|
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
Imaninmu Game Da Imamanci: 23- Imaminmu Game Da Imamanci Mun yi Imani cewa asalin Imamanci na daga cikin jiga-jigan addini[1] kuma imani ba ya cika sai da imani da shi kuma bai halatta a kwaikwayi iyaye a kan haka ba, ko kuma zuriya ko masu tarbiyya kome girmansu da darajarsu kuwa, sai dai ma ya wajaba ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda Ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci. Alal akalla imani da sauke nauyin da ke kan mukallafi yana daga cikin wajiban shari’a wadanda aka wajabta masa kuma sun dogara ne a ka Imani da su tabbatarwa ko korewa koda kuwa ba jigo ne daga cikin jiga-jigai da a kwaikwayi wani a kansu ba saboda shi kansa ta wannan kwibin wajibi ne a yi imani da shi. Wato ma’ana ta bangaren wajabcin sauke nauyin da ya wajaba a kansa tabbatacce daga Allah Ta’ala da kuma a hankalce; kuma ba dukansu ne aka san su ta fuskar matabbacin dalili ba don haka babu makawa a koma ga wanda muka san cewa tabbas bin sa zai kai mu ga sauke nauyin da ya wajaba a kanmu, wato mu koma ga Imam ga wanda Ya yi Imani da Imam ko kuma wani da ba Imam ba ga wadanda suka yi imani da wanin Imam. Kazalika mun yi imani cewa Imamanci tausasawa ne daga Allah kamar Annabci. Don haka babu makawa a kowane zamani ya zamanto akwai Imami mai wakiltar Annabi a aikinsa na shiryar da bil Adama[2], da dora su a kan abinda yake maslaha a Sa’adar duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancata daga mutane baki daya shi ma ya cancata domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da kiyayya daga tsakaninsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin kuma da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni ne aininhin wanda ke wajaba ayyana Imami bayan Manzon Allah. Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa Muke cewa: Lalle Imamanci ba Ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah Ta’ala a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da Ya gabata; kuma Imamanci ba nadin ko zabin kowa ba ne a tsakanin mutane[3], ba wai al’amarinsu ba ne da idan suka so za su dasa wanda suke son dasawa ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan sakaka ba su da Imami bil hasali ma “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu ne mutuwa irin ta jahiliyya”[4] kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W.A.) a hadisi. A bisa wannan asasin ba zamani da daga zamuna da zai zamanto babu Imami wanda aka wajabta yi masa biyayya ba a cikinsa, wanda kuma Allah ne Ya nada shi, sawa’un mutane sun ki ko ba su ki ba, sawa’un sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sawa’un sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, sawa’un yana hallare ne ko kuwa yana suturce ne daga idandunan mutane-domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W.A.) ya suturtu daga ganin mutane, kamar yadda ya suturtu a cikin kogo wanda game da shi Allah Ta’ala ke cewa: “Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah Ya riga Ya taimake yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma’abucinsa kada ka damu Lalle Allah na tare da mu, sai Allah Ya saukar da natsuwarSa gare shi Ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce Madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne mai hikima” Surar Tauba: 40. Ko kuma kamar yadda ya suturtu a wadi[5], to haka nan ya inganta Imami ya suturtu kuma babu bambanci tsakanin fakewa mai tsawo da gajera a hankalce. Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma ga kowace a’luma akwai mai shiryarwa.” Surar Ra’ad: 7. “Kuma babu wata al’umma face mai gargadi Ya zamanto a cikinta.” Surar Fatir: 24.
24- Imaninmu Game da Ismar Imami.Mun yi Imani da cewa Imami ma tamkar Annabi wajibi ne Ya zama katangagge daga duka munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da mantuwa ko da ganganci. Kazalika wajibi ne Ya zama katangagge daga kuskure da mantuwa da rafkanuwa domin Imamai masu kare shari’a, masu tsayiwa a kanta, halinsu tamka halin Annabi ne. Dalilin kuwa da Ya hukunta mana imani da ismar Annabawa haka na shi ne dalilin da Ya hukunta mama imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci[6] ba. Kuma ba gagararre ba ne ga Allah Ya Tare talikai duk cikin abu dai duk jimillah[7]
25- Imaninmu Game da Siffofin Imami.Mun yi Imani cewa Imami tamkar Annabi shi ma ya wajaba ya zamanto mafificin mutane a siffofin kamala, kamarsu jaruntaka, da karimci, da kamewa kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hkima da kuma kyawun hali. Dalilinmu kuma game da Annabi shi ne ainihin dalilanmu ma game da Imami a game da haka... Dangane da Iliminsa, kuwa, shi yana samun saninsa da hukunce-hukuncen ubangiji da dukan masaniyar sa ne ta gurin Annabi ko kuma Imamin da ya gabace shi. Idan kuwa aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhami daga karfin kwanyar da Allah Ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure kuma ba ya rikirkicewa kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka kuma ba ya bukatar fahintarwar Malamai[8]; koda yake ilimin nasa na iya karuwa ya kara inganta, wannan shi ne abinda ya sa Annabi (S.A.W.A.) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilimi.” Yana kunsa fadar Allah “Ka ce Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi.” Surar Taha.: 114. Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayya cewa kowa yana da wata sa’a ayyananniya ko ma awowi da yakan san wani abu shi da kansa ta hanyar kaifin fahinta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abinda Allah Ya sanya masa na karfin yin haka, wannan kudurar ta sha bamban wajen tsanani da raunana, da karuwa da kuma raguwa a bil Adama gwargwadon sabanin daidaikunsu, sai tunanin mutum ya kai ga sani a wancan lokacin ba tare da bukatar ya tsaya ya yi tunnani ko kuma tsara mukaddama da hujjoji ba ko kuma koyawar malamai ba, kuma sau da yawa mutum kan sami irin haka sau da yawa a kan kansa a rayuwa. Idan kuwa al’amarin haka yake to Ya halatta ga mutum Ya kai ga madaukakan darajojin kamala a karfin tunaninsa na saun ilhami. Wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu. Don haka mike cewa: shi a kan kansa: to lalle karfin ilhami a gurin Imami da ake kira “kuwwal kadsiyya” Ya kai ga mafi kololuwar darajar kamala, don haka yana da tsarkakar ruhi da ke daidai da karbar sannai a kowane kokaci ta kowane hali, don haka duk lokacin da Ya mai da hankali ga wani abu daga abubuwa yama bukatar Ya san shi sai Ya san shi da wannan kudurar ta “Kuwwa Kudsiya” ta Ilhami ba tare da jinkirtawa ba ko shirya wasu mukaddimomi ko kuma koyo daga bakin malami, haka abinda yake son sanin zai bayyana gare shi kamar yadda abubuwa ke bayyana a tsafta tacce madubi, babu wani dindimi ko rikitarwa game abinda Ya so sanin. Wannan kuwa abu ne da yake bayyananne game da tarihim Imamai (A.S.) tamkar Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) ba su ji tarbiyya a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwanu shekarun balaga, koda rubutu ba su koya a gurin wani ba, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu Ya shiga gurin koyon rubutu ko Ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa kuwa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa[9]. Kuma ba a taba tambayar wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar (ban sani ba)[10] daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu.[11] Alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba face wadanda ya yi tarbiyya a hannunsu da kuma guraren da ya ciro ruwayoyinsa ko kuma inda ya sami iliminsa daga mashahurai, da kuma cewa ya dakata a kan wasu matsaloli, ko kuma ya yi shakka a kan al’amura da dama kamar dai yadda al’adar mutum take a kowane guri a kowane zamani.
