyana musu ko wanne daya daga wadannan nauòì na abin farauta, sai Imam ya bayyana musu hukuncin kowanne daya daga cikin wadannan halaye wanda hakan sai ya kara bada mamaki da tau ujjubi ga mutanen dake wurin Sai Maamun ya juya ga mutanensa na kusa da shi ya ce: Shin a cikin ku akwai wanda zai iya bada irin wannan amsa ? Sai suka ce masa: Wallahi babu babu koda kuwa alkalin alkalai Sai Maamun ya ce musu, yayin nan kwalliya bata biya kudin sabulu ba, domin kuwa ya gaza zubar da mutuncin Imam Jawad(A.S.) kamar yadda yayi nufi, ya ce musu: Kaicon ku, shin baku san cewa Ahlu Baitin Annabi ba halitta ba ne irin kuba ?! Anan ne sai fuskar da na Hamidu ta cika da farin ciki mai tsanani sai yayi murmushi gwanin kyau da gani ya ce: Ai gaban irin wannan ilimi da haske na zuriyar Manzon Allah(S.A.W.A.) ba abinda wani mahaluki zai musu iya yi face kawai yaa sallama musu tilas, komai kin sa E haka ne da na, hakika Maamun ya rasa abinda zai ce wa Imam Jawad(A.S.), haka suma sauran mutanen dake wurin musammam ma Yahya bin Aksam domin kuwa ya sami kansa a cikin mawuyacin hali na fargaba da rikicewa da kuma rudewa, bai san abinda zai aikata ba to sai ya ci gaba da tambayar Imam Jawad(A.S.) wasu tambayoyi, ko ya samu yayi nasara cikin wata: ya ce: me zaka ce ya dan Maΰikin Allah dangane da wannan ruwaya:, an ruwaito cewa Jibrilu(A.S.) ya sakko wajen Manzon Allah(S.A.W.A.) sai ya ce masa: Ya Muhammadu Allah madaukakin sarki yana karanta maka sallama yana kuma ce maka: ka tambayi Abu Bakr shin ya yarda da ni, domin ni na yarda da shi Sai Imam Jawad(A.S.) ya ba shi amsa ya ce: ya wajaba ga wanda ya ruwaito wannan ruwaya ya dauki misalin irin ruwayar da Manzon Allah(S.A.W.A.) ya fada a hajjin bankwanar sa, ya ce:Hakika masu yi mini karya sun yi yawa, kuma zasu yi yawa a bayana to wanda yayi mini karya da gangan ya tanadi makomarsa a wuta idan hadisi ya zo muku daga gare ni to ku gwada shi da littafin Allah abinda yayi daiddai da littafin Allah ku yi aiki da shi, abinda kuma ya sabawa littafin Allah kada ku yi aiki da shi kuma wannan ruwayar da ka tambaya bata yi daidai da lattafin Allah ba domin kuwa Allah Taΰla ya ce: hakika mun halicci mutum, kuma Mun san abinda ransa ke yin waswasi da shi, kuma Mu ne muka fi kusanta zuwa gare shi daga jijiyar wuyansa[1]. Shin kana ganin yaddar Abu Bakr ko kuma fushinsa zai buya wa Allah har Allah Yayi tambaya akan wannan asirin?! Lallai wannan abu baya taba yiwuwa a hankalce Sai Yahya ya sake yi wa Imam(A.S.) wata tambayar ya ce: An kuma ruwaito cewa misalin Abu Bakr da Umar a kassai tamkar misalin Jibrilu da Mikaìlu ne a Sammai ? Sai Imam Jawad(A.S.) ya amsa masa ya ce: wannan ma wajibi ne a duba shi, domin kuwa Jibrilu da Mikaìlu malaìku guda biyu na Allah wanda Allah ya kusantar da su, basu taba sabawa Allah ba koda sau daya kuma basu taba barin biyayya ga Allah ba, koda na dan lokaci Umar da Abu Bakar kuwa sun taba yin shirka da Allah madaukaki, koda yake sun musulunta bayan shirkarsu, saidai kuma kwanakin su sun fi yawa a shirka Saboda haka abu ne da baya yiwuwa a ce sun yi kama da Jibrilu da Mika`lu wannan bai ishi Yahya bin Aksam ba, sai ya sake yin wata tambayar, ya ce wa Imam Jawad(A.S.): An ruwaito cewa Umar bin Khattab shine fitilar `yan aljanna ? Sai