|
Gabatarwa |
||
|
بسم الله الرحمن الرحيم DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI“MU MUNA BAYAR DA MAFI KYAWUN LABARAI A GARE KA” SURATU YUSUF AYA TA 3
Godiya ta tabbata ga Allah amincinsa ya tabbata ga bayinsa zababbu Annabi Muhammadu da ‘ya‘yan gidansa, Imamai ma asumai masu albarka. Rayuwar Imamai ma’asumai (A.s.) ta taro falala da Kuma dabi’u na kwarai don kuwa sune masu shir ya swa ga bil Adama kuma sune masu kira zuwa ga alheri sabili da haka Allah Madaukaki ya zabe su domin su zama shugabanni kuma ababen koyi ga mutane. Hakika tarihinsu ya kunshi labarai na koli wanda ke nuna muhimmancin halaye da kuma dabi’u na gari a rayuwar al ‘ummu. To don ganin cewa tarihin rayuwarsu mai albarka yana da yawa so sai sai Muassasar Imam Ali (A.s.) ta fara buga tarihinsu a jere ta hanyar da ta dace da matasa. Sai ta zabo wani lamari daga rayuwar su ta buga shi wani lamari daga rayuwar su ta buga shi a salon labari, an kuwa zabi wannan hanyar ce domin a ga amfanin dake cikin rayuwarsu ya game kowa, kuma daga bisani a kwadaitar da ‘ya ‘yanmu domin su kara Samun ilimi da kuma ci gaba na ruhi wanda tarihin musulana madauwami ya kunsa. Muna rakon Allah madaukaki mai iko yayi mana katari ga abinda zai zama hidima ga tarihin Ahlul Bait tsarkakku. DUKKAN HAKKW MALLAKA YA RATAYA GA: MUASSASAR IMAM ALI (A.S.)
Allah shi ne mai yin katari. Muassasar Imam Ali (A.s.) Watan shauwal 1418 Hijiriyya. |
||