26- Imaninmu Game da Biyayya Ga Imamai.Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul-Amri” Shugabannin da Allah Ta’ala Ya yi umarni a yi musu biyayya[12], kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane,[13] kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin isa gare shi, kuma masu shiryarwa zuwa gare shi.[14] Kuma su ne taskar iliminSa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa,[15] don haka su ne aminai ga mazauna bayan kasa kamar kuma yadda suke su ne taurarin amincin mazauna sama. Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) Ya fassara.[16] Kazalika kamar yadda ya fada (S.A.W.A.) : “Lalle misalansu a wannan al’umma kamar jirgin Nuhu ne , wanda ya hau shi ya trias, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka.”[17] Kamar kuma yadda Ya zo a Alkur’ani mai girma su, “Sai dai su bayi ne ababan girmamawa. Ba sa zarce shi da magana kuma su da umarninSa masu aiki ne.” Surar Anbiya’i :26 - 27. Kuma su su ne wadanda Allh Ya tafiyar mmsu da datti Ya tsarkake su Sosai[18]: Bil hasali ma mun yi Imani da cewa umarninsu umarnin Allah Ta’ala ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare shi.[19] Bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne.[20] Don haka Ya wajaba mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu. Saboda haka: Mu mun yi imani cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai dai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta sai dai daga gurinsu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba Ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba Ya samun kwanciyar hankalin cewa Ya ba da wajibin da aka dora masa face ta hanyarsu.[21] Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S.) suke duk wanda Ya hau to Ya tsira wanda kuwa Ya jinkirta Ya bar su to Ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makare da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da’awowi da rikice- rikice. A wannan zamanin bayanin tabbatar da lmamai (A.S.) a matsayin cewa su ne halifofin gaskiya a shar’ance kuma shugabannl zabin Ubanjiji domin wannan al’amari ne da ya riga ya s’hude a tarihi , kuma tabbatar da hakan ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba, da kuma samar da abinda Manzon Allah (S.A.W.A.) kamar yadda Ya zo da shi din ba. Sai dai kuma karban hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kum Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu to nesanta ne daga tafarkin sawaba a addini, kuma baligi ba ya taba samun kwanciyar hankalin cewa ya saukar da abinda aka kallafa masa daga Allah Ta’ala, domin tare da kaddara cewa akwai sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a , sabani irin wanda babu mai sa ran yin daidai a kansa to kuwa babu wani abu da ya saura ga mukallafi face ya juya ga mazhabar da ya so da kuma ra’a yin da ya zaba, kai babu makawa gare shi face ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah Ta’ala wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda Ya hakikance cewa da ita ne zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abinda ake dayakinin wajibcinsa babu makawa yana bukatar a samu yakinin saukar da shi. Dalili tabbatacce da ke nuna wajabcin komawa ga Ahlul Bait, da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce ba yan Annabi (S.A.W.A.) akalla shi ne maganar Manzon Allah (S.A.W.A.) “Ni lalle na bar muku abinda idan har kuka yi riko da hi ba za ku taba bata ba har abada bayana, shi abubuwa biyu masu nauyi, dayansu ya fi daya girma, wato littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma zuriyata mutanen gidana, ku ji ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su iske ni a tabki.”[22] Wannan hadisin masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun yi ittafaki a kansa. Don haka ka kyautata nazarin wannan hadisin da kyau za ka iske abinda zai gamsar da kai ya kuma ba ka mamaki a ma’anarsa da abinda Ya kunsa, manufar maganar Manzo “Matukar kun yi riko da shi ba kwa taba bacewa bayana har abada”, tana da zurfi, kuma abinda ya bari a tsakaninmu masu nauyi guda biyu ne a hade tare, domin ya sanya su ne kamar abu guda daya bai wadatu da a yi riko da guda daya ba kawai daga cikinsu, saboda haka ta riko da su tare ne kawai ba za mu taba bacewa ba har abada. Kuma ma’anar fadinsa (S.A.W.A.) cewa “Ba za su taba rabuwa ba har su iso gare ni a tabki” a sarari take sosai, wato wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su tare ba to ba ya taba samun shiriya har abada, wannan kuma shi ne abinda ya sa suka zamanto “Jirgin Ruwan Tsira” da “Amincin Alah a bayan kasa”. Kuma duk wanda ya jinkirta ya dakata ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba. Fassarar wannan kuwa da soyayya gare su ne kawai ba tare da riko da maganganunsu da bin hanyarsu ba guje wa gaskiya ne, babu abinda ke kaiwa ga hakki illa ra’ayin rikau da gafala daga ingantacciyar hanya a bisa fassarar bayyanannen zancen Larabci.
27- Imaninmu Game da Son Ahlul Bait (A.S.)Allah Ta’ala Yana cewa: “Ka ce ni bana rokon ku wani Lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai.”[23] Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa baicin wajabcin riko ga Ahlul Bait wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi addini da soyayya gare su da kaunarsu domin a wannan ayar Allah Ta’ala Ya kayyade abinda ake rokon mutane da su yi shi shi ne soyayya ga dangi makusata. Ya zo jejjere ta hanyoyi dabam-daban da dama daga Ananbi (S.A.W.A.) cewa soyayya gare su alamar imani ne kuma kiyayya gare su alamar munafunci[24] ne da kuma cewa wanda ya so su ya so Allah da ManzonSa wanda kuma ya ki so to a ki Allah da Manzonsa.[25] Bilhasali ma soyayya gare su farilla ne da wajib ian addinin Musulunci wadda ba zai yiwu a yi jayayya ko shakka a kai ba. Dukan musulmi sun yi ittafaki a kai duk dasabanin da suke da shi kuwa a tsakaninsu a tafarkuna da ra’ayoyi in banda wata jama’a kalilan ba da aka dauke su a matsayin masu geba da Zuriyar Manzon Allah ba wadada aka yi watsi da su da suna “Nawasib” wato wadanda suka kulla gsba a zuriyar gidan muhammadu(S.A.W.A.). Don haka ne ma ake kidaya su a cikin masu karyata waiban addinin musulunli’ tabha- tattu , mai karyata wayiban addinin mu- cin zokkato ana kidaya ahi ne a aikih hukunlinwanda Ya karyata ainihin addinin musulmci’, kai tabbatacce ne ma cewa shi’ ya karyata Sakon koda kuwa a zahiri ya yi furui’ da kalmar shahada. Wannan shi ne abinda ya sa kiyayya ga zuriyar Muhammadu (S.A.W.A.) ta zama daga cikin alamun munafunci, soyayya gare su kuma daga alamun imani, saboda haka ne kuma har wa yau kiyayya gare su ta zama kiyayya ga Allah da ManzonSa, kuma babu’ shakka Allah Ta’ala bai farlanta soyayya gare su ba sai don sun cancanci soyayya da biyayya, ta bangaren kusacinsu gare shi Ta’ala, da matsayinsu a gurinSa, da tsarkakarsu daga shirka da sabo, da kuma daga dukan abinda zai nesantar daga gidan karamarSa da farfadiyar yardarSa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa Allah Ta’ala Ya wajabta son wanda ke aikata sabo, ko kuma wanda ba ya bin sa yadda ya kamata, domin shi ba shi da wata kusantaka ko abota tare da kowa, mutane a gurinsa ba kome ba ne illa bayi halittattu a matsayi guda, sai dai kawai mafifici a cikinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoron Allah daga cikinsu.[26] Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafificinsu a takawa, kuma mafi darajarsu baki daya, idan da ba don haka ba kuwa to da waninsa ya fi cancantar haka, ko kuma da kenan Allah Ya fifita wani sashe a kan wani a wajabcin soyayya da biyayya haka nan siddan sarmadan ba tare da cancanta ko karama ba.
28- Imaninmu Game da Imamai (A.S.)Ba mu yi imani game da Imamai (A.S.) irin yadda ’Yan Gullatu[27], masu wuce iyaka suka yi ba haka nan ba mu yi irin yadda ’Yan Halluyuna[28] suka yi ba, “Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girmama.” (Surar Kahf: 5). Mu Imaninmu a kebe shi ne cewa su mutane ne kamar mu, suna da abinda muke da shi, kuma abinda yake kanmu yana kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah Ya kebance su da karamarSa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dai dukan kyawawan dabi’u mafifita na da kyawaya sifofi, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abinda aka kebance su da shi. Da wannan ne kuma suka cancaci su zamo Imaman shiriya, da kuma duk abinda yake ya shafi bayanin shari’a da kuma abinda ya kebanci shari’a da kuma abinda ya kebanta da Akur’ani na daga tafsiri da bayani. Imam Sadik (A.S.) Ya ce: “Duk abinda Ya zo muku daga gare mu wanda bai halatta ya zamanto daga halittu ba kuma ba ku san shi ba ba ku fahince shi ba to kada ku musa shi ku mayar da shi gare mu, kuma abinda ya zo muku daga abinda bai halatta ya kasance daga halittu ba ku musa shi kuma kada ku mayar da shi gare mu.”[29]
29- Imaninmu Game da Gewa Imamanci Sai da NassiMun yi imani cewa Imamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah Ta’ala a harshen ManzonSa, ko kuma a bisa harshen lmamin da ya k;asance da nassi idan har ya so ya ba da nassi game da lmamin bayansa. Hukuncin lmamanci a kan haka tamkar hukuncin Annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah Ya ayyana shi mai shiryarwa da datarwa ga bil Adawa baki daya, kamar kuma yadda ba su da hakkin ayyana shi ,ko kuma kaddamar da shi , ko zabensa, domin wanda yake da tsarki da kwazon daukar alkyabbar lmamanci baki daya da kuma shiryawa da illahirin bil Adama gaba daya bai dace ya san wami abu ba face da sanarwar Allah kuma bai kamata a ayyana shi ba face da ayyanawar Allah.[30] Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W.A.) Ya ba da nassi game da halifansa kuma lmamin talikai Aliyu Bin Abi Talib Amirul muminina (A.S.) , amini a kan wahayi lmamin halittu, ya ayyana shi a gwrare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai’a a kan shugabancin Muminai ranar Gadir Ya ce: “A ji a fadaka duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne, Ya Allah ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka tozorta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya.”[31] Daga cikin guraren farko dangane da nassi a kan lmamancinsa maganarsa (Manzo) yayin da ya kirayi danginsa makusata da ’Yan ’uwansa na kusa kuma Ya ce. “Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina kumaHalifana ku bi shi”[32] a yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma Ya maimaita maganarsa sau da dama cewa: “Kai a gare ni matsayin Haruna ga Musa kake sai dai kawai babu Annabi ne bayana.”[33] Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar da ke cewa: “Tabbatacce kawai shi ne cewa Allah ne Majibincinku da ManzonSa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka su suna masu ruku’i.” Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya ba sadakar zobensa yana cikin ruku’u.[34] Bin diddigin dukan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur’ani ba ya goyon bayan cewa wannan sakon kagagge ne kazalika bayani manufofinsu da suke nuni da su.[35] Sa’an nan shi kuma kansa (A.S.) Ya ba da nassi game da Imamancin Hasan da Husain (A.S.), shi kuma Husain[36] ya ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (A.S.) haka nan dai Imami ke ba nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.
