FASALI NA FARKO

 

Sanin Ubangiji Imaninmu Game da:

  1.  Allah Ta’ala

  2.  Tauhidi

  3. Siffofinsa Ta’ala

  4. Adalci

  5. Hukuncin Allah da Kaddara

  6. Al-Bada’

  7.  Hukunce - Hukuncen Addini

  8. lmaninmu Game da Hukunce-Hukuncen Addini


 

5- Imaninmu Game da Allah Ta’ala

Mun yi jmani cewa Allah Madaukaki Daya ne makadaici babu wani abu kamar Shi, wanzazze bai gushe ba kuma ba Ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai Iko, Mawadaci, Mai Ji, Mai gani, Ba a siffanta Shi da abinda ake siffanta halittu, Shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jiki ba ne kuma ba rabi ba ne, ba Shi da nauyi ko sakwaikwaya, ba Shi da motsi ko lambo, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi.[1] Kamar kuma yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi, maganai ba sa riskar Sa Shi kuwa yana riskar maganai.

Duk wanda Ya ce ana kamanta Shi to Ya zamar da Shi halitta ke nan, wato Ya suranta fuska gare Shi da hannu da kuma idaniya, ko kuma cewa Shi yana saukowa zuwa saman duniya, ko kuma kuma cewa zai bayyana ga `yan aljanna kamar wata, ko kuma makamantan wannan,[2] to lalle yana matsayin wanda Ya kafirce da Shi ne, wanda Ya jahilci hakikanin mahaliccin da Ya tsarkaka daga nakasa, kai duk ma abinda muka bambance Shi da sake-saken zukatanmu a mafi daldalewar ma’anarsa to Shi abin hali’tta na kamar mu wanda kuma mai komawa ne gare mu, kamar yadda Imam Bakir (A.S.) fassara Shi gare mu da bayyani mai hikima da kuma zurfin ma’ana ta ilimi mai zurfi.

Har ila yau ana hade duk wanda Ya ce yana nuna kanSa ga halittunSa ranar Kiyama,ana hade Shi, a cikin kafirai[3], koda kuyaa kore maSa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai kuma irin wadannan masu da’awa sun sandare ne kawai a kan wasu laffuza na zahiri  na Alkur’ani ne ko kuna wasu hadisai kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su a bayansu. Don haka suka gaza yin aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai suka hukunta da kuma ka’idojin lakabi da kuma aror ma’anar kalma ba.

 

6- Imaninmu Game da Tauhidi

Mun yi imani Ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahiya, kamar yadda ya wajaba a kadaita Shi a zatinSa haka nan muka yi imani da cewa Shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarSa, kazalika Ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinSa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biya ahalitta da arzutawa kuma ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukan kamala kuma ba Shi da kwatankwaci.

Kazalika mun yi imani da kadaita Shi a bauta. Bai halatta a bauta wa waninSaba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani nau’i nanau’o’in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.

Duk wanda Ya yi shirka Ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusacin wanin Allah Ta’ala, hukuncinsa Shi wanda Ya yi haka hukuncin wanda Ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.[4]

Amma abinda Ya shafi ziyatar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusaci ga wanin Allah ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarKin Shi’a Imamiyya suke so su rayawa suna masus jahiltar hakikanin al’amarin su.[5] Sai dai ma wani nau’i ne na kusaci ga Allah Ta’ala ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusaci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar’yan’uwa a addini, da kuma taimakon fakiri.

Don zuwa gaishe da marar lafiya Shi a kan kansa, alal misali, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusaci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusaci ga marar lafiyar ba ne da zai zamar da aikata Shi Ya zama bauta ga wanin Allah Ta’ala ko kuma shirka a bautarSa. Kazalika sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar yan’uwa.

Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari’a al’amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.[6]

Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufin da su kawai Shi raya al’amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin addinin Allah da tare da su “wancan duk wanda Ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyakan ibadar zukata.” Surar Hajj: 32.

 

7- Imaninmu Game da Siffofinsa Ta’ala

Mun y.i imani cewa daga cikin siffofinsa Ta’ala akwai wajiban siffofi tabbatattu na Hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi da kudura, da wadata, da irada, nufi, da rayuwa wadanda su kansu su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne kari ne dabam a kan zatinSa. Ainihin samuwarSa ba wani abu ba ne a kan zatinSa, kudurarSa kuma dangane da rayuwarSa, rayuwarsa ita ce kudurarSa, Shi mai kudura ne ta Yadda yake rayayye, kuma rayayye ta yadda Yake mai kudura, babu tagwaye tsakanin siffofinSa da samuwarSa, haka nan kuma a sauran siffofinSa na kamala.

Na’am siffofinSa sun sha bamban a ma’anoninsu da manufofinsu amma ba wai a hakikaninsu da samuwarSa ba saboda idan da sun kasance haka to da lalle Ya kasance an sami wajibabbun samammu da dama kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ba wannan kuwa Ya saba wa Akidar Tauhidi.[7]

Tabbatattun siffofi kamarsu halitta da arzutawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta Hakika, ita ce kasancewarSa mai tafiyar da alimauran bayinSa.Wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la’akari iri dabam-daban.

Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru wadanda har wa yau ake kiran su siffofin Jalala, siffofi girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarSa mai yiwuwar samamme ba wajibin samamme ba, ma’anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore-rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu, wato dai kore dukun nakasa.

Sa’an nan kuma tushen kore kasancewarSa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarsa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarSa wajibin samamme, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na komala, don haka siffofin Jalala korarru dai a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah Ta’ala kuwa Shi kadai Ae ne Makadaici ta kowace fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawarwa a hakikaninSa makadaici abin nufi da bukata.

Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda Ya yake da ra’ayin cewa siffofin tabbatarwa wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru. Saboda haka ne Siffofin da suke korarru. Saboda Ya yi masa wahala Ya fahinci cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka Ya kintata cewa siffofin, subutiyya, tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah, duk suna komawa ga korarrun siffani ne domin kawai Ya natsu da fadin kadaitaikar zati da rashin yawaitarsa sai kawai Ya auka a cikin abinda Ya fi shi muni, domin zamar da ainihin zati wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa, wanda ba shi da duk wata nakasa, da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da samamme wajibin sanuwa ba, Ya sanya shi Ya aininin ma shi ne rashi kuma ainihin korarre,[8] Allah Ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntubewar duga-dugai.

Kamar kuma yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan tarayya ke nan ga wajibin samamme, ko kuma kenan ya ce Shi mai hauhawa ne sashe bisa sashe.[9]

Sayyyidina Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa Ya ce:

Cikar Ikhlasi gare shi kuwa Shi ne kore siffofi gare Shi saboda shaidar cewa dukan abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukan abin siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda Ya siffanta Allah to ya gwama shi wanda Ya gwama Shi kuwa ya tagwaita shi wanda Ya tagwaita Shi kuwa Ya zamar da Shi sassa-sassa, wanda sanyashi sassa-sassa kuwa to lalle Ya jahilce Shi.”[10]

 

8- Imaninmu Game da Adalci

Mun yi imani da cewa: Lalle daga cikin siffofin, Allah Tla’ala, As-Subutiyya kamaliyya wato tabbatattun siffofin kamala akwai cewa shi Adaline ba azzalumi ba, ba Ya karkacewa a hukuncinsa ba Ya tabewa a hukuncinsa, zai yi sakayya ga masu biyayya, kuma yana gare Shi Ya hukunta masu sabo, ba Ya kallafa wa bayinsa abinda ba za su iya ba, ba zai musu ukuba fiye da abinda suka cancanta ba.[11]

Kuma mun imani cewa Allah Ta’ala ba Ya barin abu mai kyau matukar ba gwamuwa Ya yi da abu wanda shi ne mafi kyau ba kuma ba Ya aikata mummuna saboda Shi Allah Ta’ala Mai kudura ne a kan Ya aikata kyakkyawa Ya bar mummuna tare da kaddara saninsa game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan. Babu wani kyakkyawan (aiki) da aikatashi zai cutar da Shi balantana Ya bukaci barin sa, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa ballantana Ya aikata shi kuma duk da haka mai hikima ne babu makawa aikinSa Ya kasance Ya dace dahikima kuma daidai gwargwadon tsari mafi kamala.[12]

Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki -shi Ya daukaka ga aikatawa- to da al’amarin hakan ba zai zamanto Ya rabu da daya daga cikin surorin nan hudu:

1- Ya kasance Ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.

2- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi

Amma kuma Ya zamanto Ya aikata shi ala tilas Ya gaza barin aikata shi.

3- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi ba a kuma tilasta shi Ya aikata ba bai kuma gaza kin bari ba amma Ya zamanto Yana bukatar aikatawa.

4- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi, ba mai aikata shi ala tilas ba, ba kuma mai bukata Ya zama Ya takaita ke nan da aikata shi a bisa Sha’awa da wasa da bata lokaci.

Dukan wadannan surori kuwa sun koru ga Allah Ta’ala, Kuma tabbatar da nakasa gare Shi alhali Shi kuwa zallan kamala ne saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa Shi tsarkakakke ne daga zalunci da kuma aikata abinda yake mummuna.

Sai dai kuma wani bangare daga cikin musulmi sun halatta wa Allah Ta’ala aikata mummuna,[13] sunayeNsa sun Tsarkaka, suka halatta cewa zai iya hukunta musu biyayya, Ya kuma shigarda masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa Yana iya kallafa wa bayinSa abinda Ya fi karfinsu da abinda ba za su iya aikatawa ba amma kuma duk da haka Ya azabtar da su idan har suka bari ba su aikata shi ba. Har ila yau kuma sun halatta zalunci na iya faruwa daga gare Shi da tabewa, da karya da yaudara, kuma Ya aikata aiki ba tare da wata hikima,ba ba da manufa ba, ba da amfani ba, ba da fa’ida ba da hujjar cewa “Ba a tambayar sa a kan abinda yake aikatawa su kuwa ana tambayar su.” Surar Anbiya: 23.

Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, mai Ja’irci, mai wauta ne, mai wasa ne, mai karya ne, mai yaudara ne, Yana aikata mummuna, Yana kuma barin kyakkyawa, Allah Ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa, daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa. Kuma Allah Ta’ala Ya ce:

“Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi.” Surar Mumin ayata 23. “Kuma Allah ba Ya son barna.” Surar Bakara: 31 “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu muna Masu wasa ba.” Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halitta Ajannu da Mutane ba face don su bauta Mini.” Surar Zariyat: 56.

 

9- Imaninmu Game da Wajabta Aiki.

Mun yi imani cewa Allah Ta’ala ba Ya kallafa wa bayinSa aiki sai bayan Ya tabbatar musu hujja a kansu[14] kuma ba Ya kallafa musu sai abinda za su iya aikata shi kuma suke da ikon aikata shi kuma suka san shi domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, wanda ba zai iya ba, da kuma Jahilin wanda ilimi bai isa zuwa gare shi ba, ba wai Ya ki neman ilimin da ganganci ba.

Amma shi kuwa Jahili wanda Ya ki neman sani da gangan alhali yana da damar samun ilimin hukunce-hukunce da ayyukan ibada to shi ne mai amsa tambaya a gurin Allah Ta’ala, kuma shi za a yiwa ukuba a kan sakacinsa domin wajibi ne a kan kowane mutum Ya koyi abinda yake bukata           na daga hukunce-hukuncen shari’a.[15]

Kuma mun yi imani cewa: shi Allah Ta’ala babu makawa Ya kallafa wa bayinsa ayyuka Ya kuma sanya musu shari’o’i abinda na amfani da kuma alheri gare su a cikinta domin Ya sanya su a kan hanyoyin alheri da rabbonta dindindin, sa’an nan kuma Ya shirye su zuwa ga abinda Yake shi ne maslaha kuma Ya gargade su game da abinda yake akwai fasadi da barna a cikinsa da kuma cutarwa gare su da kuma mummunan karshe gare su. Koda kuwa Ya san cewa su ba za su bi Shi ba, domin wannan tausasawa ne da kuma rahama ga bayinSa don kasancewarsu sun jahilci mafi yawancin amfanin kansu da hanyoyinsu a nan duniya da kuma lahira. Sun jahilci da yawan abubuwan da za su jawo musu cuta da hasara, Shi kuwa Allah Ta’ala Shi ne Mai Rahama mai Jin kai a ainihin zatinSa, Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa kuma har abada bai rabu daga gare shi.

Wannan tausasawa kuwa ba za ta gushe ba, don bayinsa sun kasance sun bijire sun ki bin sa, sun ki kayyaduwa da umarce-umarcensa kuma sun ki hanuwa da hane-hanenSa.

 

10- Imaninmu Game da Hukuncin Allah da Kuma Kaddara

Jamar’ar Al- Mujabbira[16] sun tafi a kan cewa Allah Ta’ala shi ne mai aikata ayyukan halittu don haka sai Ya zamanto ke nan Ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma Ya yi musu azaba.

Sa’an nan kuma Ya tilasta su a kan yin da’a duk da haka kuma Ya ba su ladaa kai. Domin su suna cewa: Lalle ayyukansu alal hakika ayyukanSa ne ana dai dangata ayyukan gare su ne kawai don sassautawa donin su ne muhallin ayyukan, asalin wannan kuwa shi ne kasancewar su sun yi inkarin musabbabai na dabi’a a tsakanin abubuwa domin sun yi tsammani cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Allah Ta’ala mahalicci da ba Shi da abokin tarayya kuma Shi ne mai sabbabawa na ainihi ba waninSa ba.

Duk wanda yake fadin irin wannan ra’ayi kuwa to lalle Ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa Ya daukaka ga haka.

Wasu jama’a kuma wato-mufawwidha[17] sun yi imanin cewa Allah Ya sallama ayyuka ne ga halittu, Ya janye kudurarSa da hukuncinSa da kuma kaddarawarSa daga gare su, wato ma’ana danganta ayyuka gare shi Ta’ala yana nufin dangata nakasa gare shi, kuma samammun halittu suna da nasu musabbaban na musamman koda yake dai dukansu suna komawa ne ga musabbabi guda daya na farko wanda shi ne Allah Ta’ala.

Duk wanda yake fadin wadannan irin maganganu to lalle Ya fitar da Allah daga mulkinSa Ya kuma hadar da Shi a shirka da halittunSa.

Kuma mun yi Imani muna masu biyayya ga abinda Ya zo daga Imamanmu tsarkakakku da ke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu kuma tafarki matsakaici a tsakanin maganganun biyu, wanda irin wadancan ma’abuta tsaurin kan suka gaza fahintarsa wasu suka zurfafa wasu kuma suka yi kwauro, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da Ya fahince shi sai bayan karnoni.[18]

Ba abin mamaki ba ne ga wanda ba shi da masaniya game da hikimar Imamai (A.S.) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, da kuma hanya matsakaici ba a maganganun biyu Ya ce wannan batu ne daga cikin al’amuran da masana falsafa a Yammacin Turai na baya bayan nan suka gano alhali kuwa Imamai sun riga su tun kafin karni goma da suk wuce.

Imam Sadik (A.S.) yayin da yake bayanin hanyar nan matsakaiciya yana cewa: “Babu Jabru, tilastawa, kuma sallamawa, ayyuka baki daya sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.[19]

Wannan ma’ana girmanta na da yawa manufarta kuma na da zurfi. Abin nufi a takaice shi ne cewa: Lalle ayyukanmu a bangare guda ayyuka namu alal hakika kuma mu ne musabbabansu na dabi’a kuma suna karkashin ikonmu da iyawarmu. A daya bangaren kuma su ayyukan kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin ikonSa. Domin Shi ne mai ba da samuwa mai samar da ita. Bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana Ya zamanto Ya zalunce mu a kan yi mana ukuba idan har muka saba. Saboda muna da iko da kuma zabi a kan abinda muke aikatawa. Kuma bai sallama mana samar da ayyukanmu ba ballantana Ya zamanto Ya fitar da su daga karkashin ikonSa ba, Shi dai Shi ne Mai halittawa Shi ne kuma mai hukuntawa, Shi ne kuma mai umarni, Shi kuma Mai iko ne a kan kome, kuma a kewaye yake da bayinSa.[20]

Ko ta halin kaka dai abinda muka yi imani da shi game da hukuncin Allah da kuma kaddara shi ne cewa sirri ne daga asirran Allah Ta’ala duk wanda Ya iya Ya fahince shi yadda Ya dace ba tare kwauro ko zurfafawa ba to shi kenan, idan kuwa ba haka ba to ba wajibi ba ne Ya kallafa wa kama cewa sai Ya fahince shi daidai wa daidai, domin kada Ya je Ya bata akidarsa, kuma ta baci saboda wannan yana daga cikin al’amura masu wahala, har ma sun fi binciken al’amuran falsafa zurfi. Babu mai iya gane su sai ‘yan kalilan daga cikin mutane wannan shi abinda Ya sa da yawa daga cikin ma’abuta ilimin akida suka tabe.[21]

Don haka kallafa shi ma ga bayi kallafa abu ne da Ya fi karfin mutum wanda yake daidai da sauran mutane. Ya wadatar mutum Ya zamanto Ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga maganar Imamai tsarkaka amincin Allah Ya tabbata gare su cewa shi wani al’amari ne tsakanin al’amura guda biyu, babu tilastawa babu kuma sallamawa a cikinsa.

Kuma shi baya daga cikin jigo daga cikin jiga-jigan addini ballantana Ya zama kudurcewa da shi wajibi ko ta halin kaka filla-filla daram.

 

11- Imaninmu Game da Bada

“Bada” ga mutum: shi ne wani sabon ra’ayi Ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato Ya canja himmarsa da Ya yi a kan wani aiki da Ya kasance yana nufin aikata shi, wannan kuma saboda Jahilcine game da amfani da kuma nadama a kan abinda Ya riga Ya gabata daga gare shi.

“Bada” da wannan ma’anar Ya koru ga Allah Ta’ala. Domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa wannan kuwa Ya koru ga Allah Ta’ala Shi’a Imamiyya kuma ba su yarda da shi ba.

Imam Sadik Alaihis Salam Ya ce:

“Wanda Ya yi da’awar cewa Bada Ya auku ga Allah Ta’ala game da wani abu. Bada irin na nadama ta agurinmu wannan Kafirine a game da Allah mai girma.[22] Har ila yau kuma Ya ce: “Wanda Ya raya cewa wani abu Ya yi Bada ga Allah wanda da Ya kasance bai san shiba jiya to ni ba ni ba shi”.[23]

Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kamar nuni da ma’anar “Bada” yadda ta gabata. Kamar yadda Ya zo daga Imam Sadik Alaihis Salam cewa: “Bada bai taba yiwuwa ga Allah ba kamar yadda Ya yiwu gare shi ba a kan Isma’ila dana.”[24] Don haka ne wadansu marubuta daga cikin bangarorin musulmi suka dangata Bada ga Shi’a Imamiyya don yin suka ga mazhaba da tafarkin Ahlul Bait suka sanya shi Ya zama abin kyama ga Shi’a.

Sahihin al’amari a nan shi ne mu fadi kamar yadda Ya fada a Alkur’ani “Allah Yana shafe abinda Ya so kama Yana tabbarwa Asalin littafi kuma gare Shi Yake.” Surar Ra’ad: ayata 39.