Imam Jawad(A.S.) ya ba shi amsa ya ce: Wannan shi ma ba mai yiwuwa bane, domin kuwa a cikin aljanna akwai malaìkun Allah makusanta, kuma ga su Annabi Adam(A.S.) da Annabi Muhammadu(S.A.W.A.) da dukkan sauran Annabawa da Manzanni, shin aljanna ba zata haskaka da haskensu ba ? Sai da hasken Umar ne zata haskaka? Sai Yahya ya komo da wato tambayar kuma, ya ce hakika an kuma ruwaito cewa Annabi(S.A.W.A.) ya ce: Da ba a aiko ni ba, to da an aiko Umar Sai Imam Jawad(A.S.) ya amsa da cewa: Littafin Allah Shi ya fi gaskiya akan wannan hadisin domin Allah Taΰla Yana cewa cikin littafinsa:Kuma a lokacin da Muka riki alkawari daga Annabawa, kuma daga gareka, kuma daga Nuhu [2] Hakika Allah ya riki alkawari daga Annabawa to ta yaya zai canja alkawarinsa? Kuma dukkan Annabawan Allah basu yi shirka ba koda kwatankwacin kiftawar ido, to ta yaya Allah zai aiko wanda yayi shirka ya zama annabi? Kuma mafi yawancin ranekunsa a shirka ya yi su Kuma hadisin Manzo(S.A.W.A.) ya wadace mu inda yake cewa: An ba ni annabci a yayin nan Adam yana tsakanin ruhi da jiki. Yahya ya ci gaba dai da tambayar Imam Jawad(A.S.) Sai da na Hamidu yayi dariya har sai da idanunsa suka yi kwalla don tsananin dariya sannan ya ce Baba ai a banza ne Yahya yake ta faman yin tambayoyi ga Imam Jawad(A.S.) Koda kuwa ya saura a bisa wannan hali duk tsawon rayuwarsa to amma wace tambaya ce kuma yayi bayan haka ? Ya ce: An ruwaito daga Annabi(S.A.W.A.) cewa ya ce: Wahayi bai taba jinkiri ba a gare ni face na yi zaton cewa ya sauka wa zuriyar Khattabi ? Imam Jawad(A.S.) ya ba shi amsa: Da cewa wannan ma ba zai yiwu ba domin kuwa bai halatta ba Annabi(S.A.W.A.) yayi kokwanto akan annabcinsa Allah Taΰla yana cewa:Allah yana zaben manzanni daga malaìku, kuma daga mutane[3]. To ta yaya zai yiwu a ce annabci ya tashi daga wurin wanda Allah ya zabe shi, ya koma wajen wanda ya yi shirka? Yahya ya sake komowa da wata tambayar har yanzu, ya ce: An ruwaito cewa Annabi ya ce: Da azaba zata sauka, to da babu mai tsira daga gare ta face Umar ? Imam Jawad(A.S.) sai ya amsa masa da cewa, wannan baya yiyuwa domin Allah madaukaki yana cewa:Kuma Allah Bai zama mai yi musu azaba ba alhali kai Kana cikinsu, Kuma Allah bai zama mai yi musu azaba ba alhali suna yin istigifari[4] Hakika Allah ya fada cewa ba zai azabtarda wani mutum ba matsawar Manzon Allah(S.A.W.A.) yana cikin mutanen, kuma matsawar suna yin istigifari To da haka ne dukkan kokarin Yahya bin Aksam ya za ma ya ci tura, bai tsinana komai ba, sai ya daina magana. Alhali faduwarSa da rashin nasarasa ta na cin zuciyarsa Shi kuma Maamun wannan abin ya dada bayyana masa hadarin lamarin, sai ya bata shiru, saboda girman fargabansa ya kuma gane cewa dole ne ya fuskanci wannan lamari da gaske, tare kuma da makirci mai tsanani, matsawar yana so ya sami nitsuwa kan makomarsa da ci gaban mulkinsa ga Banu Abbas suma suna tare da shi to wannan abin ne ya kai shi ga ya bayyana darajar Imam(A.S.) da ganin kuma irin yawan iliminsa a wannan taron ne kuma Maamun ya sanar da cewa ya aurar da `yarsa Ummul Fadl Saidai Maamun ya saura yana ta jiran wata dama da zai dau fansa akan Imam Jawad(A.S.), ya kuma samu wannan damar ta hanyar `yarsa Ummul Fadl, matar Imam Jawad(A.S.), yayin da ta sa masa guba. |
||