30- Imaninmu Game da Adadin ImamaiMun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamanci na gaskiya, su ne wadanda muke komawa gare su a hukunce-hukuncen shari’a wadanda aka ba da nassi game da Imamancinsu su goma sha biyu ne, Annabi (SAWA) ya ba da nassi a kansu dukkaninsu da sunayansu[37], sa’an nan kuma duk wanda Ya gabata daga cikinsu to Ya ba da nassi a kan wanda ke biye da shi kamar haka:-
Shi ne Hujjar wannan zamanin namu, shi ne boyayyen da ake jira, Allah Ya gaggauta bayyanarsa Ya saukaka mafitarsa, domin Ya zo Ya cika kasa da adalci da daidaito bayan an cike ta da zalunci da ja’irci.
31- Abinda Muka Yi Imani da shi Game da Mahadi (A.S.)Lalle yin albishir game da bayyanar Mahadi’ (A.S.) daga’ya’yan Fatima (A.S.) a karshen Zamani -domin ya cika kasa da daidaitawa da adalii bayan an cika ta da zalunci da jairci- tabba-tacce ne daga Annabi (SAWA) daga hanyoyin ru- waya dabam-daban masu yawa, kuma dukan musulmi sun ruwaito hadisi game da haka a bisa mababantan hanyoyinsu na karbar ilimi.[38] Kuma Wannan ba wani sabon ra’ayi ba ne da Shia suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci da ja’irci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarki game da bayyanar wani da zai tsarkake kasa daga kazantar zalunci kamar yadda wasu ’Yan rikikitarwa marasa insafi ko adalci suke kintatawa.[39] Idan da ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S.) daga Annabi (SAWA) ta yadda dukan musulmi suka sani ba ya kuma kafu a zukatansu suka yi imani da shi ba to da masu da’awar imani da Mahadi (A.S.) a karnonin farko kamarsu kisaniyawa[40] da Abbasawa da wasu daga cikin Alawiyawa da sauransu ba su iya sun yaudari mutane sun yi amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci ba, domin sun sanya da’awarsu ta karya game da Mahadi (A.S.) hanyar tasiri a kan jama’a gama gari da kuma yada karbuwarsu a kansu (jama’ar). Mu kuwa duk da Imaninmu da ingancin addinin Musulunci, da kuma cewa shi ne cikamakin addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani addini da zai zo ya gyara bil Adama, tare da dukan abinda muke gani na yaduwar Zalunci, da yawaitar fasadi a duniya ta yadda ba za ka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashe mallakakku, tare kuma da abinda muka gani kuru-kuru na nesantarsu da addininsu su da kansu, da kuma jingine hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a dukan kasashen musulinci da kuma rashin lizimtuwarsa ga dubban hukunce-hukuncen musulunci amma duk da haka babu makawa lalle ne mu saurari budi yayin da addinin musulunci zai dawo da karfinsa da iya warsa da gyaran wannan duniyar da ta dulmuye a cikin rashin gaskiyar zalunci da fasadi. Sa’an nan kuma ba zai yiwu ba ga musulunci ya dawo da karfinsa da shugabancinsa a kan bil Adama baki daya yana cikin halin da yake ciki a yau da ma kafin yau din na daga sabanin mabiyansa a dokoki da hukunce-hukunce da ma ra’ayoyinsu game da shi tare kuma da kasancewarsu a halin da suke ciki a yau na daga bidi’a da fandarewa a dokokinsa da ma bata a da’awarsu. Na’am ba zai yiwu ba addini ya koma ga karfinsa sai dai idan har wani mai gyara babba ya bayyana ya shige masa gaba, yana hade kalma guri guda kuma yana soke abinda aka lika masa na daga bidi’a da bata tare da taimakon Ubangiji domin Ya sanya shi ya zamanto shiryayye mai shiryarwa, mai girma da Shugabanci na gaba daya da kuma iko wanda ya saba wa al’ada domin ya cika ta da daidaituwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da jairci. A takaice dai dabi’ar mummunan halin da dan Adam ke ciki wanda Ya kai kololuwa a fasadi da zalunci kuma da imani da cewa wannan shi ne cikaton addinai tare kuma da imani da ingancinsa na tabbatar da jiran wannan Mahadi (A.S.) mai kawo gyara domin Ya kubutar da duniya daga halin da take ciki. Saboda haka ne dukan bangarorin Musulmi suka yi imani da wannan jiran, kai hatta ma al’ummun da ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da ke akwai tsakanin mazhabar Imamiyya shi ne cewa Mazhabar Ja’afariyya, Imamiyya ta yi imani da cewa wannan mai gyaran wato Mahadi (A.S.) mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekara ta 256 Hijiriyya kuma bai gushe ba yana nan da rai, shi ne dan Imam Hasan Askari (A.S.) kuma sunansa “Muhammad”. Wannan kuwa saboda abinda Ya tabbata daga Annabi (SAWA) da kuma Ahlul Bait (A.S.) game da alkawari [41] game da shi, da kuma hadisan da suka tabbata a gare mu ta hanyoyin ruwaya dabam-daban masu yawa game da haihuwarsa da kuma bayyanarsa. Ba ya halatta Imamanci ya yanke, ko Ya katse a wani zamani daga zamuna[42] koda kuwa Imamin a boye yake, domin ya bayyana a ranar da Allah Ya yi alkawari wanda kuma wannan daga cikin asirran Ubangiji babu wanda ya san su sai Allah. Ba zai gagara ba cewa wannan rayuwa tasa mai tsawo da dogon zamaninsa su zama Mu’ujiza da Allah Ta’ala Ya ba shi, kuma wannan ba ta fi Mu’ujizar kasancewarsa Imami yana dan shekara biyar kawai ba, yayin da mahaifinsa ya koma ga Ubangiji[43] Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S.) girma ba yayin da ya yi magana da mutane yana cikin shimfidar jaririnsa yana yaro, kuma aka aike shi Annabi ga mutane. Tsawon rayuwa fiye da dabi’a kuwa, ko kuma ga wanda ya dauka cewa ta dabi’a ce - fannin Likitanci ba zai hana ta ba kuma ba zai shamakance ta ba, sai dai kawai cewa ilimin likita bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba, idan kuwa har ya gaza ai Allah Ta’ala mai iko ne a kan kome, kuma haka ya auku tabbatacce a tsawaita rayuwar Annabi Nuhu[44] (A.S.) da Wanzar da Annabi Isa[45] (A.S.) kamar yadda Alkur’ani ya bayyana. Idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abinda Alkur’ani ya ba da Labari game da shi to musulunci kam sai wata rana. Abin mamaki ne har Musulmi ya tsaya yana tambaye-tambaye game da yiwuwar haka alhali kuwa yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi. Daga cikin abinda lalle ne mu ambata shi a nan shi ne cewa zaman jiran ba wai yana nufin cewa musulmi su nade hannuwansu ba ne game da al’amuran da suke na gaskiya dangane da addininsu da abinda Ya wajaba na taimaka masa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da yakkyawa da hani da mummuna. Bilhasali ma musulmi dimin da’iman an kallafa masa ya yi aiki da abinda Allah Ya saukar na daga hukunce-hukuncen Shari’a kuma ya wajaba a kansa Ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon abinda ya iya kuma ikon yin haka ya samu gare shi: “Dukanku makiyaya ne kuma dukanku ababan tambaya ne game da abin kiwonSa.”[46] Don haka bai halatta gare shi ba ya jinkirta wajibansa don kawai yana jiran Mahadi (A.S.) mai kawo gyara, mai shiryarwa, wanda aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya sauke aikin da aka kallafa, kuma ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama sun bar aiki.