Abin nufi shi ne cewa Allah Ta’ala na iya bayyana wai abu a bisa harshen Annabinsa ko waliyinSa ko kuma a zahiri wata maslaha ta sa bayyanawar sa’an nan daga baya kuma Ya shafe shi Ya zama ba abinda Ya bayyana da farko ba, kamar yadda Ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S.) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S.) Ya ga yana yanka shi.[25]

Wato kenan ma’anar maganar Imam Alaihis salam sai ta zama kenan cewa: Lalle babu wani abu da Ya bayyana ga Allah Ta’ala na daga al’amari a kan wani abu kamar yadda Ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa domin (Allah) Ya dauke shi (Isma’ila) Kafin shi (Imam Sadik (A.S.)) domin mutane su san, (cewa) shi (Isma’ila) ba Imami ba ne, A zahiri Ya riga Ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.[26]

Abu da yake da “Bada” a ma’ana kuma shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu sallallahu Alaihi wa ahlihi hatta ma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen shi Annabin namu sallallahu Alaihi wa ahlihi.[27]

 

12- lmaninmu Game da Hukunce-Hukuncen Addini

Mun yi imani cewa Allah Ta’ala Ya sanya hukunce-hukunce - wajibai da haram-haram da sauransu daidai da,maslaha,alheri ga bayinSa a cikin ainihin su ayyukan, abinda maslaharsa ta zama babu makawa sai da ita Ya sanya shi wajibi wanda kuma cutarwar da ke tare da shi ta kai matuka to Ya haramta shi wanda kuwa maslaharsa ta zama da kadan ta rinijayi cutarwarsa to Ya sanya mana shi mustahabi.

Kazalika ma sauran hukunce-hukuncen, wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuama tausasawarSa ga bayinSa.

Kuma lalle babu makawa Ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari[28], babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hakikanin hukuncin Allah a kansa koda kuwa tafarkin saninsa  a toshe yake gare mu.

Kuma har ila yau muna cewa lalle yana daga mummunan abu Ya zamanto Ya yi umarni da aikata abinda yake akwai cutarwa a cikinsa, ko kuma Ya hana abinda akwai maslaha a cikinsa.

Sai dai kuma wasu daga cikin bangarorin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne kawai abinda Allah Ta’ala Ya hana, kyakkyawa kuwa shi ne abinda Ya kyautata kuma Ya yi umarnin a aikata, ba wai ainihin maslaha da cutarwar a ayyukan suke ba, kuma babu kyawu ko rashin kyawu a ainihin zatin.[29] Wannan kuwa batu ne da Ya saba wa abinda hankali Ya wajabta.

Kazalizaka sun halatta cewa Allah na iya aikata mummuna Ya yi umarni da bu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma Ya hana abinda yake akwai maslaha a cikinsa. Ya riga Ya gabata cewa wannan irin magana akwai rashin girmamawa a cikinta kwarai. Saboda wannan magana na hukunta danganta jahilci da gazawa ga Allah, Allah Ta’ala Ya daukaka, daukaka mai girma ga barin irin wadannan al’amura.

A takaice dai: Abinda yake sahihi a akida shi ne mu ce: shi Allah Ta’ala ba Shi da wata maslaha ko fa’ida a kallafa wajibai da kuma haramata haramtattu sai maslahar da fa’idojin duka suna komawa ne gare mu a dukan ayyuka. Kuma babu wata ma’ana wajen a kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni ko aka hana aikatawa, Allah ba Ya umarni don wasa ba Ya hani haka banza shi kuma mawadaci ne ga barin bukatar bayinSa.


 

 

[1]- An ruwaito daga Amir’ul Muminin Imam (A.S.) a amsar da ya ba wa Za’alab cewa: “Ni ba bawan Ubangijin da bana gani ba ne” sai kuma ya kara bayani game da siffofin Allah yana cewa: “Kaiton ka ai idanduna ba sa ganin Sa da hallarar maganai sai dai zukata ne ke ganin Sa da hakikanin Imani, Kaitonka ya Za’alab, lalle Ubangijina ba a siffanta Shi da nisa, ba a siffanta Shi da motsi ko lambo, ko tsayuwa, tsayuwa ta mikewa kyam, ba kuma a siffanta Shi da zuwa ko kuma tafiya, mai Taushin Tausasawa ba a siffanta Shi da babba ,mafi girman masu girma wanda ba a siffanta Shi da girma mafi daukakar masu daukaka wanda ba a siffanta shi da gallazawa, Mai jin kai da rahama ba a siffantashi da rauni mumini ba wai da ibada ba, mai riska amma ba da jiki ba, mai magana amma ba da lafazi ba, Yana tare da abubuwa amma bada gauraita ba, Yana kuma rabe da su amma ba wai da sabani ba, yana sama da kome ba a ce wani abu na sama da shi, yana gaban  kome a a ce yana da gaba, yana cikin kome ba wai kamar yadda wani abu ke wajen wani abu ba.”

Littafin At-Tauhid na Saduk Shafi na 304 Babin Hadisin Za’alab da kuma Amali Saduk Shafi na 280 Al-Majlisul Khamis Wal Khamsun, da Biharul Anwar Fuzu’i Na” 4. Shafi na 27.

[2]- Kamar Yadda Karamiyawa ke fada cewa yana sama.

[3]- Asha’irawa sun hukunta cewa Allah zai nuna kansa ga bayinSa. A duba littafin Al-Ibana, fi Usulid Din na Al- Hasanul Ash’ari Juzu’i na 5 da na 6 da Almilal wan Nihal Juzu’i na 1 shafi na 85-94, da kuma Hashiyyar kastali da aka buga a Hamish sharhin Al-Aka’id na Taftazani sahafi na 70 da kuma Allawani’u Ilahiya Shafi na 82-98l

Al-Bagadadi ya kara da cewa: “Ahlussunna sun hadu a kan cewa ranar Alkiyama Muminai za su ga Allah kuma suka ce ya halatta a gan shi ko ta halin kaka ta hanyar hankali, amma wajabcin ganin sa ga muminai ranar Alkiyama ya z0 ne a hadisasi Littafin Al fark bainal Firak shafi na 335-336.

In banda Jama’ar da ake kira Mujassama daga cikin, Ahlussunna, wadanda suka yi imanin cewa dukan wadanda za su tashi ranar Kiyama za su gan Shi tamakar yadda ake ganin rana da wata ba tare da giragizai a tsakaninsu-Abinda ake da sabani a kai baki daya shi ne ganin Allah Ta’ala, shi zai yiwu ne tare da tsarkake Shi? Ko kuwa sam ba zai yiwu ba ne sam, tare kuma da tsarkake shi? Su Asha’irawa su nyi Imani da na farko (yiwuwar ganinsa) mu kuma Shi’a mun yi imani da na biyu (rashin yiwuwar ganin sa) muna masu bin maganar Imamanmu (A.S.) na Ahlul Bait.

A duba Littafin: Kitab Haular Ru’uya na Imam Sharafuddin ya warwane wannan al’amari yadda ya kamata ta hanya mai karfi.

Wannan kuma duk kari ne a kan abinda ya zo na cewa Allah Ya halitta Annabi Adam (A.S.) a kan kama irin tasa,  kuma cewa yana da gabobi bayyanannu kamar su yatsu da makyangyama, da kasfa da kuma cewa akwai wata alama a makyangyamarSa da za a gane shi da ita, da kuma cewa zai sanya kafarSa a cikin wutar Jahannama ranar Alkiyama har sai ta ce kad-kad,. Da kuma Manzon Allah (S.A.W.A) zai ga Allah sai ya fadi ya yi sujada. Da kuma cewa Allah zai sauko ranar Kiyama zuwa gurin bayinSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu. Da kuma cewa muminai za su ga Ubangijinsu ranar Alkiyama kuma ba za su matsatsu ba wajen ganinsa. Da dai irinsu irinsu da yawa. A duba sahih Bukhari Juzu’i na 8 shafi na 62, da Juzu’i na 9 shafi na 156. Da kuma sahih Muslim Juza’i na 4 shafi na 2, 83, da Ibin Majah Juzu’i na 1 shafi na 64, da Musnad Ahmad Juzu’i na 2 shafi na 264, da Muwadda Juzu’i na 1 shafi na 214 Hadisi na 30.

[4]- Shaikh Muzaffar (R.A.) ya ambata ta a laccarsa ta Falsafar Musulunci cewa: “A bayananmu game da Ubangiji muna bin mataki-mataki ne, muna ketare marhaloli:

1-    Marhala ta farko: a tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne.

2-    Marhala ta Biyu: Bayan tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne to lalle ne ya zamonta abin siffantawa da ainihin samuwa.

3-    Marhala ta uku: bayan mun tabbatar da marhalolin biyu sai mu zarce zuwa kadaitakarSa, domin idan har ya tabbata cewa ainihin samuwa ne to lalle ne ya zamanto shi makadaici ne domin ainihin sanuwa makadaici ne idan kuwa ba haka ba zai zama ainihin samuwa ba.

 Sa’an nan kuma sai ya ambato daliian malamai magabata wajen tabbatar da samuwar Allah a takae kamar haka: “Duniya daya ce don haka mahaliccinta ma lalle ne ya zamnto daya. Akwai dangantaka tsakanin kasancewar mahalicci daya abin halittar ma daya wato duniya ta yadda idan da an kaddara cewa an samu duniyoyi biyu o da iyayen gijinsu ma sun kasance biyu shi ne fadinsa cewa: Makadaici ba ya samarwa illa makadaici.

