FASALI NA BIYU ANNABCI

 

  1. Annabci

  2. Annabci Tausasawa Ne.

  3. Mu’ujizar Annabawa.

  4. Ismar Annabawa.

  5. Siffofin Annabawa

  6. Annabawa da Littafansu.

  7. Mai Shar’anta Musulunci

  8. Alkur’ani Mai Girma

  9. Tafarkin Tabbatar da Alkur’ani da shari’u Magabata.

  10. Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin Musulunci Da Sauran Shari’u Magabata.

 


 

13- Imaninmu Game da Annabci

Mun yi imani cewa Annabci aiki ne na Allah Ta’ala, wakilci ne na Ubangiji, wanda shi Allah Ta’ala Yake daukar wadanda Ya zaba daga cikin bayinSa salihai da waliyanSa kamilai a ‘yan Adamtakarsu, Ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da maslaha gare su a duniya da kuma Lahira. Tare kuma da nufin tsabtace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u da munanan al’adu kuma da koya musu hikima da ilimi da bayyana musu hanyoyin Sa’ada da alheri domin ‘yan Adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da na Lahira

Kuma mun yi Imani cewai Lalle ka’idar tausasawa -wanda da sannu za mu yi bayanin ma’anarta nan gaba- ta sanya ya zamababu makawa Allah Ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sokan gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa.

Kamar kuma yadda muka yi imani da cewa Allah Ta’ala bai dora wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zaben sa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al’amarin haka ga Allah yake domin “shi ne Ya fi sanin inda zai sa sakonSa.” Surar An’am ayata 124.

Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, kamar kuma yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hakunce-hukunce da sunnoni da shari’a.[1]

 

14- Annabci Tausasawa

Lalle shi mutum halittane mai haddodi masu ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi’arsa da rahinsa da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin jama’arsa/ Nauo’in zaburar fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda masu zaburarwa zuwa ga alheri da gyara suka tattara a cikinsa ta bangare gudan.

Allah Ta’ala yana cewa: “Da rayi da abinda Ya daidaita takuma Ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta.” (Surar Shamsi: 7-8) “Lalle shi mutum tabbatacce yana cikin hasara.” Surar Asri: 2. da kuma “Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata” Surar Aiak: 6-7 “Lalle zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma sha’awa.

A bangare na biyu kuma, Allah Ta’ala Ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya mai gargadi da ke masa fada kada Ya aikata mummuna da zalunci tare da aibata shi a kan aikata abinda yake mummuna abin zargi.

Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da’iman yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali. Duk wanda hankalinsa Ya yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan adam takarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa Ya rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi, masu taraddudi a yan Adamtaka, masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.

Mafi tsanani daga cikin wadannan masu husuma biyu itace tausasawar zuciya da rundunarta. Don haka ne kake ganin yawancin mutane sun dulmuye a cikin  bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran raunin zuciya, “kuma mafi yawan mutane ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka.” Surar Yusuf: 103.

Shi mutum saboda gazawarsa da rashin saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda ke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa’ada ko ya ka’ shi ga tsiyacewa ba, sawa’un a kan abinda ya kebatu da shi ne shi kadai ko kuwa wanda Ya shafi dan Adam baki daya da kuma al’ummar da ke kewaye da shi. shi bai gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahintar jahilcinsa ne duk yayin da iliminsa game da dabi’a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.

Yawanci bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara na  kara tsananta ne yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake mummuna cewa mai kyau ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun fandarewarsa, ta rikitar masa hanyar gyara da sa’ada da ni’inma a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna marar amfani ga mai gaggawar kutsawa cikin wannan arangamar ne ta yadda ya sani ko kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah Ya kubutar.

Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani Ya kai kansa ga dukan tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko Ya cutar da shi a duniya da Lahira ballantana kuma jahili; sawa’un al’amari ne da ya kebe shi shi kansa ko kuma Ya hada da al’umma da yake zaune a cikinta ne. Ba Ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa sunyi tarurruka da zama dabam-dabam da kuma shawarwari.

Don haka ne ya zama wajibi Allah Ta’ala Ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su.

“Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima” (Surar Juma’a: 2) Yana musu gargadi game da abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da alheri da gyaruwa da sa’ada a gare su. Tausasawar daga Allah wajibi ne domin tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar Ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa Ya zuba tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a kyautarSa da karimcinSa.

Ma’anar wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba ne har Ya zama tilas a kansa Ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah Ya daukaka ga haka ma’anar wajibi a nan tamkar ma’anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah wajibin samamme ne wato ba zai taba koruwa ba ba zai taba yiwuwa a raba shi da samuwa ba.

 

15- Imaninmu Game da Mu’ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa lalle Allah Ta’ala tunda Yake sanya wa bayinsa mai shirya da kuma Manzo to babu makawa Ya sanar da shi gare su, Ya kuma nuna musu ko wane ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasasarSa da kumaa kammala rahamarSa.

Allah Ta’ala Yana cewa: “Manzanni masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a gurin Allah bayan Manzanni kuma Allah Mabuwayi ne Mai hikima.” Surar Nisa’i: 165.

Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya zamanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu, mai sarrafa samammu- wato ya zamanto abin a dara kudurar dan Adam. Ya sanya shi a hannun shi manson mai shiryarwa, domin Ya zamanto an san shi da shi kuma Ya zamanto mai shiryanwa zuwa gare shi wannan dalili da hujja shi ake kira mu’ujiza; wato gagara badau saboda kasncewarsa ya gagari dan Adam, ya yi gasa da shi ko kuma ya kawa makamancinsa.

Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza yha bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya nuna ta kuma yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa; ballantana kuma sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu’ujizar, saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.

Idan wannan Ya tabbata ga mutum, bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada, ya kuma yi da’awar Annabci   da sako, to a lokacin sai ya zamanto abin gaskatawar mutane a kiran da yake yi, tare da yin imani da sakon nasan, da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi Ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya kafirce masa.

Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa. Mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin ba duhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu, lalle wannan yana daga cikin abubuwan da, dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa da ilimi sun dushe a gabansa. Allah Ta’ala yana cewa:

“Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandanka sai ga shi yana hadiddiye abubuwan da suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci. Sai aka rinjaye a nan ,sa’annan suka koma suna kaskantattu. Kuma aka kifarda masu sihirin suna sujada.” Surar A’araf: 117-120.

Hakanan mu’ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci shi ne fannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma akwai malamai akwai likitoci da suke su ne manyan bokaye gare su sai iliminsu ya gaza jeruwa da abinda Annabi Isa (A.S.) Ya zo da shi. Allah Ta’ala Yana cewa? “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai.” Surar Al- Imran: 49.

Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Alkur’ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma’abuta  ilimin balaga su ne kan gaba a tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da balagarsu sai da Alkur’ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya fahintar da su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu.

Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma idan damutane da Aljannu za su taru a kan su zoda kwatankwacin wannan Alkur’anin to da ba za su zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe.” Surar Isra’i: 88.

Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta’ala Yana cewa: “Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah in kun kasance masu gaskiya” Surar Hud: 13

Sa’an nan kuma ya sake kalubalantar su kan su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23

Allah Ta’ala Yana cewa: “Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya ba Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.

Ya sanar da mu yadda suka koma fito na fito da hakora ba da harshe ba Ya sanar da mu cewa shi Alkur’ani wani nau’i ne na mu’ujiza kuma Annabi Muhammad bin Abdullah ya zo da shi ne da kira da kuma da’awar sako.Don haka muku san cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo da gaskiya da hakika kuma shi ma ya gaskata da shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

 

16- Imaninmu Game da Ismar Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma’asumai ne, ba sa, aikata sabo dukkaninsu kazalika Imamai kyakkyawar gaisuwa ta tabbata a gare su. Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma rashin aikata sabo ga.

Annabawa[2]ballantana ma Imamai Isma: Ita ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu; da kuma tsarkaka daga mantu wa[3] , koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba. Sai dai kawai wajibi ne Ya zamnato Ya tsarkaka hatta daga dukan abinda ke zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala dariya da dai dukan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane.

Dalilin da ya Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaroda rangwame daga Ailah, bilhasali ma dai mun wajabta haka[4] ne wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban addini da kuma a gurin hankali.

Idan kuwa biyayya gare shi bata wajaba ba a kan haka to kuwa wannan ya saba wa Annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin da’a dimin da’iman.

Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da’a a kan kome ba, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai, Annabin kuma sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wato kimar da za a dogara a kanta da’iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki daya game da maganganunsa da ayyukansa.[5]

Wannan kuma daliline da ke tabbatar da cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbene daga Allah Ta’ala don shiryar da mutane amatsayin halifan Annabi, za mu yi karin bayani a fasali game da Imama.

 

17- Imaninmu Game da Siffofin Annabi

Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda ya wajaba ya zamanto ma’asumi haka na ya wajaba ya zamanto yana da mafi kamalar siffofin dabi’u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya tafida jama’a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto shugabaci a kan dukan halittu kamar kuma yadda ba zai yiwu ya zamantoya tafi da al’amuran duniya baki daya ba.

Kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haikuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukan miyagun dabi’u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.

 

18- Imaninmu Game da Annabawa da Littafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da kasancewarsu ma’asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin izgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda Ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.[6]

Wadanda aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S.) da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan da Alkur’ani ya ambace sua sarari Ya wajaba a yi imani da su a ayyane[7] duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to Ya karyata su baki daya kuma Ya karyata Annabinmu a kebance.

Kazalika Ya wajaba a yi Imani da littafansu da abinda aka saukar Musa.

Attaura da Linjila ko kuma Bebul Tsoho da sabon Alkawarin da ke hannun mutane a wannan zamanin ya tabbata cewa gurbatattu ne daga ainihin wadanda aka saukar saboda abinda ya auku gare su na daga canje-canje da musanyawa, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S.) saboda wasan da ma’abuta son rai da kwadayi suka yi da su. Bilhasali ma dai yawanci ko kuma ma dukkaninsu mabiya ne suka kaga su; bayan su Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) ba sa nan.

 

19- Imaninmu Game da Musulunci.

Mun yi imani cewa lalle addini a gurin Allah kawai shi ne Musulunci[8], kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wadda ita ce Shari’ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga alherin Bil Adama, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da Lahira, ita ce mafi dacewa duk tsawon zamani, ba ta canjawa ba ta sakewa, kuma matattara ce ga dukan abinda Dan Adam ke bukata na daga tsarin rayuwar daidaiku da halin zaman jama’a da na siyasa.

Da yake Shari’ar Musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za ta zo ta yi gyara ga Dan Adam da ya rigaya ya dulmuye a cikin zalunci da fasadi, don haka babu makawa wato rana ta zo addinin Musulunci ya yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.[9]

Idan da an gudanar da Shari’ar Musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da addinin Musulunci ya game tsakanin Bil Adam kuma da alheri ya game su, kuma da sun kai kololuwar abinda Dan Adam ke mafarkinsa na daga jin dadi da daukaka da sa’ada da ginuwa da halin kwarai, kuma da zalunci ya kare a duniya, soyayya da ’yan’uwantaka, kuma da talauci da fatara da miyata sun kare baki daya.