32- Imaninmu Game da Raja’a -komowa-Abinda Mazhabar Ja’afariyya -Imamiyya take kai- tare da riko da abinda ya zo daga Ahlul Bait (A.S.) Shi ne cewa Allah Ta’ala zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa, duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, zai daukaka wasu kana kuma zai kaskantar da wasu, kana zai rarrabe masu gaskiya daga cikinsu daga marasa gaskiya, da wadanda aka zalunta daga azzalumai, wannan zai auku ne bayan bayyanar Mahadi daga zuriyar gidan Manzon Allah mafifita tsira da aminci su tabbata a gare su. Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka, ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna. Bayan nan kuma sai a mutu daga nan kuma sai zuwa tashin Alkiyama zuwa ga abinda suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah Ta’ala Ya kawo a cikin Alkur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din ke yi, wato wadanda ba su gyaru ba da komowarsu, don haka suka sami ukubar Allah kan cewa a dawo da su zuwa na uku ko sa gyaru; “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu to mun yi ikrari da zunubanmu shin akwai wata hanyar fita.” Surar Mumin: 11. Na’am Alkur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama kuma daga Ahlul Bait (A.S.) suka zo a kan haka, mabiya Mazhabar Ja’afariyya ko kuma Imamiyya sun yi ittifaki a kan haka sai dai ’Yan kalilan daga cikinsu da suka yi tawilin abinda ya zo game da raja’a da cewa Ma’anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani ga Ahlul Bait da bayyanar Imamin da ake jira (A.S.) ba tare da komowar wasu ayyanannu ko raya matattu ba. Batun raja’a kuwa a gurin Ahlus Sunna yana daga cikin abin ki wand imani da shi Ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a a matsayin suka ga mai ruwaya da kuma abin kiyayya gare shi wadda ke wajabata kore ruwayarsa da watsi da ita, kuma Ya bayyana cewa suna kirga ta a matsayin karfirci da shirka, har ma ta fi muni, don haka, wannan na daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a Imamiyya da shi da kiyayya da su a kansa. Babu shakka wannan duk wata mafaka ce kawai da bangarorin kungiyoyin musulunci da can suka kasance suna riko da ita don sassansu su soki sashe da shi, kuma alal hakika mu ba muga wani abu da zai halatta wannan mafakar ba domin imani da raja’a ba ya soke imani da tauhidi kuma ba ya soke imani da Annabci bilhasali ma kara inganta akidu biyun yake yi Domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya tamkar dai tashin Kiyama da tayar da mamata, kuma tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wadanda ya inganta ta zama Mu’ujiza ga Annabinmu Muhammadu (SAWA) da zuriyar gidansa. Kuma ita raja’a tamkar mu’ujizar raya matattu ce wadda ta kasance ga Annabi Isa (A.S.) ne sai dai ma ta fi ta cika a nan domin wannan za ta zo ne bayan mamata sun zama rididdigaggu. “Ya ce wane ne zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdi gaggu. Ka ce zai raya su wannan da ya fare su karon farko kuma shi game da dukan halitta masani ne.” Surar Yasin: 79-87. Amma wanda Ya soki raja’a kuwa da dalilin cewa tana daga shafewa batacciya to lalle bai fahinci bambanci tsakanin “tanasuhi” da kuma ainihin tayar da mamata da ainihin jikinsu ba, ita raja’a wani nau’i ne na tayar da mamata da ainihin jikinsu. Domin ma’anar tanasuhi ita ce kauratar da rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba, ma’anar tayar da matattu da ainihin jikkunansu kuwa ba haka take nufi ba, ma’anarsa ita ce komo da ainihin jikin da ainihin abubuwan ransa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa har aka ce “Raja’a” “Tanasuhi” ce to raya mamata da Annabi Isa (A.S.) ma ya kasance yana yi “tanasuhi” ce to tayar da mamata da komo da ainihin jikkunan mamata ma “tanasuhi” ne ke nan. Saboda haka babu abinda ya saura illa Muhawara ta fuska biyu game da “Raja’a”. Na farko: Korarriya ce sam ba za ta auku ba. Ta Biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita. A bisa asasin Kaddara cewa muhawarorin biyu daidai suke, sam yin imani da ita ba a daukar sa a matsayin kyamar da masu adawa da Shi’a suka juya ta. Kuma nawa ne daga cikin abubuwan da suke daga cikin korarru wadanda sauran bangororin musulmi suka yi imani da su ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalin su da dama A cikinsu akwai: Yarda da yiwwar rafkanuwa ga Annabi (SAWA) ko kuma aikata sabo[47] da kuma imani da Wanzuwar Alkur’ani[48] da kuma batun “Wa’idu”[49] da kuma imani da cewa Annabi bai ba da nassi kan halifan bayansa ba. To dangane da Muhawarori biyun da muka kawo a dauka cewa ba su da wani asasin ingancin tabbatar da Raja’a amma ai mun riga mun bayyana cewa ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da mamaci ko kuma komo da ainihin jiki, sai dai kawai cewa ita tana aukuwa ne a wannan duniyar. Dalilin kuma da ke tabbatar da yiwuwar tashin kiyama shi ne dalilin da ke tabbatar da ita babu wani abu kuma da zai sa a yi al’ajabi game da ita sai dai kawai don zukatanmu ba su saba da ita ba ne a rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu da sabubbanta da abubuwan da ke hana ta da za su sa mu yi ikrari da ita ko mu kore ta, da kuma fahimtar cewa abu ne marar sauki ga mutum Ya yarda ya gaskata abinda bai saba da shi ba, wannan kuwa kamar wanda ya ga cewa tayar da mamata abu ne bako ya ce: “Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce Masa: “Wanda Ya fare su a karon farko shine zai raya su kuma shi a kan kome masani ne”. (Yasin: 78-79) Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali akai na tabbatar da ita ko kore shi, ko kuma muka raya rashin dalili to wannan kuwa zai kallafa mana komawa ga nassosin addini wadanda suke daga tushen wahayin Ubangiji. Kuma abinda zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Alkur’ani kamar dai Mu’ujizar Annabi Isa (A.S.) a raya matacce: “Kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho da kuturu kuma ina rayar da matattu da izinin Allah.” Surar Ali Imran: 49. Da kuma fadin Allah Ta’ala: “Ta yaya Allah Zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah Ya matar da shi Shekara dari sa’an nan kumo Ya raya shi.” Surar Bakara: 259. Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa: “Suka ce Ya Ubangijinmu Ka matar da mu sau biyu.” Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba za ta fito daidai ba ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba koda yake wasu masu tafsiri sun wahalar da kansu wajen yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba. Muhawara ta biyu kuwa wadda ke cewa hadisai game da ita Raja’a Kagaggu ne kawai wannan da’awar ba ta da wani asasi, domin Raja’a na daga cikin al’amuran da suke ba makawa sun zo daga Ahlul Bait (A.S.) daga hadisai masu tafarkunan ruwaya da dama. Bayan duk wannan ashe ba a yi mamaki ba game da mashahurin marubuci mai da’awar sani kamar Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, saboda yana cewa; “Ai Yahudanci Ya bayyana a cikin Shi’anci ta hanyar batu game da raja’a[50].” Don haka ni nake cewa gare shi: “To ai Yahudanci ma ya bayyana a Alkur’ani game da batun Raja’a” kamar yadda ya gabata game da ayoyin Alkur’ani da suka ambaci raja’a. Za kuma mu kara masa da cewa: Alal hakika babu makawa Yahudanci da Nasaranci su bayyana a cikin da dama daga abubuwan da aka yi imani da su da kuma hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi Mai girma (SAWA) ya zo yana mai gaskata Shari’o’i da suka gabata[51] kuma koda yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. To bayyanar Yahudanci da Nasaranci a wasu abubuwan da Musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin Musulunci idan ma har aka dauka cewa Lalle Raja’a daga akidojin Yahudanci take kamar yadda wannan marubucin yake da’awa. Ko ta halin kaka dai Raja’a ba wai tana daga cikin ji’ga-jigan addinin (Musulunci) da ya wajaba a dauke ta a akida ba ne da kuma yin bincike a kanta sai dai kawai imani da muka yi da ita biyayya ne ga hadisai ingantattu daga Ahlul Bait (A.S.) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga Karya, kana kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita kuma aukuwarta ba gagara badau ba ne.
33- Game da TakiyyaAn ruwaito daga Imam Sadik -Sadiku AhlulBait- (A.S.) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya addinina ce[52] kuma addinin iyayena ce.” Da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi.”[53] Kazalika haka nan ta kasance taken Ahlul Bait (A.S.) wajen kore cutar da su kansu da kuma ga mabiyansu da kare jininsu sa’an nan da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hade kalmarsu da taro tsakaninsu.[54] Kuma Mazhabar Shi’a Imamiyya ba ta gushe ba ana saninta da takiyya ba kamar sauran jama’o’i da al’ummu ba, dukan mutum kuma idan ya ga’alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yada abinda ya yi imani da shi ko kuma fito da shi sarari babu makawa ya boye ya kare a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar han- kali ke hukunci da shi. Abu ne sananne cewa Mazhabar Shi’a lmamiyya da lmamansu sun sha nau’o’in jarrabawa da matsa lamba da babu wata jama’a[55] da ta sha irinta. Saboda haka ne ya zamanto tilas gare su a yawancin lokuta su yi takiyya suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyana hakikanin abinda bayyanarwar ke jawowa a addini da kuna duniya. Saboda wannan ne suka bambantu daga wadanda ba su takiyya kuma aka san su da ita banda wasunsu. Takiyya tana da hukunce-hukunce dangane da wajabcinta da rashin wajabcinta gwargwado sassabawan guraren tsoron cutarwar kamar yadda aka ambata a littafan malaman fikihu. Takiyya ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya halatta kuma saba mata kan wajaba a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiyada fitowadaita sarari ya zama taimako ne ga addinin musulunci da jihadi a tafarkinsa, to a wannan lokacin sai a yi banza da dukiya kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya na iya zama haram [56] a ayyukan da ka iya wajabta[57] kashe rayuka masu alfarma ko kuma yada karya, ko barna a addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su ko kuma yada zalunci da ja’irci a tsakaninsu. Ko ta halin kaka dai takiyya a gurin Shi’a Imamiyya ba wai tana nufi zamar da su ‘yan wata kungiyar asiri ba ne domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi’a marasa fahimtar al’amura ke surantawa kuma ba sa dora wa kansu nauyin su zo su san ingantaccen ra’ayin daga garemu.[58] Kamar kuma yadda ma’anarta ba ita ce asanya addini ya zama wani sirri daga asirran da bai halatta a bayyana shi ba ga wanda bai dauke shi a matsayin addini ba, ta yaya zai zamanto haka alhali littafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu dangane da fikihu da hukunce-hukunce bayanai game da akida sun game duniya, sun ma wuce Yadda ake tsammani daga kowace al’umma da ke bin addininta? E, gaskiya ne makiyanmu da ke nufin Kiyayya da Shi’a sun munana amfani da takiyya sun sanya ta daya daga cikin abubuwan soke-soke ga Shi’a, tamkar ka ce ba sa wadatuwa har sai dai in an sassare wuyansu domin a ga bayansu baki daya a wancan zamanin da cewa mutum Shi’a ne kawai ya isa ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Bait daga Umayyawa da Abbasawa hatta zuwa Zamanin daular Usmaniyya. Idan sukan mai suka ya dogara ne da abinda yake zaton cewa suka ba halas bane a addini to sai mu ce masa: Na Farko: Mu dai masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S.) mu muna bin shiriyarsu ne su ne suka umarce mu da ita, kuma su ne suka farlanta ta a kanmu a lokacin bukata, kuma ita tana daga addini a gurinsu kuma lalle ka ji hadisin Imam Sadik (A.S.) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi.” Na Biyu: Shar’anta ta kuma Ya zo a Alkur’nai mai girma, wato fadar Allah Ta’ala cewa: “Sai dai wanda aka tilasta shi Zuciyarsa kuwa tana natse da imani.” Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar bin Yasir wanda ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan musulunci. Da kuma fadin Allah Ta’ala: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya.” Surar Âli Imran: 28. Da kuma: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ce.” Surar Gafir: 28.