Sa’an nan sai ya yi ishara ga hudubar Imam Ali (A.S.) game da tauhidi da ke cewa “cikar tauhidi shi ne tsarkake aiki gare Shi.” Gajeruwar fahinta game da tsarkakewa shi ne tsarkakewa gare Shi a ayyukan ibada, sai dai kuma wannan ba zai dace da abin da ya gabace shi da kuma wanda ya biyo baya ba a maganar.

Tsarkakewa gare Shi na nufin tsarkake Shi daga dukan nakasa, da kuma dukan abinda zai soke cewa Shi Wajibin samamme ne, wato tsarkakewa ta fi da’irar tsarkake aikin ibada girma. Don haka tawhidi ko kuma kadaita Allah ba ya zamantowa na hakika har sai ya zamanto ka kadaita Shi ta kowace jiha, a zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da kuma bautarsa, tsarkakewa gare Shi na nufin kadaita Shi ta kowace fuska, da kuma tsarkake shi daga abokin tarayya ta kowane bangare...”

A duba littafin Falsafatul Islamiyya; laccocin Shaikh Muzaffar (R.A.) da ya yiwa daliban kwalejin Fikihu a garin Najaf mai Alfarma, darasi na goma Shafi 91, da kuma darasi na goma sha daya shafi na 93, da darasi na goma sha hudu shafi na 103.

[5]- A nan marubucin yana ishara ne ga irin batutuwan rikitarwar da wasu masu husuma da Shi’a suka tayar kan cewa ziyartar kaburbura haramun ne kuma suka yi ta yayatawa. Suka dogara da wani hadisi da Nisa’i ya ruwaito a cikin littafinsa sunan Nisa’i wanda lafazinsa ya zo kamar haka:

“Allah Ya la’anci masu ziyartar kaburbura da kuma wadanda suka rike masallatai da kuma gurin kunna fitila.” Juzu’i na 4 shafi na 95. Littafin Kanzul Ummal ma ya Kawo shi da lafazi iri daya, Juzu’i na 16 shafi na 388 hadisi na 45039, Ibin Majah shi ma ya kawo shi da lafazi sababin wannan da ke cewa: “Manzon Allah (S.A.W.A.) ya La’ani masu ziyartar kaburbura” Juzu’i na 1 shafi na 502 Babu Ma Ja’a fin Nahyi an Ziyakatun Nisa’il Kubura hadisi na 1574 da 1576. A sarari yake cewa a hadisan biyu akwai sabanin lafazi da kuma rikitarwa lafazin masu ziyarta mata ya bambanta daga lafazin masu yawan ziyarta da ke nufin matukar ziyarta ta kali. Kamar kuma yadda akwai rashin karin da yake Nisa’i ya ambata, bugu da kari kuma Muhammad Nasiruddin Al- Albani ya ambata wannan hadisin a cikin jerin raunanan hadisai “Silsilatul Ahadisid Dha’ifa Juzu’i na 1 shafi na 258 hadisi na 225 da kuma Ibin Uday a littafi Al- Kamil Fid Dhu’afa Juzu’i na 5 shafi na 1698 ba tare da ya ambata karin da ke akwai a cikin sunani Nisa’i ba.

Wannan dangane da matanin hadisin ke nan, amma abinda ya shafi Isnadi wato hanyar ruwaito hadisin. A cikin Isnadin wannan hadisin akwai Abdul Waris bin Sa’id Abu Salih a ruwayar Nisa’i da kuma ruwayar Ibin Majah na farko da kuma Abdullah bin Usman da kuma Abdurrahman bin Bahman a ruwayar Ibin Majah ta biyu, su wadanan maruwaita kuwa za a iya fahintar al’amarinsu kamar haka:

Abdulwaris bin, Sa’id Ibin Haban ya ce shi dan Kadariyyane. Assaji ya ce: Dan Kadariyya ne da ake zargi saboda bidi’arsa. Ibin Mu’in ma ya ce: Ya yi imani da kadariyya kuma yana bayyana haka. An ambata wannan ne a cikin littafin Tahzibit Tahzib Juzu’i na 6 shafi na 391-392.

1-    Abu Salih: Shi ana taraddudi a kansa tsakanin kasancewarsa shi ne Mizan Al- Basari ko kuwa shi Bazam Mawla Ummi Hani. Wanda mafi yawanci malaman sanin maruwaita suka fi ba da karfi a kai shi ne cewa shi Bazam ne. Bazam kuwa Ibin Hijir ya fada a cikin Tahzibit Tahzib a Juzuz’i na 1 shafi na 364 da 365 cewa game da shi Ahmad ya ce: Ibin Mahdi ya bar hadisinsa, Abu Hatim kuma ya ce: Ana rubuta hadisinsa amma ba a kafa hujja da shi. Nisa’i kuma ya ce: Shi ba amintacce ba ne. Ibin Udayyi ya ce: Ban san wani mutum daya daga cikin magabata da ya yarda da shi ba. Zakariyya bin Abi Za’ida kuma ya ce: Sha’abi ya kasance yana wucewa ta gurin Abi Salih ya kama kunnensa ya ja ya ce: kaitonka kana fassara Alkur’ani alhali kai ba ka kiyaye Alkur’ani ba,Ibin Madini kuma daga Kaddani daga sauri ya ce: Kalbi ya ce Abu Salih ya ce mini duk hadisin da na fada karya ne. An kuma kawo daga Jawzi daga Azdi cewa ya ce: Makaryaci ne. Wannan abinda Tahzibut Tahzib ya ambata ke nan kawai. Amma a littafin Silsilatul Ahadisud Dha’ifa “Silsilar Raunanan Hadisai” bayan an ambato hadisin an kuma ba da karfin cewa Abu Salih din shi ne Bazam sai ya ce: “Abu Salih din nan shi ne Mawla Ummi Hani Bint Abi Dalib Kuma sunansa Bazan ne ana kuma ce masa Bazam. Shi rarrauna ne a gurin kowa da kowa, kuma mai yawan suka ne babu wani da amince shi sai dai Ajali shi kadai. Hatta Isma’il Bin Abi Khalid Azdi ma cewa ya yi makar yaci ne wasunsu kuma sun siffata shi da gurbatarwa. Hafiz ya ce a cikin At-Takrib mai rauni ne mai cudanya hadisi. Shi rarrauna ne a gurin Ibin Mulakkan da kuma Abdul Hak Asbili. Sisilatul Ahadisud Dha’ifa Juzu’i na 5 shafi na 275-276.

2-    Abdullahi Bin Usman: Nisa’i ya ce: Amintacce ne: Wani lokaci kuma ya ce: ba kakkarfa ba ne. Ibin Haban kuma ya ce: ya kasance yana yin kuskure. Abdullah bin Dauraki kuma daga Ibin Mu’in ya ce: Hadisansa ba su da karfi. Ibin Khasim kuma ya ce: Ba mai karfi ba ne. Aliya Binul Madini kuma ya ce: Ibin Khsim ya ce: Ane kiya masa hadisi. Ya ambata haka ne a cikin littafin Tahzibit Tahzib, Juzu’i na 5 shafi na 275-276.

4- Abdurrahman Bin Bahman: Wannan kuwa game da shi Ibin Madini cewa ya yi: Ba mu san shi ba, kamar yadda ya zo a Tahzibit Tahzib, Juzu’i na 6 shafi na 135.

Wannan shi ne al’amarin sanadin, ko tafarkin wannan hadisi da kuma nassinsa, karin kuma a kan wannan shi ne cewa yana da sabani da hadisai da dama da suka fi shi kyawun matani da karfin isnadi. Ya zo a cikin hadisan da ake kwadaitar da ziyartar kabarin Annabi (S.A.W.A.) wadanda da yawa daga cikinsu a Kanzul Ummal suke: Juzu’i na 15 shafi na 651 Hadisi na 42582 da 42584. Kazalika ya zo a Juzu’i na 5 shafi na 135 hadisi na 12368 da 12373 kamar kuma yadda ya zo a sunanul kubra na Baihaki Juzu’i na 5 shafi na 249 Babin ziyaratul Kuburil Lati fi Baki’i Farkad, da kuma Babu Ziyaratil Kuburus Shuhada. Kamar kuma yadda ya zo a Sunani Ibin Majah Juzu’i na 1 shafi na 500 Babu Ma Ja’a Fi Ziyaratul Kubur da dai sauran littafa da dama wadanda wannan gurin ya yi kadan ya kidaye su.

Idan ma da a ce mun sallama mun sallama mun yarda da ingancin wancan hadisin da ya gabata, duk da karonsa da kuma sabawarsa da ya yi da dukan wadannan hadisan ingantattu, ai wadannan hadisan ana iya daukaru a matsayin shafaffu idan muka lura da maganar manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: “Na kasance na hana ku ziyartar kaburbura, to ku ziyarce su, domin suna tunatar da ku game da Lahira” Kanzul Ummal Juzu’i na 15 shafi na 646 Hadisi na 42555...

Wannan kuma duk da cewa musulmi baki daya sun yi ittifakin cewa ziyartar kabari abu ne da yake halattacce. Mun ma karfafa cewa mustahabi ne tare kuma da kasancewar al’ada a kan haka tun zamanin Annabi (S.A.W.A.).