Koda a yau muna ganin halin ban kunya da ketare hakki daga gurin wadanda ke kiran kansu musulmi dalili shi ne kawai cewa ba a aiwatar da musulunci a aikace ba a hakikaninsa tun daga karni na farko - kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummuna hali zuwa wanda ya fi shi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Sai dai kuma ba wai riko da Musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa Musulmi wannan jinkiri ba sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar Musulunci da tozarta dokokinsa da yaduwar zalunci da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu, Shi’ansu da Ahlussunnansu. Wannan shi ne abinda ya lagarta yunkurin ci gaba, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah Ta’ala Ya halaka su saboda zunubinsu. Allah Ta’ala Yana cewa:

“Wannan kuwa domin lalle Allah bai kasance Yana canja wata ni’ima da Ya ni’imtar da ita a kan wasu face sun sauya abinda ke zukatansu ne kuma lalle Allah mai Ji ne masani.” Surar Anfal: 53.

Wannan ita ce sunnar Allah a halittunSa “Cewa lalle tabbas masu laifi ba sa cin nasara.” Surar Yunus: 17.

“Kuma Ubangijinka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara.” Surar Hudu: 117.

“Kuma haka nan kamun Ubangijin ka yake idan Ya kama Alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai zafi ne mai tsanani.” Surar Hudu: 102.

Ta yaya za a tsammaci addinin musulunci ya daga al’umma daga gadon barcinta alhali kuwa tana da Alkalami da tawada ba ta amfani da mafi karanci daga koyarwarsa. Lalle imani da amana, da gaskiya da ikhlasi, tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abinda yake sowa kansa da makamantansa duk suna daga asasan addinin Musulunci na sahun farko farko kuma musulmi sun yi ban kwana da su har muka kare ga halin da muke ciki a yau. Duk lokacin da zamani ya kara nisa sai mu kara jama’a-jama’a dabam-daban da kungiyoyi suna kifuwa a kan duniya suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta ko kuma a kan wasu al’amura da ba su dame su ba, suka mance da ainihin addini, suka bar maslaharsu da maslahar jama’a suka shagala da jayayya a kan al’amura kamar su halitta Alkur’ani ko rashin kasancewarsa halittacce, da batun alkawari game da azaba da raja’a, da kuma cewa Aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halitta su ne nan gaba. Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasunsu da ita babu abinda suke tabbatarwa illa kawai kaucewar musulmi da madaidaicin tafarkin da aka riga aka gyara zuwa ga halaka da karewa.

Fandarewar ta karu kuma tare da shudewar zamani har ta hada da Jahilci da bata suka dukufa a kan aibobi da bawawwaki a kan al’amura da surkulle da wahamce-wahamce tare kuma da yake - yake, da jayayyar rikitarwa. Wannnan shi ne abinda ya sa suka auka a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau Yammacin Turai babban sanannen makiyin Musulunci har sun iya sun yi mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanuwa yadda har Yammacin Turai din na iya jefa mummunna halin da Allah ne kadai Ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah Ta’ala  Yana cewa: “Kuma ubangijin ka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara.” Surar Hudu: 117.

A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita illa su koma ga kawukansu su yi wa kansu hukunci a kan sakacin da suka yi. Su yi yunkurin gyara kansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci a tsakaninsu. Da haka ne kawai za su tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa daga bisani a cika kasa da adalci da daidaitawa bayan an cika ta da zalunci munanawa kamar yadda Allah Ta’ala Ya yi alkawari.

“Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayiNa salihai ne masu gadon ta. Lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada.” Surar Anbiya’i: 105-106.

Hadisai kuma sun zo da silsila dabam-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.A.) da kuma Imamai (A.S) cewa Mahadi (A.S) daga ’ya’yan Fatima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da daidaitwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai. Karin bayani zai zo filla filla a sahen. Abinda Muka yi Imani da shi game da Mahadi (A.S.).

Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abinda aka lillika masa na daga bidi’a da bata kuma ya tserar da Bil Adama, Ya kubutar da su daga abinda suka kutsa ciki na daga fasadi gama gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da koyarwar kyawawan dabi’u da ruhin dan Adamtaka. Allah Ta’ala Ya gagagauta bayyanarsa Ya saukake hanyar bayyanarsa.

 

20- Imaninmu Game da mai Shara’anta Musulunci.

Mun yi imani da cewa ma’abucin sakon addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi, kuma shi ne cikamakin Annabawa shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar kuma yadda shi ne shugaban Bil Adama baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamar shi kuma a kyawawan dabi’u kuma shi yana kan manyan kyawawan dabi’u. Allah Ta’ala Yana cewa: “Lalle shi kana kan manyan halayen kwarai.masu girma. Surar Al- kalam: 4.

Wannan kuwa tun daga farkon tasowarsa ne har zuwa ranar tashin Alkiyama.

Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya siffantashi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa:

“Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mafi tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai, da kuma mabubbugar hikima.”

Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminina (A.S.) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa, ya shirya kayan aikinsa. Yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastun makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo da duwatsu masu tsauri.”

Nahajul Balagha Huduba ta 108.

 

21- Imaninmu Game da Alkur’ani Mai Girma.