[1]- Imamanci shi ne jigo na hudu a cikin jiga-ijgan musulunci a gurin Mazhabar Ahlul Bait Masu bin Imamai goma sha biyu, wato Shi’a Imamiyya, Imamanci kuma yana bayan Annabci a muhimmanci kuma zaa iya cewa ita ce ka’idar da ke bambance Mazhabar Imamiyya daga sauran Mazhobabi na Musulunci; kuma Imamanci asasi ne na tunani da Mazhabar mabiya Ahlul Baiti suka gina Mazhabarsu a kai. Imamanci: a lugga yana nufin shigewar gaban wani mutum domin sauran mutane su bi shi su yi koyi da shi, don haka Imami shi ne wanda mutane suke koyi da shi mutanen da ke bin sa kuma su ne mamu. Jam’insa kuma shi ne Imamai kalmar Imami ta zo a Alkur’ani har sau goma sha biyu gurare dabam-daban. Akwai guraren da ta zo da sigar mufradi ba jam’i har sau bakwai a: Surar Bakara aya ta 124 da Surar Hudu: 17 da Surar Hijri aya ta: 79 da Surar Isra’i aya ta: 71 da Surar Furkan aya ta 74 da Surar Yasin aya ta 12, da Surar Ahkaf aya ta 12. Sa’an nan kuma akwai guraren da ta zo da sigar jami’ sau biyar wadanda su ne kamar haka: “Surar Taubati:12 Surar Anbiyai aya ta 73 Surar Kasas aya ta s da kama ta 41 da Surar Sajdati aya ta 24”. Ma’anarsa ta Ka’ida kuwa Imamanci yana nufin: Mukami ne da Ubangiji Allah kan zabi bayinSa ya ba su kamar yadda yake zaben Annabawa, kuma yakan umarci Annabi ya sanar wa Al’umma wannan Imamin ya kuma umarci mutane da su yi masa biyayya. Mutane ba su da wani ikon su zaba wa kansu Imami: Allah Ta’ala yana cewa: “Kuma Ubangijinka yakan yi halitta kuma yana zabe su ba su da wani zabi.” Surar Kasas: 68. Shi Imami ya bambanta da Annabi ne da cewa Annabi ana yi masa wahayi shi kuwa Imami ba a yi masa wahayi, shi Imami yana karbar hukunce-hukunce ne daga Annabi da shiryarwar Ubangiji. Don haka shi Annabi mai isar da sako ne daga Allah shi kuma Imami mai isarwa ne daga Annabi. Wannan shi ne abinda Mazhabar Ahlul Bait ke nufi da Imamanci. Amma a gurin sauran Mazhabobi kuwa Imamanci na nufin shugabanci ne na gaba daya a kan al’amuran addini da al’amuran duniya don Halifantar Annabi (S.A.W.A.) da hukunce hukuncensa a rassan al’amuran ibada. Domin karin bayani a duba littafan luga, da Aslus Shi’a wa Usuliha da Al’aka’iduj Ja’afariyya da Milal Wan Nihal na Shahristani da Sharhil Makasid. [2]- Allah Ta’ala Yana cewa: “Mu Mune Muka aika Manzo mai albishir kuma mai gargadi kuma babu wata al’umma face mai gargadi ya je mata”. Surar Fatir: 24. Hadisai da dama da ke nuna cewa kasa ba ta taba zama babu Hujja. A duba Usul Kafi Juzu’i na 1 shafi na 136 Babun Annal Aradha Lâ Takhlû minal Hujja, da kuma na 137 Babun Annahu Law Lam yabka fil Ardhi Illa Isnani La kana Ahaduhuma Hujja. [3]- Ya riga ya shahara a tsakanin malaman addinin Musulunci game da sanya Imami akwai maganganu biyu da ba su da na uku. Akwai masu cewa Imamanci ra’ayi ne kuma zabin mutane ne ke ayyana shi. Akwai kuma wadanda ke cewa ayyanawa ne daga Allah. Kuskuren ra’ayi na farko abu ne da shi’a Imamiyya suka yi ittifaki a kai domin wajibi ne Imami ya zama Allah ne Ya ayyana shi kuma shi kuma Annabi ya nuna shi ya kuma yi wasici da yi masa biyayya bayansa-wato kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) Ya yi a Ghadir Khum- sa’annan shi kuma Imamin sai ya yi wasici da biyayya ga mai zuwa bayansa kuma ya sanar da shi, haka nan za a yi ta yi bi da bi. Ko kuma a ga wata Mu’ujiza ta bayyana a hannunsa domin “Isma” Sharadin Imamanci ce kuma tana daga boyayyun al’amura wadda babu wanda ya san ta sai Allah Ta’ala. Su kuwa sauran Mazhabobi da ba Imamiyya ba cewa suka yi: Imamanci ba a shardanta nadawar Annabi ko alkawartawarsa game da shiba, yana iya zama ta hanyar yin Mubaya’a, wato shi ne malamai masana halal da haram su yi wa wani mutum guda mubaya’a su sanya shi Imami-wannan kuwa yana ginuwa ne a kan sharadin rashin Isma ga shi Imamin kuma ba sharadi ba ne yazamanto duka kowa da kowa ya yi masa mubaya’a hatta mubaya’ar mutum guda ma tana iya wadatarwa. Idan kuwa har Mubaya’ar ba ta yiwu ba to akwai wata hanyar nada Imamin: Tilastawa da kankanewa, idan Imami ya mutu wani wanda ya cika sharuda ya maye gurbinsa ba tare da an sanya shi ko an yi masa mubaya’a ba ya kuma tilastawa mutane kansa to halifancinsa ya tabbata koda kuwa fasiki ne Jahili, Ja’iri Azzalumi kuma suka ce bai halatta ba a tsige Imami koda kuwa fasiki ne amma idan da wani da ya fi shi karfi zai zo ya kifar da shugabancinsa ya kuma tilasta kansa a kan mutane to da shi ma ya zama Imami. Tambaya a nan ita ce shin hankali yana yarje wa mutum ya bi mazhabar da ke wajabta biyayya ga Imami Fasiki Ja’iri, Jahili ba don kome ba sai dan kawai shi ne ya fi karfi da kudurar tilasta kansa a kan wasu koda ta hanyar fasikanci da ja’irci? Kuma bai halatta a cire shi ba sai dai da wanda ya fi shi karfi ya tilasta shi sa’an na shi ya zamanto shi ne Imamin? Shin wannan shi ne Imamin da idan mutum ya mutu bai san shi ba ya mutu mutuwar jahiliyya? To wannan Mazhabar ina matsayinta game da maganar Allah Ta’ala cewa: “Shin wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya shi ne ya fi cancantar a bi shi ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai an shiryar da shi, me ya same ku yaya kuke hukunta haka?” Surar Yunus: 35. A duba Littafin “Nahjul Hakk wa kashussidki shafi na 168. Da sharhul Makasid na Taftazani Juzu’i na 5 shafi na 233, da At- Tamhid na Bakilani: 168 da Aslus shi’a wa Usuliha 22’da Aka’idi Ja’afariyya: 29. [4]- Al- Kafi Juzu’i: 1 shafi na 377 hadisi na 3 da Al- Mahasin Juzur’i na 1 shafi na 176 hadisi na 273, da Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu’i na 2 shafi na 58 hadisi na 214 da Kamaluddin shafi na 413 Hadisi na 15, da Al-Gaybatu na Nu’umani shafi na 130 hadisi na 6, da Rijal Al- Kasshi Juzu’i na 2 shafi na 723 hadisi na 799, da musnad Al- Tayalasi shafi na 259 hadisi na 1913, da Hilliyatul Awliya’u Juzu’i na 3 shafi na 224 da Al- Mu’ujamul Kabir na Tabarini Juzu’i na 10 sha na 350 hadisi na 10687, da Mustadrakul Hakim Juzu’i na 1/77 da Sharhun Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu’i na 9 shafi na 155 da Yanabi’ul Muwadda Juzu’i na 3 shafi na 155 da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 5 shafi na 224 da Musnad Ahmad Juzu’i na 4 shafi na 96. [5]- Wadi shi ne fili tsakanin duwatsu biyu. Wadin da ake nufi a na shi ne wadin da ake kira “wadin Abi Talib (A.S.) wanda Bani Hashim da Banu Abdul Mutallibi bin Abdu Manaf, in banda Abu Lahab ba, suka shiga cikinsa har na tsawo shekaru biyu ko kuma uku yayin da Kuraishawa saka sunya masu fago don kada wani ma ya kai musu abinci. A duk tsawan wannan lokacin sun kasance suna amfani da dukiyar Nana Khadija ne da ta Abu