Baihaki ya kawo a cikin littafinsa sunanul kubra da waninsa cewa duk wani dare da Manzon Allah (S.A.W.A.) ya kasance a Dakin A’isha yakan fita a karshen dare zuwa makabartar Baki yana cewa: “Aminci ya tabbata gare ku gidajen mutane muminai, kuma abinda ake muku alkawari ya zo gare ku.” Ya ambata wannan a Juzu’i na 5 shafi na 249. Nisa’i ma ya ambata a littafinsa Sunan a kitabul Jana’iz, Babu Ziyaratu Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa Sunan a sashen Ziyaratul Kubur Hadisi na 3234 da kuma Ibin Majaha littafinsa sunan a Babin Ziyartar kaburburan Mushirikai cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin Mahaifiyarsa har ya yi kuka sa’an wadanda ke kewaye da shi ma suka yi kuka. Tare kuma da kari a kan cewa akwai hadisai da dama da aka ambata wadanda ke nuna cewa Annabi (S.A.W.A.) ya kasance yana koya wa A’isha yadda ake addu’a idan an ziyarci kabari.

Idan ma har muka kyale duk wadannan muka koma ga hadisin da suka dogara da shi muka ya nazarin sa tare da kawar da kai daga dukan abubuwan da muka ambata to sam ba za mu sami wata ishara a cikinsa manyan malaman hadisi da malaman fikihu sun hukunta makaruhancin Ziyartar kaburbura ne ga mata kawai.Ga nassin abinda Baihaki ya kawo a littafinsa Sunanul Kubra Juzu’i na 4 shafi na 78. Ya ce: “Lalle Fatima Yar Annabi (S.A.W.A.) ta kasance tana ziyartar kabarin kawunta Hamza kowace Juma’a tana yin salla tana kuma kuka a gurin... Sa’an nan kuma sai ya ce; kuma mun riga mun ruwaito a hadisi tabbatacce daga Anas bin Malik cewa Manzon Allah (S.A..W.A.) ya wuce wata mata tana kuka a gurin wani kabari tana kuka sai ya ce; “ Ki ji tsoron Allah ki yi hakuri” kuma a wannan hadisin babu cewa ya hana ta zuwa Makabarta, sai dai kuma a cikin wannan akwai karfi a kan abinda muka ruwaito daga A’isha sai dai kuma mafi ingancin abinda aka ruwaito a kan hakan hadisa bayyanan, shi ne hadisin Ummu Atiyya da kuma hadisan da suka yi daidai da shi, cewa; idan da su tsarkaka daga rakiyar gawawwaki zuwa makabarta da kuma fita zuwa makabarta da ziyartar kaburbura to da haka ya fi musu dacewa”.  A nan maganarsa ta kare.

Hadisin Ummu Atiyya kuwa shi ne “ Ta ce an hane mu rakiyar gawawwak zuwa makabarta: Kuma bai wani nauyay a kanmu ba.” Sunanul Kubra Juzu’i na 4 shafi na 77 kuma ya ce Muslim ma ya ruwaito shi a cikin sahihi Muslim ta fuskoki biyu daga Hisham. Da kuma sunanu Ibin Majah Juzu’i na 1 shafi na 502 hadisi na 1577.

Idan ana bukatar Karin bayani sai a duba littafin ‘Kashful Irtiyab fi Atba’i Muhammad bin Abdulwahab wanda Sayyid Muhsin Al- Amin Al- Amuli ya rubuta.

[6]- Alal misali za mu ambata misali daga sunna da kuma tarihin rayuwar Annabi (S.A.W.A.) da kuma na Zuriyarsa dangane da fifita wadannan irin kyawawan ayyuka. Akwai misalin abinda Bukhari ya ruwaito a Sahihul Bukhari a Babin Fadha’ilil Sahaban Nabi juzu’i na 4 shafi na 204 daga Annabi (S.A.W.A.) “Masu kuka su yi kuka ga Mutum kamar Ja’afar.” Kazalika Annabi (S.A.W.A.) ya sunnata kuka ga Hamza ya ce:  “Masu kuka su yi kuka ga mutum kamar Hamza”. A duba littafin Tabakat na Ibin Sa’ad Juzu’i na 2 shafi na 44 da kuma littafin Magazi na Wakidi Juzu’i na 1 shafi na 317, da Musnad Ahmad Juzu’i na 2 shafi na 40. Nisa’i ma ya ambata shi a cikin littafinsa Sunan a kitabul Jana’iz Babu Ziyarati Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa sunan a Ziyaratul Kubur hadisi na 3234 da kuma Ibin Majah a littafin Sunan a Babu Ma ja’a fi Ziyarati Kuburil mushrikin: Cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa ya yi kuka ya sa wadanda ke tare da shi suka yi kuka.

Kazalika kukan Fatimatuz Zahra (A.S.) ga mahaifinta ,kukah Zainab ‘Yar Amirul Muminin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) ga yayunta Hasan da Husaini (A.S.) Imam Sadik  (A.S.) ya ce: Imam Husain (A.S.) ya ce: Ni wanda aka kashe ne don in zama darasi, babu muminin da zai tuna ni face ya yi kuka.” [Littafin Kamiluz Ziyarat shafi na 108] Har ila yau kuma ya kara da cewa: Nisawar bakin ciki saboda mu tasbihina, himmar yinsa saboda mu kuma ibada ne, boye asirinmu kuma jihadi ne a tafarkin Allah” Biharul Anwar juzu’i na 44 shafi na 278 hadisi na 4.

Imam Ridha (A.S.) kuma ya ce: `Duk wanda ya tuna masifar da ta same mu ya yi kuka kuma ya sa aka yi kuka idonsa ba zai yi kuka ba ranar da idanduna suke kuka, wanda kuma ya zauna a gurin zaman da ake raya al’amarinmu “zuciyarsa ba za ta mutu ba ranar da zukata ke mutuwa. Littafin Amali Saduk Majilisi na 17.

[7]- Shaikh Muzaffar na ishara da wannan da fadinsa cewa: “Amma fadin cewa daukar abu a kaddare wanda ke nufin cewa siffofi ba su da ayyananniyar ma’ana ta zahiri a sarari, mu mun dauki wannan batun da cewa ba sahihi ba ne, domin Allah Ta’ala Ya siffanta kanSa da cewa  Shi masani ne, mai Hikima, Mai kudura. Shi ne tsantsan kudura, da ilimi da rayuwa, domin Shi zatine wanda ke da kudura da ilimi da rayuwa, domin shi zati wanda ke da kudura da ilimi da rayuwa, sai wadannan siffofin sun sha bamban da ma’anar da ake fahinta ga hankali, domin laffuza ba ma’ana guda suke da ita ba, sassabawarsu a ba da surar ma’ana ne kawai, ba sa sassabawa a siffofi a samuwa, da kuma kasancewa a samuwa, kuma babu adadi a daukar ma’ana kamar yadda suka ambata sai dai akwai adadin maafofi da ke hakaito wannan hakika, wannan kuwa ita ce hakika baki dayanta. Amirul Muminin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) ya ce: “Duk wanda ya siffanta Shi to ya sanya Shi, adadi...” Ashe ba ya siffanta shi da siffofi da dama ba ne? Abinda yake nufi Shi ne wanda ya siffanta Shi da siffofi kari a kan zatin ta yadda zai zamanto zati adadi-adadi da kuma adadin masu wanzuwa da dama har ya zamanto ya fita daga kasance wajibin samamme.” Laccocin marubucin Al- Falsafatul Islamiyya. Shafi na 102.

[8]- A maganar marubucin akwai ishara ga ra’ayin da shaikh Saduk ya tafi a kai na cewa: “Duk yayin da muka siffanta Allah Ta’ala daga siffofin zatinSa to muna nufin kore kishiyoyinsu ne kawai daga gare Shi Ta’ala. Muna cewa: Allah Ta’ala bai gushe ba yana Mai ji, Mai gani, Masani, Mai Hikima, Mai kudura, Madaukaki, Rayayye, Tabbatacce, Makadaici, Wanzazze, wadannan kuma siffofin zatinSa ne.

Mu ba ma cewa: Shi Azza Wa Jalla bai gushe ba yana mai yawan halitta, mai Aikatawa, mai so, mai Nufi, Mai Yarda, Mai ki, Mai Arzutawa, Mai yawan kyauta, Mai magana, domin wadannan siffofin ayyukanSa ne, su kuma fararru ne bai halatta ba a ce: Allah Ta’ala bai gushe ba ana siffanta shi da su”. Littafin Al- l’itikadat shafi na 8.

Ba boyayye ba ne cewa za a iya danganta koruwa da dama ga al’amari guda, domin ma’anar Rayuwa ita ce rashin mutuwa, ma’anar ilimi kuwa shi ne rashin Jahilci, ma’anar kudura kuwa koruwa gazawa.... haka nan, wadannan korewar dabam-dabam zai yiwu a danganta ga zati makadaici wato ma’ana dai, Allah Ta’ala wanda ya daukaka ga haka, shi tarin korarru dabam-dabam ne, sa’an nan sai kuma shaikh Muzaffar ya biyar da batun cewa: “Mu muna girmama shaikh Saduk, a matsayin mai hadisi, mai ruwaitowa, amma idan ya fadi irin wadannan maganganu to ba za mu karbi ra’ayoyinsa ba. Mu muna nufin mu ce ne Hakika ba ta yawaita, ta fuskar kasancewa ne ko kuma ta adadi kawai a manufa domin yawa ko adadi ta fuskar kasantuwa ko kuma manufa ba shi da wata ma’ana. Ra’ayin da muka yi imani da shi shi ne abinda Farabi ya ce fadi da cewa:

“Shi Masanine ta inda Yake Mai kudura ta yadda yake rayayye, rayayye kuma ta yadda yake masani... Wadannan siffofin babu yawan adadi tare da su a Hakika ne ko kuma ta fuskar manufa.