Mun yi imani cewa Alkur’ani wahayin Ubangiji ne da ya sauko daga Allah a harshen AnnabinSa, akwai bayanin kome da kome a cikinsa; shi ne Mu’ujiza madawwamiya wadda ta gagari bil Adama wajen karawa da ita a fasaha da azanci, abinda ya kunsa na daga hakika da sannai madaukaka. jirkita ko canji ko karkacewa ba sa shafar sa. Allah Ta’ala Yana cewa:

“Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma Mu gare shi lalle masu kariya ne”. Surar Hijri: 9.

Alkur’anin da ke hannunmu wanda ke karanta shi a yau shi ne wanda aka saukar, wa Annabi (S.A.W.A.) duk kuma wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, ko mai rikitarwa ko mai kuskurene dukaninsu kuma ba a kan shiriya suke ba; domin shi Akur’an zancen Allah ne wanda: “Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa.” Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da ke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa duk yayin da zamani ya dada tsawo ilimi da fasaha kuma suka dada ci gaba shi yana nan daram a kan abubuwan da yake kaddamarwa da daukarkar manufa da abubuwan da ya kunsa na ra’ayoyi babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar kuma yadda ba ya taba kunsar tawaya game da falsafa ta hakika da yakini sabanin littafan da malamai da manyan masanan falsafa kome matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani. Domin duk yayin da bincike ya ci gaba to yakan bayyana a sarari cewa rarrauna ne ko sabo ne ko kuma kuskure, hatta a gurin manyan masana falsafar kasar Girka kamarsu Sakarot da Aplato a Arostatle wadanda kowa da kowa daga cikin wadanda suka zo daga bayansu suka musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa.

Kazalika mun yi imani da mutunta Alkur’ani mai girma da daukaka shi a magana da kuma a aiki. Bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda aka dauka cewa yanki ne daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take.

Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya shafa kalmominsa ko harrufansa. “Babu mai shafa shi sai wadanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79.

Sawa’un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne kowa sai dai bayan yin ko kuma yin wanka a bisa asasin filla-fillan bayanan da ke cikin littafan fikihu.

Kazalika bai halatta a kona su ba, bai halatta a wulakanta shi ba, koda ta wace fuska ne kuwa da yake sananne a tsakanin mutane kamar jefarwa, ko sanya masa kazanta, ko shurin sa da kafa , ko sanya shi a guri; wulakantacce. Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi ya shiga cikin masu karyata addinin Musulunci da abubuwan tsarkakewarsa, kuma abin hukuntawa ne da ficewa daga addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

 

22- Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin Musulunci Da Sauran Shari’u Magabata.

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin addinin Musulunci za mu iya ja da shi mu tabbatar masa da mu’ujizarsa madawwamiya wato Alkur’ani mai girma kamar yadda Ya gabata game da kasancewarsa gagarabadau. Kazalika Alkur’ani shi ne hanyar sanya mana yakini mu da kanmu yayin da kokwanto ya fara shigar mu saboda irin tambayoyin da kan tasowa mutum a zuciya kamar yadda babu makawa kowane mutum mai yanci ya fada cikin irin wadannan tambayoyin yayin karfafa akidarsa da tabbatar da ita.

Dangane da shari’o’in da suka gabata kuwa kamarsu Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja kafin amincewarmu da Alkur’ani ko kuma idan muka raba kanmu da addinin Musulunci, babu hanyar da za mu bi mu gamsar da kanmu ko kuma mu gamsar da mai tambaya, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza tasu da ta saura kamar yadda Alkur’ani yake. Abinda mabinyan wadannan addinan ke dauke da shi kuma ana zarginsu a kan daukar da suke yi ko kuma sun sanya hannu a cikinsa. Babu wani abu da ke cikin littafan addinan da suka gabata da ke hannun mutane a wannan zamanin wanda ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya mai karfi da za ta iya yanke hanzari, ko dalili mai gamsarwa kafin a yi imani da Musulunci.

Sai dai kawai mu musulmi ya inganta ne a gare mu da mu gaskata Annabacin ma’abuta shari’unda suka gabata domin bayan gaskatawarmu da addinin musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukan abinda ya zo da shi, kuma a cikin abinda ya zo da shi akwai gaskata Annabcin Annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a sashen bayani game da abinda muka yi imani da shi game da Annabawa da littafansu.

Saboda haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, kiristanci da kuma abinda ya gabace shi bayan ya yi imani da Musulunci domin yin imani da shi imani da su ne, imani da shi imani ne da sakonnin da suka gabata da kuma Annabawan da suka shude. Bai wajaba a kan musulmi ya yi bincike game da gaskiyar mu’ujizar Annabawansu, domin abin kaddarawa shi ne cewa shi musulmi ne kuma ya yi imani da su saboda imaninsa da Musulunci kuma ya wadatar.

Na’am, idan da mutum, zai yi bincike game da addinin Musulunci ya ji cewa bai gamsu ba to lalle ne a kan kamar yadda hankali da kuma wajabcin neman ilimi suka wajabta Ya yi bincike game da addimin kirista domin shi ne addinin karshe kafin musulunci. Kazalika idan ya bincika addinin kirista bai gamsu ba ta sai kuma ya dukufa a kan addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zaiyi ta bincike har sai ya kai ga yakini yana binciken addinan da suka gabata har Ya tabbatar da ingancinsa Ya yi imani da shi ko kuma rashin ingancinsa ya yi watsi da su baki daya.