Talib har suka kare. A lokacin ba su kasance suna fita daga wannan wadi ba sai dai lokacin Umura a watan Rajab da kuma lokacin aikin haji. A wannan lokacin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) shi ne ya kasance yana fita a boye zuwa Makka yana samo musu abinci. A duba As- Sahih Fi Siratin Nabi Juzu’i na 2 shafi na 108, da Lisanil Arab Juzu’i na 1 shafi na 499. [6]- Idan da ba don sun kasance ma’asumai ba to da ba su cancanci su zamo Halifofin Annabi (S.A.W.A.) domin rashin Ismarsu zai kare a dori a kan dori ne marar iyaka. Domin dalilin bukatar Imami bayan Annabi (S.A.W.A.) shi ne rashin Ismar mutane don haka suke bukatar wanda zai sa su a tafarki madaidaici, idan kuwa mai shiryarwar bai zama Ma’asumi ba to lalle da akwai bukatar wani ba shi ba wanda wannan zai sa a yi ta bi ni in bi ka har abada. Awa’ilul Makalat Shaikh Mufid 37 Tajridul I’itikad: 222. [7]- Dala’ilul J’ijaz 196 (218), da 424 (499) da 428 (502) Diwani Abi Nuwas. [8]- Domin a bisa dabi’a idan da yana bukatar malami ta da malamin nasa ya fishi ilimi a kan abinda ya koya masa don haka sai ya zama tilas ya bi shi a umarnin da ya masa kuma shi kansa malamin yana bukatar malami sai al’mari ya zamanto bi ni in bi marar iyaka. Don haka ne ya zama wajibi Imami ya zaman mafi ilimin zamaninsa. [9]- Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W.A.) ya sanar da ni Babi dubu, kowane Babi daga cikinsu kuma yana bude Babi dubu, wato Babi dubu-dubu kenan har sai da na san abinda Ya kasance da wanda zai kasance har zuwa ranar Tashin kiyama, kuma na san ilimin Bala’o’i da Mutuwa da kuma fasahar magana” Al- Kafi Juzu’ina 1 shafi na 239, Yanabi’ul Muwadda Juzu’i na 1 shafi na75. Kazalika ya kara cewa: “Wallahi idan da na so da ba wa kowa daga cikin labarin in da ya fito da inda zai je da dukan al’amuransa da na yi haka, amma ina jin tsoro ne kada ku kafircewa Manzon Allah (S.A.W.A.) a kaina. Ku sani cewa ni zan sanar da shi ga wani daga cikin kebabbun da aka amince da shi game da haka. Na rantse da wanda ya aiko shi da gaskiya ya kuma zabe shi a kan ba na magana face gaskiya. Kuma tabbas ya sanar mini da wannan duka da kuma mutuwar duk wanda zai mutu da tsiran wanda zai tsria da kuma makomar wannan al’amarin. Bai bar wani abu da ke shiga kaina ba face ya saka mini shi a kunnena ya bayyana mini shi.” Nahjul Balaga Huduba ta 175. [10]- Ya zo a hadisi daga Hisham Bin Hakam cewa Imam Sadik (A.S.) ya ce “Lalle Allah Ta’ala ba Ya sanya hujjarsa a bayan kasa a tambaye shi ya ce ban sani ba.” Al- Kafi Juzu’i na 1 shafi 177 karshen hadisi na 1 Tanbihi na 32. [11]- Abu ne da ya shahara daga Amriul Mumini Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: “Ya ku mutane ku tambayelini kafin ku rasa ni, na fi sanin hanyoyin sammai fiye da na kasa” Nahjul Balaga Huduba ta 184. [12]- Ishara ga fadar Allah Ta’ala: “Ya ku wadanda suka yi Imani ku bi Allah ku bi Manzo da shugabanni daga cikinku kuma idan kuka yi jayayya a kan wani abu ku mayar da shi ga Allah da Manzo idan kun kasance masu imani da Allah da Ranar Lahira wannan shi ne alheri kuma mafi kyau.” Surar Nisa’i: 59. [13]- Ya zo daga Imam Bakir (A.S.) da kuma Imam Abi Abdullah Sadik (A.S.) cewa sun ce: “Mu mu ne al’umma tsakatsaki, mu mu ne shaidun Allah a kan halittunSa”. Al-Kafi Juzu’i na 1 shafi na 146 Hadisi na 2 da na 4 inda ayar nan ta zo “Haka nan muka sanya ku al’umma matsakaiciya domin ku kasance shaidu a kan mutane Manzo kuma ya zama shaida a kanku”. Surar Bakara: 143. [14]- Saboda su su ne Imamai na gaskiya, ya zo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ta fuska maruwaita da dama cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwar jahiliyya” A duba Abinda Muka Yi Imani da shi game da Imamai. Ya zo daga Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: “Lalle idan da Allah Ya so hakika da Ya sanar da bayinsa kansa amma Ya sanya mu kofofinsa, da Tafarkinsa, da hanyarsa, da kuma mafuskantarSa da ta nan ne ake zo masa, duk wadanda suka fandare da shugabancinmu ko kuma suka fifita wani a kanmu to lalle su sun tabe daga kan tafarki.” Alkafi: 192. [15]- Kazalika ya zo daga Imam (A.S.) cewa “Mu mu ne taskokin ilimin Allah, kumu ma ne masu fassarar wahayin Allah, ku mu mu ne hujjarAllah cikakkiya a kan wadanda ke koma bayan sama, da wanda ke doron kasa.” Alkafi: Juzu’i na 1 shafi na 192. Kazalika Ya z0 daga Imam Sadik (A.S.) cewa: “Mu mu ne Shugabanni a kan alamuran Allah, kuma taskar ilimin Allah kuma ma’ajiyar wahayin Allah” Al- Kafi Juzu’i 1 shafi na 192. [16]- A duba Sahifatul Imam- Ridha (A.S.) shafi na 47 hadisina 67, da kuma Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu’i na 2 shafi na 27 hadisi na 14, da Ilalis Sharai’i Shafi na 123 Hadisi na 1 da Kamaluddin Juzu’i na 1 shafi na 205 hadisi na 19 da Fadha’ilu Ahmad: Shafi na 189 Hadisi na 267 da Mu’ujamul Kabir na Tabarani Juzu’i na 7 shafi na 25 Hadisi na 6260 , Matalibul Aliya Juzu’i na 4 shafi na 74 Hadisi na 4002, da Ihya’ul Mayyit Bi Fadha’ili Ahlul Bait na Suyuti Shafi na 42 hadisi na 21, da Zakha’irul Ukba shafi na 17, Fara’idus Sumtin Juzu’i na 2 shafi na 241 hadisi na 515, da Kanzul Ummal Juzu’i na 12 shafi na 101 Hadisi na 34188, da Mustadrak na Hakim Juzu’i na 3 shafi na 149, da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 9 hadisi na 174, da Sawa’ikul Muhrika shafi na 234. [17]- Malaman tafsiri sun yi ittifaki kuma an ruwaito daga Imaman Ahlul Bait (A.S.) da kuma sahabbai da dama cewa fadar Allah Ta’ala: “Abin sani kawai shi ne cewa Allah Yana nufin kawai Ya tafiyar muku da datti ne Ya ku Mutanen gida kuma Ya tsarkake ku sosai.” Surar Ahzab: 33. [18]- Cewa wannan ayar ta sauka ne game da Manzon Allah (S.A.W.A.) da Aliyu (A.S.) da Fatima (A.S.) da Hasan (A.S.) da Husain (A.S.) kuma wannan shi ne abinda marubucin Littafin Ya yi ishara da shi. Domin karin bayani a duba: Nahjul Hakk shafi na 173, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu’i na 2 shafi na 10 Hadisi na 192, da Durrul Mansur Juzu’i na 5 shafi na 198, da Mushki Lil Asar Juzu’i na 1 shafi na 332, da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 9 shafi na 121; da Musnad Ahmad Bin Hanbal Juzu’i na 1 shafi na 330 da Juzu’i na 4 shafi na 107 da Juzu’i na 6 shafi na 292, da Sawa’ikul Muhrika shafi 85, da Tafsirut Tabari Juzu’i na 22 shafi na 5 da Usudul Ghabati Juzu’i na 4 shafi na 29, da Khasa’isun Nisa’i Shafi na 4, da AlGadir Juzu’i na 1 shafi na 49 da Juzu’i na 3 shafi na 195 da Juzu’i na 5 shafi na 416 da Ihkakul Hakk Juzu’i na 2 Shafi na 501-553 da kuma Juzu’i na 5 shafi na 54, 55, 58 da kuma Juzu’i na 9/69-1 da Juzu’i na 18 