Domin fuskar sani ba daban take da fuskar rayuwa ba. Don haka kasancewarsu adadi a fahinta ne kawai abin nufi ne kawai. Kuma ba ma nufin cewa fahintar abin nufi tana nufin ma’ana wanda take fassara hakika, wadda yawanta shi ne kadaitakarta. Mu abinda muke fada shi ne cewa: “Shi masani ne ta yadda yake mai kudura, wadannan kuwa manufofi ne na hakika amma ba wai don cewa suna da samuwarsu ta kai tsaye su ya su ba. Sai dai ma’anar cewa samuwa kanta ita ce ilimin, ita ce kudurar ba wai kudurar kanta samammiya ba ce wadda da wannan samuwar ne, wadda manufarta za ta zama daura da waccan manufar. Saboda haka wadannan siffofin koda yake dai tabbatattune da gaske amma a halin kasancewarsu masu yawa ne har ila yau kuma su kadaitaka ne kuma adadin manufofinsu yana bayyana ma’ana ta hakika ne amma dai babu yawaitaka ta fuskar ma’ana. Wannan shi ne kolin al’amari a wannan batu kuma shi ne abinda ya shiga duhu ga tunanin masu maganganun da uka gabata. A duba littafin falsafatul Islamiyya na shaikh Muzaffar shafi na 101 zuwa shafi na 102. A kuma duba littafin Tashihul I’itikad na Shaikhul Mufid shafi na 41 da kuma littafin Matarihun Nazar fi sharhil Babil Hadi Ashar na shaikh Safiyuddin Turaihi fasali na 3 Shafi na 131-162.

[9]- Marubucin ya yi karin bayani a kan wannan al’amari kamar haka:-

One- Cewa siffofi kari ne a kan zati, kuma su ma wajiban samammu ne to wannan maganar Ash’ari yawa ce.

Two- Maganar karramiyawa kuwa ita ce cewa siffofi kari ne a kan zati sai dai kuma ba lazimai ba ne ga zatin saboda kasancewarsu lazimai zai wajabta kasancewarsu wajiban samammu ya zamanto an samu wajibai dama.

[10]- Nahjul Balagha: Huduba ta 1, maganar Amirul Muminin game da fara halitta sama da kasa da kuma Al- Ihtijaj juzu’i na 2 shafi na 473 hadisi na 113.

[11]- Adalci shi ne sakamako a kan aiki gwar-gwadon abinda aka cancanta a kansa, zalunci kuwa shi ne hana hakkoki. Allah Ta’ala kuwa Adali, karimi, mai yawan alheri, mai bayar da alheri don zabinsa, mai Jin kai, Ya riga Ya ba da tabbacin yin sakamako a kan ayyuka da kuma musanya al’amari ga wanda ya fara alheri ya wahala Ya kuma yi alkawarin ba da kari daga gare shi. Allah Ta’ala Ya ce: “Wadanda suka kyautata suna da kyakkyawa da kuma kari.” Surar Yunus a ya ta 26. Wato Ya ba da labarin cewa masu kyautata aiki to yana da kwatankwacinsa goma” wato yana da kwatankwacin abinda ya cancanta a kan haka har rubi goma. “Kuma wanda ya zo da mummuna ba za a sakamta masa ba sai dai gwargwadonsa kuma su ba za a zalunce su ba.” Surar An’ami aya ta 160. Wato ma’ana ba za a yi masa sakayya sama da abinda ya cancata ba. Sa’an nan kumaya ba da tabbacin yafewa kuma ya yi alkcawarin gafartawa. Allah Ta’ala ya ce: “Kuma lalle Ubangijinka tabbas ma’abucin ga mutane a kan zaluncinsu ne.” Surar Ra’ad aya ta 6. gafatawa Kuma yana cewa: “Allah ba ya gafarta cewa a yi shirka da shi amma Yana gafarta abinda ba wannan ba ga wanda Ya so” Surar Nisa’i aya ta 48.

Kuma Allah Ta’ala Ya yi umarni da a yi adalci kuma Ya hana yin zalunci. Allah Ta’ala Yana cewa: “Lalle Allah Yana umarni da adalci da kuma kyautatawa.” Surar Nahl ayata 90.

Da kuma Tashihul I’itikad na Shaikh Mufid shafi na 103.

[12]- Mazhabar Ja’afariyya wato Shi’a Isna Ashariyya ta dauki adalci a matsayin Jigo daga cikin ginshikan addini sai dai kuma alal hakika shi ba ginshiki ne guda shi kadai mai zaman kansa ba sai dai shi yana kunshe ne a cikin siffofin Allah Ta’ala kuma wajabcin samunsa ya lizimta tattara siffofin kyawu da kamala saboda haka shi dai adalci yana daga cikin al’amuran tauhidi ne. Sai dai kuma su Asha’irawa da suka saba wa Adaliyyawa, wato Mu’utazilawa da kuma ‘yan Ja’afariyya, Shi’a Isna Ashariyya sai suka musa abu mai kyau da kuma mummuna wadanda hankali ya tabbatar da su. Suka ce babu wani abu mai kyau sai wanda shari’a ta ce mai kyau ne, babu mummuna kuma a sai wanda shari’a ta ce mummuna ne kuma cewa idan da Allah zai dawwamar da mai biyayya a gidan wuta mai sabo kuma a gidan aljanna to wannan ba mummuna ba ne saboda yana jujjuya al’amura ne da ke karkashin mulkinSa kum kamar yadda Alkur’ani ya ce: “Ba a tambayarSa a kan abinda ya aikata su kuwa ana tambayar su” Surar Anbiya’i aya ta 23. Su kuwa Adaliyyawa kuwa cewa suka yi: Mai yanke hukunci a wannan al’amari shi ne hankali shi kadai dinsa, babu abinda zai shigar da shari’a a cikinsa sai dai karin ta’akidi da kuma shiryarwa. Shi kuma hankali ya kebantu da hukunta kyawun wasu ayyuka da hukanta munin wasu kuma yana hukunta cewa danganta mummunan abu ga Allah abu ne da ba shi da kyau kuma ba zai yiwu ba Allah Ya aikata shi domin shi mai hikimane azabtar da mai biyayya kuwa zalunci ne, zalunci kuwa mummunan abu ne kuma ba zai taba faruwa daga Allah Ta’ala ba.

Da haka ne suka tabbatar da siffar Adalci ga Allah suka kebance ta da ambato banda sauran siffofin don ishara ga sabani da Asha’ira. Su kuwa Adaliyawa ta hanyar ka’idar kyakkyawa da mummuna kamar yadda suke a hankali sun tabbatar da wasu ka’idoji daga ka’idojin ilimin sanin Allah: Kamar su ka’idar Tausasawa, da kuma Wajabcin godiya ga wanda ya yi alheri da wata ni’ima, da kuma wajabcin bincike da nazari a mu’ujiza, kuma a kan wadannan ka’idojin suka gina al’amari tilasta wa da kuma ‘yancin zabi da ke daga cikin mafi wahalar matsaloli.

Domin karin bayani a duba: Aslus Shi’a wa kuma Matarihun Nazar na shaikh Turaihi Fasali na 4 shafi na 164.

[13]- Da dai sauran wadannan da Asha’irawa suka tafi a kai na daga maganganunsu na cewa Allah Ta’ala Ya aikata mummuna da maimaitawarSa na nau’o’in zalunci da shirka da dagawa da ketare haddi da kiyayya da yarda da su ya kuma so su -Allah Ta’ala Ya daukako ga haka, Tsarki ya tabbata gare Shi, domin kara samun filla-fillan wadannan munanan ra’ayoyi’a duba littafi Nahjul Hak na Allama Hilli shafi na 85, da kuma sharhin Aka’ida da kuma Hashiyar na kistal, shafi na 109-113, da Milal wan Nahal Juzu’i 1 shafi na 85, 91 da kuma Al- Faslu da na Ibin Hazm Juzu’i na 3 shafi na 66 da 69 da kuma sharhit Tajrid na Kurshaji shafi na 373.

[14]- Lalle ne a san cewa abinda ake nufi da kallafa aiki shi ne cewa ya kallafa aiki ya bukaci wanda ya kallafawa din da ya aikata wani abu mai wahala mai tsanani. Wato ke nan abin dubawa da komawa gare shi a nan shi ne bukata saboda yadda ya zo a cikin fassara ko bayyana ma’ana da kuma fassarar kallafa aikida cewa shi ne bukatar aiki mai tsanani da wahala daga wanda aka kallafawa. Kazalika Sayyid Sharif Murtadha Alamul Huda ya biyar da magana yana mai gyara batun da cewa: Kallafa aiki ba ya ingata sai bayan kamalar hankali da tabbatar da dalilai:

“Kuma Shi Allah Ta’ala mafi kammala hankula kuma ya kuma cika sauran sharuda don babu makawa Ya ba da taklif wannan yana ishara da cewa takalifi ba shi ne sanarwa ba.” Malamanmu sun yi bayanai masu yawa game da kallafa aiki tare da ambata fuskoki dabam-daban na abinda ake nufi da takalifi da kuma alakarsa da shi mukallaf\ wanda aka kallafawa aikin da kuma aikin da aka kallafa masa da siffofi shi wanda aka kallafa wa aikin da kuma manufar shi kansa aikin da kuma yadda za a yi a aiwatar da shi da kuma irin ayyukan da za a yi ya zama an aiwatar da wannan takalifin, da wanda ya kallafa masa wannan aikin, da kuma abubuwan da ya kebanta da su domin ya zamanto ya kyautata aiki ko kuma wadanne abubuwa ne wajiban wannan aikin. Sananne ne cewa wannan bangare yana daga cikin bayanan Irada wadanda suka cancanci himmatuwa ta musamman daga bangaren malaman Akida tare kuma da kebe masa sashe na musamman a sakamakon babban sabanin da ke akwai a kansa a tsakanin malamai da shugabannin mazhaba game da nufin Allah da aka ambata a ayoyin Alkur’ani da kuma alakarsa da al’amuran da Allah bai yarda da su ba da kuma tawilinsu da fuskokin da ba za su rasa matsa wa kai ba ,mafi muhimmanci daga cikinsu kamar aya ta 148 daga surar An’am da ke cewa: “Wadanda suka yi shirka za su ce idan da Allah Ya so da ba mu yi shirka ba, kuma da iyayenmu (ma ba su yi ba) kuma da ba muharamta daga wani abu ba, haka nan wadanda suka kasance kafin su suka yi karya har suka dandani azabarmu, ka ce shin kuna da wani abu na daga ilimi da za ku fito mana da shi? Babu abinda kuke bi face zato ku ba kome ba ne illa kuna dirkaniya kawai.” Da kuma aya ta 20 daga surar Zukhruf: “Kuma suka ce idan da mai Rahama Ya so da ba mu bauta musu ba, ba su da wanidalili game da wannan ba sa kome sai dai dirkaniya.”