Wato sabanin wanda ya tashi a addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da addininsa ba zai wadatar da shi ba ya bar binciken addinin Nasaranci da kuma addinin Musulunci bilhasali ma aiki da hankali da neman sa wajibi ne a kansa - kamar yadda hankali ya hukunta, haka nan shi ma addinin Kiristanci ba isar masa ba ya zama ya yi imani da Almasihu (A.S.) wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa. Domin Yahudanci da addinin kirista ba su kore shari’ar da za to daga bisani ba; wadda za ta shafe ta, kazalika Annabi (A.S.) bai ce babu Annabi bayan shi ba sabanin haka ma Annabi Isa (A.S.) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma yayin da Isa dan Maryama Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abinda ke gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da ke zuwa bayana, sunansa Ahmad. Sai dai a lokacin da Ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.” Surar Saff: 6.

Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da addininsu kafin su yi bincike game da shari’ar da ta biyo bayansa wato kamar shari’ar addinin Kirista, da kuma addinin Yahudanci dangane da Musulunci. Wajibi ne kamar yadda yake a bisa dabi’ar hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga baya. Idan ingancinta Ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta a addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su ci gaba da bin addininsu na da tare da riko da shi.

Shi kuwa musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci to ba bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai a kaddare an san cewa ya yi imani da su don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da ita? Abin kawai da ya hukunta masa game da su shi ne cewa Shari’ar Musulunci ta ya shafe su don haka bai wajaba a yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littafansu ba.

Wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa shi ne saboda cewa Annabin Musulunci Muhammadu (S.A.W.A.) Ya ce: “Babu wani Annabi bayana.”[10] Kuma shi mai gaskiya ne kuma Amini. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai ba wani abu ba ne face wahayi da ake yiwo wahayinsa” Surar Najmi: 3-4.

Don haka saboda mene ne ba zaa bukaci hujjar da’awar Annabcin da aka yi daga baya ba idan har mai da’awar ya yi da’awa?

Na’am yana kan musulmi ya yi bincike bayan tsawon kokaci tsakaninsa da wanda ya kawo sakon, a kuma sami Mazhabobi da tafarkuna dabam-daban Ya yi bincike Ya bi hanyar da ta fi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar wa wanda ya kawo sakon Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukan hukunce hukuncen da shari’a ta zo da su kamar yadda aka saukar.

Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba, jama’a-jama’a sun rarraba, babu salla guda, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai ba hatta a bangaren mu’amala... don haka yaya zai yi? Da wace irin hanya zai yi salla? Da wace irin fuska na daga ra’ayoyi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa kamar aure, da saki, da gado da saye da sayarwa da zartar da haddi, da sauransu?

Kuma sam bai halatta gare shi ya bi ra’ayin iyaye ba ko ya koma ga abinda zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakina shi da kansa tsakaninsa da Allah Ta’ala domin babu wata zazzagawa a nan ba rufa-rufa, babu raragefe babu zurfafawa.

Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah. Ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai aibata shi a kan bin ta da aiki da ita ba. Bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai.” Surar Alkiyama: 36.

“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne.” Surar Kiyama: 14.

“Lalle wannan fadakarwa ce don haka wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa.” Surar Muzammil: 19.

Tambaya ta farko da za ta fara taso masa ita ce, shin ya kama tafarkin zuriyar gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Bait, zuriyar gidan Manzo (S.A.W.A.) shin tafarkin Imamiyya “Isna Ashara’, masu bin Imamai sha biyu, shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori dabam-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi daga cikin Mazhabobi hudun nan ne ko kuwa daga wasu Mazhabobi dabam daga cikin wannan bangaren? Haka nan dai tambayoyi za su yi ta tasowa ga duk wanda ba ya tunani ’yanci da zabi har ya kai ga gaskiya abar dogaro.

Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bayani a kan abinda ke biye da ita game da akidar Imamiyya Isna Ashariyya, Masu bin Imamai goma sha biyu.

 

[1]- Imam Aliyu Bin Abi Talib (a.s.) yayin da yake bayani ya siffanta fara halitta sama da kasa da halitta. Annabi Adam (A.S.) da kuma ambata Annabawa da aiko ya fada a hudubarsa cewa: “Kuma Subhanu Ya zabi Annabawa daga cikin ‘ya’yansa (Adam) Ya karbi Alkawarinsu a kan wahayi da kuma amanarsu a kan isar da sako. Yayin da yawancin halittunSa suka canja suka jahilci hakkinSa, suka riki ababan bauta tare da Shi shedanu suka fitsare su daga saninSa, suka yanke su daga bautarSa. Sai Ya aiko musu da ManzanninSa, kuma Ya bibiyar musu da AnnabawanSa domin su sake shiryar su ga alkawarin halittarsu, su tunatar da su mantattun ni’imominSa kuma su kafa musu hujja da isar da sako, su farfado da abubuwan da hankali ya mance, su nuna musu ayoyin kudura, na daga rufin da ke dage a samansu, da shinfidar da ke sanye a karkashinsu da abincin rayuwarsu, da ajalin da ke kare su, da gajiya da ke tsofar da su, da faruwar al’amura dake bibiye da su, kuma Allah bai taba barin bayinSa babu Annabi aikakke ko kuma littafi saukakke ba, ko kuma wata hanya bayyananniya ba. Manzanni da karancin mabiya ba ya sa su gaza ko kuma yawan masu karyatawa gare su, duk wanda ya gabata daga cikinsu kan sanar musu wanda zai zo daga bayansa ko kuma wanda ya zo daga baya ya sanar da yanda ya gabance shi. A kan haka karnoni suka yi ta shudewa, zamunna suka yi ta wucewa, iyaye suka yi ta gabata Annabawa suka yi ta biyowa, har Allah subhanahu ya aiko Muhammadu Rasulullahi sallallahu Alaihi wa alihi domin aiwatar da alkawarinSa da cika AnnabcinSa da Ya karbi alkawari a gurin AnnabawanSa wanda sunansa mashahuri ne, haihuwarsa kuma mai girme ce. A lokacin mutanen bayan kasa al’ummu ne a rarrabe, masu ra’ayoyin zukata dabam-dabam, da hanyoyi mabambanta, tsakanin masu kamanta Allah da halittunSa, ko kuma wuce iyaka a sunanSa, ko kuma mai nuni zuwa ga waninSa, sai Allah Ya shirye su da shi daga bata, Ya tserar da su da kokarinsa daga jahilci.” Nahjul Balagha Huduba ta. 1.

[2] - Aduba sharhin Almakasid Juzu’i 5 shafi na 50, da kuma Al- Ganiyyatu Fi Usuluddin shafi na 161.

Sayyid Murtadha ya ambata a cikin littafin Tanzihil Anbiya da nassi kamar haka: “Asahabul Hadis da Hashwaiyawa sun halatta wa Annabawa aikata manyan zunubai kafin a ba su Annabci. Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka halatta wa Annabawa aikata sabo hatta bayan karbar Annabcin in banda karya a kan al’amuran shari’a, akwai ma wadanda suka halatta karyar amma da sharadin a boyewa ba bayyanawa ba, akwai ma wadanda suka halatta a kowane hali, su Mu’utazilawa kuwa sun haramrta cewa Annabawa na aikata sabo babba ko karami kafin Annabci da sukuma bayan ba su Annabcin amma sun halatta aukuwar abinda bai kai karamin zunubi ba gare sukafin Annabci da kuma bayan Annabcin amma sun yi a kan Shugaban Manzanni Muhammadu (S.A.W.A.) wasu sabi daga cikinsu akwai wadanda suka ce zai iya aikata kananan ayyukan sabo haka nan da gangan, daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce atabau sam Annabawa ba sa taba aikata wani abu da suka san cewa sabo ne sai dai kawai fuskar ba shi wata ma’ana ta dabam. An hakaito daga Nizam da Ja’afar Bin Mubasshir da kuma wasu jama’a da suka bi su a kan cewa aikata sabo daga gare su ba ya yiwuwa sai dai a kan mantuwa da rafkanuwa kuma za a kama su da haka koda kuwa an yafewa al’ummunsu saboda karfin saninsu da kuma martabarsu.

Tanzihul Anbiya: Gabatarwa.

[3]- Ma’anar Isma a luga ita ce: Abu da ke kange mutum daga wani abu wato kamar ya kange shi daga aukuwar wani abu da ba ya so. Akan ce wane ya yi isma da dutse idan ya yi kariya da shi, da haka ne ake kiranta Isma wato fakewa a dutse don kariya da shi ya zo a Lisanil Arab cewa: “Isma ita ce kariya, a kan ce na kare wani sai ya karu, na yi kariya da Allah idan har ya tsaru daga sabo da tausasawarSa.

Isma daga Allah Ta’ala kuwa ita ce: Muwafaka da ke kubutar da mutum daga abinda da ya so idan har ya zamanto ya aikata aikin biyayya, kamar yadda muke mika igiya ga mutumin da kogi yake kokarin dulmuyarwa ya kama ya tsira da ita, Allah Ta’ala ya bayyana wannan ma’ana da a littafinSa da cewa: “Ku yi riko da igiyar Allah baki daya” SurarAli Imran: 103. A nan abin nufi da igiyar Allah shi ne addininsa.

Ya zo daga Imam Zainul Abidin (A.S.) cewa yayin da aka tambaye shi ma’anar ya ce: Shi ne mai riko da igiyar Allah, igiyar Allah kuma shi ne Alkur’ani da lmam ba sa taba rabuwa har zuwa ranar tashin kiyama, Imam yana shiryarwa ne zuwa ga Alkur’ani shi ma Alkur’ani yana shiryarwa zuwa ga Imam. Wannan shi ne fadin Allah Ta’ala “Lalle ne shi wannan Alkur’ani yana shiryarwa zuwa ga wadanda suke su ne mafiya daidai.” Surar Isra’i: 9.

Biharul Anwar Juzu’i na 25 shafi na 194 da kuma farko Al-makalat na shaikh Mufid Juzu’i na 4 shafi na 34. Da kuma Lisanul Arab Juzu’i na 12 shafi na 403 bayani game “Asama”.

[4]- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur’ani wadda take kwadaitarwa da a yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: “Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu.” Surar Nisa’i: 13. da kuma fadin Allah Ta’ala cewa: “Kuma wanda ya bi Allah da Manzon to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi niima gare su,” Nisa’i:69 da kuma fadinsa cewa: “Kuma wanda ya bi Manzon Allah to Lalle ya bi Allah ne” surar Nisa’i: 80 da kuma: “Lalle hakika gare ku daga Mazon Allah akwai kyawawan abin koyi ga duk wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira kuma ya ambaci da yawa” Surar Ahzab: 22 da kuma fadin Allah Ta’ala: “Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa to lalle ya rabbonta da rabo mai girma”. Surar Ahzab: 71.

[5]- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur’ani da ke kwadaitar da biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: “Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna da koramu ke gudana a karkashinsu.” Nisa’i: 13

“Kuma wadanda suka yi da’a ga Allah da ManzonSa to wadan suna tare da wadanda Allah ya yi ni’ima gare su”. Surar Nisa’i: 69.