Da dai ayoyi da dama da ake wahimtar cewa su shafi Iradar mahalicci ne game da abinda halittu ke aikatawa mummuna. Allah Ta’ala Ya daukaka ga yin haka, daukaka mai girma. Daga nan na shaikh Muzaffar (R.A.) ya ware sashe guda shi kadai domin ya rubuta abinda ya dace a cikinsa game da abinda ya kebantu da matsayin Shi’a Imamiya. Domin Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) tana da matsayinta bayyananne wanda ke yin ta’akidi a kan tsarkake Ubangiji da kuma raba Shi da duk wani mummunan abu ko kuma mai kama da mummuna tare da matukar kore cewa Allah Ta’ala ne Ya nufi a yi shirka ko zalunci ko Alfasha, ballantana ma aikata shi, ko kuma halatta aikata shi ko umarni da shi domin dukan wannan zai kai ga saba wa hikimarSa da adalcinSa da falalarSa.

Abinda shaikh Mufid (R.A.) ya ambata shi ne sakamako ko kuma amfanin wannan magana inda yake cewa: Allah Ta’ala ba Ya nufin  a aikata sai kyakkyawa daga ayyuka, kuma ba ya so sai kyakkyawa daga ayyuka kuma ba ya son munanan ayyuka, ba Ya nufa a aikata alfasha, Allah Ya daukaka daukaka mai girma daga abinda mabarmata suke fada Allah yana cewa: “Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi.” Surar Mumin: 31

“Allah yana nufin sauki gare ku ba Ya nufin tsanani gare ko.” Surar Bakara: 185

“Allah Yana nufin Ya yi muku bayani kuma Ya shiryar da ku tafarkin wadanda suka gabace ku.” Surar Nisa’i: 26.

“Allah Yana nufin Ya yafe ku wadanda suke bin sha’auce-sha’auce kuwa suna nufin ku fandare fandarewa mai girma.” Surar Nisa’i: 27.

Allah Ta’ala Ya ce: “Allah Yana nufin Ya saukaka muku kuma shi mutum an halitta shi rarrauna ne.” Surar Nisa’i 28.

Allah Ta’ala Ya bayyana cewa ba Ya nufin tsanani ga bayinSa Yana nufin sauki ne gare su, kuma cewa Yana nufin bayani gare su, ba Ua nufin bata gare su, kuma Yana nufin saukakawa gare su ba ya nufin nauyayawa. Kuma idan har da Allah Ya kasance Shi ne mai nufar su da sabo to ai da wannan ya sabawa nufinSa na yin bayani gare su da saukakewa gare su. Littafin Allah shaida ne a kan sabanin abinda batattu masu kaga karya ga Allah suka tafi a kai. Allah Ya daukaka daga abinda azzalumai, suke fada| daukaka mai girma.

A duba littafin Azzakhira na Sayyid Murtadha Mufid Juza’i na 5 shafi na 48-51.

[15]- Abinda ke nuna haka shi ne fadin Allah Ta’ala cewa: “To ku tambayi ma’abuta sani idan har kun kasance ba ku sani ba.” Surar Nahli: 31.

Da kuma fadin Allah Ta’ala da ke cewa: “Don me wata jama’a daga cikinku ba za ta fita domin su nemi ilimi don su fahinci addini kuma su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su ko sa yi taka tsatsan ba.” Surar Tauba aya ta 122.

Kazalika maganar Imam Sadik (A.S.) na yin ishara da haka yayin da aka tambaye shi dangane da maganar Allah Ta’ala da cewa “ka ce: To Allah na da cikakkiyar hujja a kanku” Sai Imam (A.S.) ya ce: “Ranar Alkiyama Allah zai ce wa bawa, bawaNa shin ka kasance masani? Idan ya ce “E” sai Ya ce masa: Shin ka yi aiki da abinda ka sani. Idan kuwa ya ce: Nina kasance Jahili| sai ya ce masa: Ashe ba ka koya ba har ka yi aiki: Sai ya ja da shi: To wannan ita ce cikakkiyar hujja.” Haka ya zo a littafi Amali shaikh Tusi shafi na 9 Juzu’i na 10/10. Kuma mai Biharul Anwar ya kawo daga gare Juzu’i na 2 shafi na 29 hadisi na 10. Da kuma hadisin da aka kawo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: “Ku lizimci neman ilimi a ddinin Allah kada ku zamanto jahilan kauye, domin wanda bai nemi ilimi addinin Allah ba, Alalh ba zai dube shi ba ranar Alkiyama kuma ba zai tsarkake masa aiki ba.” Alkafi Juzu’i na 1 shafi 24 hadisi na 7.

Kamar kuma yadda ya zo a “Risalolin” hukunce-hukuncen ibade ake aiki da su cewa: Wajibi ne akan mukallafa wato balagi ya nemi ilimin al’amuran shakku da na mantwa wadanda zai yiwa su taso masa, domin kada ya auka cikin saba wa abinda aka kallafa masa idan har bai koya ba. A duba Risalar Sayyid Sistani mai suna Minhajis Salihin Babin Ibada shafi na 13 matsala ta 19.

[16]- Daga cikinsu akwai Al- Asha’ira wadanda suke inkarin musabbabi inda suka kayyade musabbabin da cewa Allah Ta’ala ne kawai, suka ce, alal misali wuta ba za ta kona kome ba sai dai kawai ala’dar Allah Ta’ala ce ta gudana a kan cewa duk yayin da tutafi suka shafe ta za su kone ba wai don wuta ita ce mai wani shiga cikin al’amarin konawar ba. Don hakan ne suka tafi a kan cewa ayyukan mutane Allah ne Ya halitta su ba tare da wani hannun su bayin a kai ba, wato shi bawa bashi da wani tasiri a kan aikata aiki. A duba littafin Bidayatul Ma’ar’ful Ilahiyya Juzu’i na 1 shafi na 159 da shafukan da ke biye.

Ba boyayye ba ne ga duk wanda ya bibiyi littafan Mazhabar Ja’afariyya, shi’a Imamiyya, cewa suna soke akida Jabru da ke cewa duk abinda mutum ya yi Ubangiji ne Ya sa shi sun yi sabani da Asha’ira da suka yarda da hakan kamar kuma yadda har ila yau su ‘yan Mazhabar Ja’afariyya ba su yarda da sallama kome ga bawa ba shi ne mai iko a kan kome sabanin Mu’utazilawa. An ruwaito daga Imam Abil Hasan Aliyu Bin Muhammad Al-Hadi (A.S.) cewa an tambaya shi game da ayyukan mutane inda aka ce masa: Shin Allah ne Ya halitta su? Sai Ya ce: “Ai idan da Shi ne ya halitta su to da bai kore su daga gare Shiba ai Allah Ta’ala Ya ce lalle Allah ba Shi ba mushirikai haka nan ma ManzonSa.” Surar Tauba aya ta 3. Babu abinda yake nufi da rabuwar ba wai daga ainihin halittarsu ba na abin nufi shi ne shirkarsu da munanansu.”

[17]- Mufawwadha su ne wadanda suka kare tilasta mutum a kan ayyuka, yawancinsu Mu’utazilawa ne, suka ceayyuka dai an sallama su gare mu ne babu abinda ke sanya Irada da Izinin Allah Ta’ala a cikin ayyuka. Abinda ya jawo wannan mummunan ra’ayi shi ne gudun danganta sabo da kafirci ga Allah Ta’ala Al- Tafwidh shi ne kore taka tsantsan a ayyuka ga bayin Allah da kuma halitta musu aikata abinda suka so na daga ayyukan. Wannan magana ce irinta Zindikai da ma’abuta halastarwa.

[18]- Shaikh Mufid ya fadi a cikin littafin Tashihul I’itikad cewa: “Hanya matsakaiciya a tsakanin wadannan maganganun biyu wato Aljabru-tilasta aiki da kuma Tafwidh-sallama ayyuka. Ma’ana cewa Allah Ta’ala Ya kaddara wa bayinSa ayyuka daYa sa su aikata su Ya kuma sanya musu iyakoki a kan haka, Ya kuma shata musu -zane-zanen, kuma Ya hane su aikata munanan ta hanyar gargadi da tsoratarwa da narko da azabtarwa. Kuma bai kasance Yana ma tilasta su ba ta hanyar barinsu da ikon aikatawa, kuma bai sallama musu ayyuka ba saboda hana su aikata mafi yawa daga cikin su da kuma sanya musu iyaka a kansu, Ya umarce su da masu kyau Ya hana su munana, wannan shi ne bambanci tsakanin tilastwawa da kuma sallama wa musanafat Shakihul Mufid. Juzu 15.