[6]- “Ku ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar gare mu da abinda aka saukar zuwa ga Ibrahima da Isma’ila da Ishaka da Yakuba da Jikoki da abinda aka ba wa Musa da Isa da abinda aka ba wa Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma rarrabewa a tsakanin kowa daga cikinsu kuma mu masu sallamawa ne a gare shi.” Surar Bakara: 136

“Amma tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani daba inda aka saukar zuwa gareka da abinda aka saukar kafin kai kuma suna masu tsai da salla suna ba da zakka suna masu imani da Allah da ranar lahira wadannan za mu ba su lada mai girma” Surar Nisa’i: 162.

[7]- Ya zo aruwayoyi da hadisai cewa adadin Annabawa ya kai dubu dari da ashirin da hudu dari uku da ashirin da uku daga cikinsu ne, ko kuma dari uku da ashirin da biyar a bisa sabanin ruwaya, su kuma wadannan Annabawan sunan mafi yawansu bai zo a Alkur’ani ba. Allah Ta’ala na cewa: “Kuma lalle hakika mun aika wasu Manzannin kafin kai, daga cikinsu akwai wadanda muka ba ka labarinsu daga cikinsu akwai wadanda ba mu ba ka labarinsu ba” Surar Ghafir: 78.

Adadin wadanda sunansu ya zo a Alkur’ani kuwa ashirin da shida ne kamar haka:-

1- Annabi Adam (A.S.) sunansa ya zo sau 18 a Alkur’ani, game da shi Allah Ta’ala yana cewa: “Lalle Allah ya zabi Adama da Nuhu da zuriyar Ibrahim da zuriyar Imran  a kan dukan talikai.” Surar Al- Imran 33, Kamar Kuma yadda ya zo da Kiran Bani Adam sau Bakwai.

2- Annabi Nuhu (A.S.) sunansa ya zo a Alkur’ani sau 43 game da shi Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa ya zauna a cikinsu har shekaru dubu babu hamsin” Surar Ankabutu: 14.

3- Annabi Idris (A.S.) sunansa ya zo sau biyu a Alkur’an, Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma ka ambata Idris a cikin littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya Annabi” Surar Maryam: 56.

4- Annabi Hudu (A.S.) Sunansa ya zo sau goma a cikin Alkur’ani, game da shi Allah Ta’ala na cewa: “Kuma zuwa ga Adawa dan’uwansu Hudu, ya ce ya mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa baicin Shi.” Surar A’araf: 69 da Surar Hudu: 50.

5- Annabi Salihu: Sunansa ya zo sau tara a Alkur’ani, game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle Mun aika wa Samudawa Dan’uwansu Salihu ku bauta wa Allah sai suka zamanto bangarori biyu suna husuma.” Surar Namli: 45.

6- Annabi lbrahim’i (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau 69 a Alkur’ani, game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle Mun aika Ibrahima kuma Muka sanya Annabci da littafi a zuriyarsu...” Surar Hadid: 26.

7- Annabi Ludu (A.S.) sunansa ya zo a gurare 26 a Alkur’ani game da shi Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma lalle Ludu tabbas yana daga Manzanni”. Surar Saffat: 133.

8- Annabi Isma’il (A.S.): Ambaton sunansa ya zo a gurare goma sha daya a Alkur’ani game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrahima da Isma’ila da Ishaka da Yakuba...” Surar Nisa’i: 163.

9- Alyasa’u: Ambaton sunansa ya zo sau biyu a Alkur’ani: game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Da Isma’ila da Alyasa’u da Yunusa da Ludu kuma kowanne mun fifita shi a kan talikai.”

10- Zulkifli: An ambace shi sau biyu a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma ka ambaci Isma’ila da Alaysa’u da Zulkifli kuma duka suna daga zababbu.” Surar Sad: 48.

11- Annabi Ilyasu (A.S.) An ambace shi sau biyu Alkur’ani Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle Ilyasu tabbas na daga cikin manzanni.” Surar Saffat: 123.

12- Annabi Yunus (A.S.) Ambatonsa ya zo sau hudu a Alkur’ani. Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma lalle Yunusa Tabbas yana daga cikin Manzanni.” Surar Saffat: 139.

13- Ishak (A.S.) Ambaton sunansa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma mun yi Masa albishir da Ishaka Annabi daga cikin Salihai.” Surar Saffat: 112.

14- Annabi Yakub (A.S.) An ambaci sunansa sau goma sha shida a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma Muka yi wahayi ga Ibrahima da Isma’ila da Ishaka da Yakuba da Asbata da Isa...” Surar Nisa’i:

15- Annabi Yusuf (A.S.) Ambatonsa ya zo sau ashirin da bakwai a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan Muke sakamtawa masu kyautatawa.” Surar An’am: 84.

16- Annabi Shu’aib (A.S.) Sunansa ya zo sau goma sha daya a Alkur’ani. Game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma ga Madyana Dan’uwansu Shu’aibu.” Surar A’araf: 85, Hud: 84, Ankabut: 36.

17- Annabi Musa (A.S.) Ambatonsa ya zo sau dari da talatin da shida a Alkur’ani. Game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle tabbatacce Mun aiki Musa da ayoyinMu kan cewa ka fitar da al’ummarka daga duffai zuwa ga haske kuma ka tunatar da su game da ranakun Allah lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga dukan mai hakuri mai yawan godiya.” Surar Ibrahim: 5.

18- Annabi Haruna (A.S.) Ambaton sunansa ya zo sau ashirin a Alkur’ani. Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma Muka ba shi Dan’uwansa Haruna Annabi daga rahamarMu.” Surar Maryam: 53.

19- Annabi Dawud (A.S.) Ambatonsa ya zo sau goma sha shida a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimana kuma Mun ba wa Dawuda Zabura.” Surar Nisai: 163.

20- Annabi Sulaiman: Ambatonsa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur’ani. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle hakika Mun ba wa Dawuda da Sulaimanu ilimi” Surar Namli: 15.

21- Annabi Ayyuba (A.S.) An ambace shi sau hudu a Alkur’ani. Game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Ibrahima da Isam’ila da Ishaka da Ya’akuba da Asbata da Isa da Ayyuba.” Surar Nisa’i: 163.

22- Annabi Zakariyya (A.S.) Ambatonsa ya zo sau bakwai a Alkur’ani. Game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyasu kowane yana daga Salihai” Surar An’am: 85.

23- Annabi Yahya (A.S.) Sunansa ya zo sau biyar a Alkur’ani. Game da shi Allah Ta’ala Yana cewa: “Ya Yahya ka riki littafi da karfi kuma Mun ba shi hukunci yana yaro.” Surar Maryam: 12.

24- Annabi Isma’ila Sadikul Wa’ad (A.S.) shi wani Isma’ilan ne dabam banda dan Annabi Ibrahim (A.S.). Game da shi Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma ka ambaci Isma’ila a cikin littafi lalle shi ya kasance nami gaskiyar Alkawari kuma ya kasance Manzo Annabi.” Surar Maryam: 54.

25- Annabi Isa (A.S.) Sunansa ya zo sau ashirin da shida a Alkur’ani. Game da shi ne Allah Ta’ala Yake cewa: “Lalle abin sani kawai shi ne cewa Al-Masihu Isa dan Maryama Manzon Allah ne kuma KalmarSa. Ya jefa ta zuwa ga Maryama...” Surar Nisa’i: 171.

26- Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) Ambatonsa da sunan Muhammad ya zo sau hudu a Alkur’ani, da Ahmad kuma ya zo sau daya. “Kuma Muhammadu bai kasance ba face Manzo kuma Manzanni sun gabata kafin shi.” Surar Al- Imran: 144.

Daga cikin Annabawa akwai wadanda aka kawo siffofinsu ba sunayensu ba a Alkur’ani. Allah Ta’ala na cewa: “Shin ba kaga wasu mashawarta ba daga Bani Isra’ila bayan Musa, yayin da suka ce ga wani Annabinsu, nada mana wani sarki mu yi yaki a tafarkin Allah”. Surar Bakara: 246.

Su Manzannin an rarraba su ne an aika su zuwa ga al’ummu dabam daban a zamunna dabam-daban. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma lalle hakika Mun aika Manzo ga kowace Al’umma”. Surar Nahl: 36.

Wasu Annabawa da Manzannin kuma an fifita su a kan wasu: Allah Ta’ala Yana cewa: “Wadancan Manzannin Mun fifita wasunsu a kan wasu daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya daukaka sashensu a daraja.” Surar Bakara: 253

“Kuma lalle hakika Mun fifita wasun Annabawa a kan wasu kuma Mun ba wa Dawuda Zabura.” Surar Isra’i: 55.

Mafifita daga cikin Annabawa da Manzanni su ne Ulul Azami su biyar wadanda game da su Allah Ta’ala ke cewa: “Kuma yayin da Muka karba daga Annabawa alkawarinsu da kuma daga gare ka da kuma daga Nuhu da Ibrahima da Musa da Isa Dan Maryama kuma Mun karba daga gare su alkawari mai tsanani.” Surar Ahzab: 7.

“Don haka ka yi hakuri kamar yadda ma’abuta karfin himma daga Manzanni suka yi hakuri.” Surar Ahkaf: 35.

Kuma sananne ne cewa himmar Annabawa ta sha bamban, ba daya take ba a gurin dukkaninsu kamar yadda Allah Ta’ala ke bayyana haka da cewa: “Kuma lalle hakika mun yi Alkawari ga Adam kafin wannan sai ya manta kuma ba Mu sami karfin himma gare shi ba.” Surar D.H.: 115.

Mafificin Annabawa da Manzanni baki daya shi ne cikamakinsu, Annabi Amintacce Muhammad Dan Abdullahi Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi da zuriyarsa tsarkakku. A duba Biharul Anwar Juzu’i na 11 shafi na 77 da kuma Alkhisal. Al- Amali Shaikh Mufid, da Kanzul Ummal, 32276, 32277, 32282, da sauransu, da Tafsirin Al- Mizan Juzu’i na 2, da Mizanil Hikma Juzu’i na 7 da dai sauransu.

[8]- Ishara ga Fadin Allah Ta’ala “Lalle addini a gurin Allah shi ne musulunci” Al- Imran: 19. “Kuma duk wanda ya bi wani addini ba musulunci ba za a taba karba masa ba kuma ranar lahira yana daga cikin masu hasara.”

[9]- “Kuma lalle Mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayiNa Salihai ne masu gadonta.” Anbiya’i: 105.

[10]- Sahih Muslim Juzu’i na 3 shafi na 1471 hadisi na 1842 da Musnad Ahmad Juzu’i na 3 shafi na 32, da Mu’ujamul Kabir Juzu’i na 8 shafi na 161 hadisi na 7617 da sunanu Baihaki Juzu’i na 8 shafi na 144 da Amali shaikh Mufid: 33.

 

عنوان الکتاب