[19]- Al-Kafi Juzu’i na 1 shafi na 160 hadisi na 13 da kuma Al-Ihtijaj Juzu’i na 2 shafi 490, da Littafin Al Tauhidi. Shafi na 362, da Al- Itikadat na shaikh Saduk: 10 da Tashihul I’itikad Musanafat na Shaikh Mufid Juzu’i na 5 shafi na 46.

[20]- An tambayi Abul Hasan Musa bin Ja’afar (A.S.) dangane da ayyukan bayin Allah\ daga wa suke? Sai ya ce: “Ayyukan bayin Allah ba sa wuce dayan uku: Ko dai su kasance daga Allah da kebe, ko kuma su kasance daga gare shita fuskar Yana da hannu a eiki ko kuma su zamanto daga bawa zalla. Idan da sun kasance daga Allah ne zalla to da Shi ne Ya fi cancantar yabo a kan Kyawawansu, da zargi kuma a kan munanansu, yabo da zargi ba zai tama zama ya ta’allaka ga kowa ba. Idan kuwa da daga Allah ne da kuma bawa to da yabo da suka ya zamanto nasa tre idan wadannan biyan sun tabbata ba daidai ba to ya tabbata ke nan ayyuka daga halittu ne idan Allah ya yi musu ukuba a kan lafifinsu da aikatawa to hakkkinsa ne ya yi haka. Idan kuwa ya yafe su shi ma’abucin takawa ne da gafara.” Tashihul I’itikad Shaikh Mufid Juzu’i na 5 shafi na 44.

[21]- A cikin littafin laccocin Falsafa shaikh Muzaffar na da wannan ra’ayin mai zurfi da ke cewa:

“Kowane daya daga cikin Mujabbira wato masu ra’ayin tilasta ayyuka ga bayin Allah, da kuma Mufawwidha, masu ra’ayin sallama ayyuka bai daya ga bayi, sun dubi kwibi daya ne kawai sun mance da dayan sai dai kuma wajibi ne mutum ya zamanto mai  ido biyu ba mai ido daya ba, duk wanda ya duba da kwibi daya to ya zama mai ido daya yana duban bayar da samuwa ta bangare har ya suranta cewa ana tilasta mutane a kan ayyuka, sa’an kuma idan ya duba kwibi dayan da mutane ke aikata ayyukansu da zabinsu sai ya suranto cewa an sallama musu ne. Amma kuma idan da kulawar Allah za ta katse mini koda na dan lokaci ne to da na gushe kuma da ayyuka na ma sun gushe ni ina linkaya ne a karkashin mulkinSa.

[22]- Kamaluddin shafi na 69.

[23]- Kamaliddin shafi na 70.

[24]- Al- Tauhid shafi na 336 Hadisi na 10, da kamaluddin shafi na 69 da kuma Tashihul I’itikada na shaikh Mufid Juzu’i na 5 shafi na 66. Shaikh Mufid ya kara bayanin hadisin da cewa: “Abinda yake nufi, Alaihis Salam, shi ne abinda ya bayyana daga Allah Ta’ala na kore kisa gare shi, masa sai ya tausasa gare shi wajen kore shi daga gare shi.

Labarin haka ya zo ga Sadik Alaihis Salam, an ruwaito daga gare shi cewa har sau biyu sai na roki Allah don ya kore masa kuma ya kore”. Abu na iya zama rubutacce da sharadi sai halin al’amarin ya canja.

[25]- Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma yayin da ya isa aiki tare da shi ya ce: Ya karamin dana ni na gani a Mafarki lalle in yanka ka. To ka duba me ka gani. Sai ya ce: “Ya Babana ka aikata abinda aka umarce ka, in Allah Ya so za ka same ni daga masu hakuri. To yayin da suka amince kuma ya kayar da shi a gefen goshinsa. Kuma Yuka kiraye shi cewa ya Ibrahim. Hakika ka gaskata mafarki kuma tamkar haka ne Muke sakamtawa masu kyautatawa. Lalle wannan tabbatacce shi ne babban bala’i bayyananne. Kuma sai Muka musanya shi da abin yank mai girma.” Surar Saffat: 102-107.

[26]- Akwai wasu jama’a daga cikin Shi’a - duk da abinda Imamus Sadik Alaihis Salam da abubuwan da ya fada dangane da rasuwar dansa da kuma shirya jana’izarsa da kai shi kabari-suna cewa Isma’il shi ne Imami bayan mahaifinsa Imam Sadik Alaihis Salam. Wadannan su ne ake kira da ‘Yan Isma’iliyya, su dabam suke da shi’a Imamiyya da fadinsu cewa “Imamanci bayan Imam Sadik Alaihis Salam ya koma ga babban dansa ne Isma’il kuma suna raya cewa Imam Sadik Alaihis Salam shi ne ya ba da nassin haka game da shi tun yana da rai. Kuma sun yi sabani game da Isma’ila. Wasu daga cikinsu suka ce ya rasu tun zamanin Mahaifinsa Imam Sadik - wannan shi ne ya tabbata a tarihi kamar yadda marubucin littafin ke ishara da shi a nan. Su wadannan su ne suke cewa Imamanci ya ci gaba a zuriyar shi Isma’ila na farkonsu kuwa shi ne Muhammad bin Isma’ilu, wasu daga cikinSu kuma suke cewa shi Isma’la bai mutu ba mahaifinsa ya bayyana rasuwarsa don takiyya, gudun kada Abbasiyawa su kashe shi har ma ya sa gwamnan Mansur a Madina Muhammad bin Sulaiman ya halacci mutuwarsa da shirya jana’izarsa da kuma kai shi kabari. Wadanda suka tsaya a kan shi Isma’ila daga cikinsu, ba su ketare shi ba, su ake kira “yan wakafiyya a zahiri suna kidaya Imamansu bakwai ne daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib Alaihissalam zuwa kan shi Isma’ila da suke ce Imami ne. Sashensu kuwa da suke ce dan Isma’il Muhammad shi ma Imami ne suna da Imami goma sha hudu, bakwai na zahiri bakwai kuma na boye, na zahirin sun fara daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib Alaihi salam zuwa kan shi Isma’il bakwai boyayyu kuwa sun fara ne daga kan Muhammad bin Isma’il sai dansa Ja’afar As-Sadik, sai dansa Muhammadul Habib, sai kuma Abdullahil Mahdi wanda ya bayyana a Arewacin Afirka daga cikin ‘ya’yan Fatima har ya kafa hukumar Fatimiyya.

A duba littafin: Firakus Shi’a shafi na 67, da kuma Al-Fusulul Mukhtara minal Uyuni wal mahasin shafi na 308, da kuma Asshi’atu Bainal A’sha’ira wal Mu’utazila shafi na 78, da Tarikhul Mazahibi Islamiyya shafi na 54, da Al- Milal Wan Nihal na Shahristani Juzu’i na 1 shafi na 149, da kuma Al- Farku Bainal Firak shafi na 62.

[27]- As- Shaikh Muhammadul Husain Kashiful Gita ya yi bayani game da haka yana cewa: “Shi Bada a duniyar halitta tamkar shafe hukunci da maye gurbinsa da wani ne a duniyar tsara shari’a. Kamar yadda shafe hukunci da maye gurbinsa akwai wasu fa’adoji da asirrai wadanda wusunsa sun fito sarari wadansu na boye kazalika a wajen boyewa da kuma bayyanawa a duniyar halitta. A bisa asasin cewa wani bangare na Bada (Bayyanawa) saboda sanar wa zukatan, ke da sadarwa da madaukakin matsayi ne, wasu abubuwa sa’an nan a kange musu sharudansu ko kuma shamakinsu. Alal Misalian nuna wa Annabi Isa (A.S.) cewa wani ango zai mutu ranar da zai shiga dakin amarya amma ba a nuna masa cewa da sharadin rashin sadaka ba ne sai aka yi gamon katar Mahaifiyarsa ta yi masa sadaka, shi kuma Annabi Isa (A.S.) ya riga ya sanar da cewa zai mutu a daren shiga dakin amarya sai ya zamanto bai mutu ba. Da aka tambaye shi game da haka sai ya ce: “Mai yiwuwa kun yi masa sadaka ne, sadaka kuwa na iya kare bala’i mummuna.” Hakaza da makamantan wannan... Idan da ba don Bada ba to da babu wata ma’ana ga sadaka da addu’a da ceto, da ma kukan Anuabawa da Waliyi da tsananin tsoronsu da taka tsantsan dinsu ga Allah alhali ba su taba saba masa ba ko da gwargwadon kiftawar ido, tsoronsu kawai saboda saninsu ne game da shamakin nan taskantacce wanda babu wani da ya gan shi.”

Littafin Aslus shi’a wa Usuliha shafi na 314.

[28]- “Ba mu bar wai abu ba daga littafi” Surar An’am aya ta 38. Kuma ya zo a hadisi “Babu wani da mutane biyu ke da sabani a kansa face yana da asalinsa a cikin littafin Allah.” Usulul Kafi Juzu’i na 1 shafi na 78 hadisi na 6. Har ila yau kuma ya zo cewa: “Babu wani abu da ke faruwa face Allah yana da hukunci a kansa.” Biharul Anwar Juzu’i na 93 shafi na 91-93.

[29]- Asha’ira na cewa: Kyakkyawa da mummuna al’amura biyu ne da suke daga shari’a kuma hankali ba ya hukunta kyawun daya daga cikinsu ko kuma muninsa, sai dai mai hukunta haka ita ce shari’a kawai duk abinda ta ce mai kyau to shi ke nan shi ne mai kyau wanda kuwa to munana to shi ne mummuna.

A duba littafin: Nahjul Hak shafi na 83 da Almilal wan NiNphali Juzu’i 1 shafi na 89 da Sharhut Tajrid na Kaushaji: 375.

 

عنوان الکتاب