shafi na 359-383, da Dala’ius Sidki Juzu’i na 2 sahfi na 103, da sahih Muslim Juzu’i na 4 shafi na 1883, Sunan Tirmizi Juzu’i na 5 shafi na 351, da Tafsirin Ibin Kathir Juzu’i na 3 shafi na 493. [19]- Tunda yake Manzon Allah (S.A.W.A.) game da Aliyu bin Abi Talib (A.S.) a hadisin Gadir “Ya Allah so wanda ya ka so shi, Ka ki wanda ya yi kiyayya da shi da tozartu wanda ya tozarta shi ka sanya gaskiya ta juya tare da shi duk inda ya juya.” Bayani game da haka zai zo a sashen bayanin Abinda muka yi imani da shi cewa Imamanci da nassi ne. [20]- Saboda cewa Imami sanarwa ne daga Manzon Allah (S.A.W.A.) kuma da yake Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fada da nassi cewa: “Duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa.” Wannan yana nufin cewa da’ar ga Imam da’a ce ga Manzo (S.A.W.A.) kuma yin watsi da hukuncinsa tamkar watsi da hukuncin manzo ne, Allah Ta’ala Ya ce: “Duk wanda ya bi manzon Allah to ya bi Allah ne.” Surar Nisa’i: 80. [21]- Ya zo daga Abi Hamza cewa daga Imam Sajjad (A.S.) cewa: “Aliyu Binul Husain (A.S.) ya ce mana: Wane guri ne mafifici? Sai muka ce Allah da ManzonSa da dan ManzonSa su ne suka fi sani, sai ya ce mana guri mafifici shi ne tsakanin Makama Ibrahim (A.S.) da Rukun, kuma koda mutum zai yi tsawon rai irin na Annabi Nuhu (A.S.) wato shekaru dubu ba hamsin - yana azumtar yininsu yana kuma tsayuwar kiyamullailin dararensu a wannan gurin sa’an nan ya je ga Allah ba ya da biyayya ga shugabancinmu to wannan ba zai amfana masa kome ba.” Man Lâ Yahdhuruhu Fakih Juzu’i na 2 shafi na 159 hadisi na 17, da Ikabul A’amal shafi na 243 hadisi na 2, da Amâli Na Tusi shafi na 132 Hadisi na 209, Wasa’ilus Shi’a Juzu’i na 1 shafi na 122 hadisi 308 da baki dayan hadisan Babi na 29 da Babobin mukaddamar Al-Ibadat a Wasa’il Juzu’i na 1. Al- Hakimul Haskani ya kawo hadisin da ke biye a Littafin Shawahidut Tanzil Juzu’i na 2 shafi na 141 daga Abi Amamal Bahili cewa: “Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce: Allah Ya halitta Annabawa daga bishiyoyi dabam-daban, ni da Aliyu kuma an halitta mu daga bishiya guda, ni ni ne tushenta Aliyu kuma reshenta Hasan da Husain kuwa ’ya’yanta, Shi’awanmu kuma ganyayenta duk wanda ya makale wa wani reshe daga rassanta ya tsira wanda kuwa ya kauce to ya halaka, kuma idan da Bawau Allah zai yi bauta a tsakanin Safa da Marwa shekaru dubu har ya zamanto kamar tsohon kirgi da fatarsa ta tattara amma bai samu sao yayyarmu ba Allah zai kifa shi a kan fuskarsa ranar Alkiyam, Sa’an nan sai Manzo (S.A.W.A.) ya karanta wannan aya “ka ce ni ba na rokon ku wani lada kansa sai dai soyayyar dangi makusata”. Surar Shura: 23. [22]- Sunan Tirmizi Juzu’i na 5 shafi na 663 Hadisi na 3788 da Musnad Ahmad Juzu’i 3 shafi na 14 da 17 da 26, Juzu’i na 5 shafi na 182 da shafi na 189, da Sunanud Dari mi Juzu’i na 2 shafi na 431 da Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu’i na 11 shafi na 452 hadisi na 11725, da Sunan Ibin Abil Asim Juzu’i na 2 shafi na 336 hadisi na 754, da 628,m 630, 1548, 1549, 1553, 1555, da Tabakat na Ibin Sa’ad Juzu’i na 2 shafi na 194 da Mushkilul Asar Juzu’i na 4 shafi na 368, da Mustadrikul Hakim Juzu’i na 3 shafi na 109 da 148 da Hillayatul Awliya’i Juzu’i na 1 shafi na 355 da Mu’ujamul Kabir na Tabarani Juzu’i na 5 shafi na 153-154 hadisi na 4921-4923 da hadisi na 169-170, 4980-4982, Mu’ujamul Sagir Juzu’i na 1 131, da Almunakib na Ibin Magazili 234-235 hadisi 281-283, da Masabihus Sunna Juzu’i na 4 shafi na 190 hadisi na 4816 da Jami’ul Usul Juzu’i na 1 shafi na 278 da Usudul Gaba Juzu’i na 2 shafi na 12 da Zakha’irul shafi na 16 da Ihya’il Mayyit bi Fadli Ahlil Baiti (A.S.) na Suyuti shafi na 30-32 hadisi na 6-8 da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 1 shafi na 170 da kuma Juzu’i na 9 162, da Kanzul Ummal Juzu’i na 1 shafi na 172-173 hadisi na 870-873 da 875, 876, da 185-186 hadisi na 952-953 da Sahih Muslim Juzu’i na 4 shafi na 1873 hadisi na 36 da 37, Tafsirur Razi Juzu’i na 8 shafi na 163 da Tafsirin Ibin Kasir Juzu’i na 4 shafi na 122. [23]- Ya zo daga Ibin Abbas cewa Ya ce: Yayin da “ka ce ni ba na rokon ku kome na lada a kansa sai dai soyayya ga dangi na kusa kawai.” Ta sauka, sun ce: Ya Manzon Allah su wane ne danginka na kusa wadanda soyayyarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: “Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini.” Domin karin bayani a duba Durrul Mansur Juzu’i na 6 shafi na 7, da Tafsirin Tabari Juzu’i na 25 shafi na 14 da Mustadrakul Hakim Juzu’i na 2 shafi na 444 da Musnad Ahmad: 199 da Yanabi’ul Muwadda: 15, da Sawa’ikul Muhrika shafi na 11 da na 102, da Zakha’irul Akba: 25 da sauransu. [24]- Fadha’ilu Ahmad shafi na 176 hadisi na 248, da zakha’irul Akaba shafi na 18 da Kunuzul Haka’ik na Mannawi shafi na 135 da Ihya’ul Mayyit bi Fadhli Ahlil Bait Alaihimus Salam, shafi na 35 hadisi na 13 da Musnad Ahmad Juzu’i na 1 shafi na 84, 95, 128 da Sahih Muslim Juzu’i na 1 shafi na 86 hadisi na 131, da Tajuj Jami’u Lil Usul Juzu’i na 3 shafi na 335, da sunan Tirmizi Juzu’i na 2 shafi na 301, da Sunan Nisa’i Juzu’i na 8 shafi na 117, da Sawaikul Muhrika shafi na 263 da Al- Mahasin Juzu’i na 1 shafi na 176 hadisi na 274, da Amali Saduk shafi na 384. [25]- Amali Saduk shafi na 384 hadisi na 16 da Kanzul Ummal Juzu’i na 12 shafi na 98 hadisi na 34168da shafi na 12: 103 hadisi 34194, da 12 shafi 116 hadisi na 34286, da Maktalul Husain na Khuwarzami na 1/109 da Zakha’irul Akaba shafi na 18 da Sawa’ikul Muhrika shafi na 263. [26]- Allah Ta’ala Yana cewa: “Ya ku mutane lalle Mu Mun halitta ku daga namiji da mace kuma Muka sanya ku jama’a’i da kabilu don ku san juna lalle mafificinku a gurin Allah shi ne mafificinku a takawa. Lalle Allah Mai ilimi ne masani.” Surar Hujurat: 13. [27]- ’Yan Gullatu, masu wuce iyaka, suna wadanda suke imani da abinda ba daidai ba ba gaskiya ba game da Imamai (A.S.) suna cewa su Imamai Iyayengiji ne kuma su ba halittattu ba ne da dai sauransu na daga batattun akidu. Su ’Yan Gullatu sun kasu kashi dabam-daban kamar haka: · Garabiyawa: Su ne wadanda suke cewa Allah Ta’ala Ya aiko Jibrilu da sako zuwa ga Aliyu bin Abi Talib (A.S.) sai ya kuskure ya ba wa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) saboda tsananin kama da juna da suka yi. · Ulya’iyawa: Su ne mabiya Ulya’i bin Dira’id Dausi ko kuma Asadi, su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne da kuma cewa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) bawan Aliyu bin Abi Talib (A.S.) ne -wa iyaza billahi! · Khamsiyyawa: Su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne kuma Salmanu Farisa da Abu Zar da Mikdada bin Aswad da Ammar Yasir, da Amru Bin Umayyatad Dhamiri su Annabawa ne da ubangiji Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya wakilta su su gyara duniya baki daya. Bazi’iyawa: Su ne mabiya Bazi’i Bin Musa Al- Ha’ik wadanda suke cewa shi Annabi Ma’aiki ne kuma Imam Sadik (A.S.) shi ne ya aiko shi. Imam Sadik (A.S.) ya ji Labarin sa kuma ya La’ance shi a sarari. · Saba’iyawa: Su ne mabiya Abdullahi Bin Saba wanda malaman tarihi ke da sabani game da shi kan cewa shi hakika mutum ne da aka yi shi ya rayu da gaske a tarihi ko kuma dai wani tatsuniya ne kawai da makiyan Shi’a suka kago shi, mabiyansa su ma sun yi Imani ne da cewa Aliyu Bin Ali Talib (A.S.) Ubangiji ne abin bautawa. · Mugiriyyawa: Su ne mabiya Mugira Bin Sa’idil Ajali wanda ya yi da’awar annabci, kuma ya halalta aram da yawa kuma ya cusa barnace-barnacensa a littafin Shi’a hatta Ya zo a hadisi cewa Imam Sadik (A.S.) ya la’ance shi. · Mansuriyyawa: Su ne mabiya Abi mansur Ajali wanda Imam Bakir (A.S.) ya yi masa ba -ni - ba - kai kuma shi ne wanda ya yi wa kansa da’awar Imamanci kuma Ya yi wa kansa da’awar Imamanci kuma ya ce Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) Shi ne ballin tarsashin da ke fadowa daga sama kuma sakon manzonci da ba ya karewa har abada. · Khaddabiyawa: Su ne mabiya Abil Khaddab Muhammadu bin Abi Zainab Al- Ajda’il Asadi wanda ya yi da’awar cewa shi Annabi ne Manzo, kuma shi yana daga cikin Mala’iku da dai ire-irensu na daga bace-bace. Duk wadannan kungiyoyin bata da makamantansu fandararru Imamai (A.S.) sun nesata kansu daga wata alaka da su kamar yadda ya zo a hadisai da dama, kana kuma sun gargadi Shi’awansu game da su. Alal Misali ya zo daga Imam Sadik (A.S.) yayin da Sadir ya tambaye cewa: “Lalle wasu jama’a suna da’awar cewa ku iyayengiji ne kuma suna karanta mana ayar Alkur’ani game da haka wadda take cewa “kuma Shi ne wannan da yake Ubangiji a sama kuma Ubangiji a kasa” Sai ya ce: “Ya Sadir Jina da ganina da fatata, da namana, da jinina da gashina duk ba su ba wadannan, Allah Ya barranta daga gare su, wadannan ba a kan addinina suke ba kuma ba sa kan addinin iyayena, Wallahi Allah ba zai hada ni da su ba ranar Alkiyama face Yana fushi da su.” Al- Kafi Juzu’i na 1 shafi na 269. Milal Wan Nihal Juzu’i na 1 shafi na 154 Al- Farku Bainal Firak shafi na 238, Firakus Shi’a shafi na 42, Muruji’z Zahab Juzu’i na 3 shafi na220. Mikbasul Hidaya Juzu’i na 2 shafi na 361 Aslus shi’a wa Usuliha shafi na 172, Wasu hadisai da dama kuma sun yi gargadi game da ’Yan gullatu, masu ketare iyaka, daga cikinsu akwai wadanda ke Biharul Anwar Juzu’i na 25 shafi na 265 da dai sauransu. [28]- ’Yan Halluyuna: Su ne wadanda suke cewa “Ruhin Ubangiji” Ya sauka a jikin Imami kuma su kansu dukansu asalinsu ’Yan Gullatu ne, bayani game da su kuma tamkar bayani ne game da ’Yan gullatu. [29]- Mukhtasarul Basar’irud Darajat: 92. [30]- ya riga ya gabata cewa lmami tamkar Annabi ne sai dai cewa Annabi ana yi masa wahwyi lmami kuwa ba a yi masa wahayi. [31]- Al- Musannaf na Ibin Abi Shaiba Juzu’i na 12 sahfi na 67 hadisi na 1214 da 68 hadisi na 12141, da Sunan Ibin Majah Juzu’i na 1 shafi na 43 hadisi na 116, Sunan Tirmizi Juzu’i na 5 shafi na 633 hadisi 3713, da As- Sunna na Ibin Abi Asim shafi na 591 hadisi na 1361, Musnad Ahmad Juzu’i na 118-119 da kuma Juzu’i na 4 shafi 281 da 368 da 370 da 372, da Khasa’is na Nisa’i shafi na 102 hadisi na 88, Ansabul Ashraf na Balaziri Juzu’i na 2 shafi na 156 hadisi na 169, da Kashful Astar na Bazari Juzu’i na 3 shafi na 190-191, da Al Mu’ujamul Kabir na Tabarani Juzu’i na 3 shafi na 21 hadisi na 3052 da kuma Juzu’i na 4 shafi na 173 hadisi na 4053, da Mu’ujamus Sagir Juzu’i na 1 shafi na 1 shafi na 65 da Mustadrakul Hakim Juzu’i 3 shafi na 109 da Akhbaru Isfahan Juzu’i na 1 shafi na 107 da Juzu’i na 2 shafi na 228 da Tarikhu Bagdad Juzu’i na 7 shafi na 377 da Juzu’i na 14 shafi 236, da Al- Manakib na Ibin Magazili shafi na 16-27 hadisi na 23, 26, 27, 29, 33, 37, 38, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu’i na 1 shafi na 157 hadisi na 211, da Tarikhu Dimashk na Ibin Asakir - Tarjamatul Imam Ali (A.S.) Juzu’i na 2 shafi na 38-84, Tazkiratul Khawas shafi na 36, da Usdul Ghaba Juzu’i na 1: 367 da Juzu’i na 4 shafi na 28 da Zakha’irul Akba shafi na 67, da Al- Isaba Juzu’i na 1 shafi na 304, dan karin bayani kuma ana iya duba Littafan- Al- Gadir na Shaikh Amini da littafin Ihkakul Hak, da Abkatul Anwar da Dala’ilus Sidki da sauransu da dama. [32]- Amali Saduk shafi na 523, A’ilamul Wara shafi ne 167, da Ihakak Hak Juzu’i na 4 shafi na 297, Musnad Ahmad Juzu’i na 111 da shafi na 159 , Khasais na Nisa’i shafi na 83 hadisi na 66, da Tarikhut Tabari Juzu’i 19 shafi na 74, da Shawahidut Tanzil Juzu’ina 1 shafi na 420 da Sharhin Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu’i na 3 shafi 267, da Yanabi’ul Muwadda Juzu’i na 1 shafi na 104, Al- Kamil Juzu’i na 2 shafi na 62 da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 8 shafi 302 da sauransu, da ba za su kidayu ba. [33]- Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu’i na 12 sahfi na 60 hadisi na 12125 da shafi na 61 hadisi na 12126, da Tarikhul Kabir na Bukhari Juzu’i na 1 shafi na 115 hadisi na 333 da Juzu’i na 7 shafi na 301 hadisi na 1284, da Sahih Muslim Juzu’i na 4 shafi na 1870 hadisi na 2404, da Sunanut Tirmizi Juzu’i na 5 shafi na 640 hadisi na 3730, Sunan na Ibin Abi Asim: Ya ambata shi da isnadai dabam-daban daga hadisi na 1333-1348, Musnad Ahmad Juzu’i na 1 shafi na 179 da Juzu’i na 3 shafi na 32, da Juzu’i na 6 shafi na 438, Khasa’is na Nisa’i shafi na 68-79 hadisi na 45, 48, 50, 51, 62, 63, 64 da Hilliyatul Awli’ya’u Juzu’i na 4 shafi na 345 da Juzu’i na 7 shafi na 195 da 196 da Tarikhu Isfahan Juzu’i na biyu shafi na 281, 328 da Mu’ujamul Kabir na Tabarani Juzu’i na 1 shafi na 146 hadisi na 328 da 148, 333, 334, da Juzu’i na 2 shafi na 247 hadisi na 2035, da Juzu’i na 4 shafi na 17 hadisi na 3515 da Juzu’i na 11 shafi na 74 hadisi na 11087 da Juzu’i na 24 shafi na 146 hadisi na 384-389, da Mu’ujamus Sagir Juzu’i na 2 shafi na 53,54, Tarikhu Bagdad Juzu’i na 1 shafi na 325 da Juzu’i na 3 shafi na 406, Juzu’i na 8 shafi na 53 da Juzu’i na 9 shafi na 365, da na 10 shafi 43, da Juzu’i na 12 shafi na 323, da Isti’ab Juzu’i na 3 shafi na 34, da Almanakib na Ibin Magazili shafi na 27-36 hadisi na 40-56, Tarikhu Dimashk Tarjamatu Imam Ali (A.S.) Juzu’i na 1 shafi na 306-390, Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 9 shafi na 109 da sauransu. [34]- Tafsiru Furatul Kufi shafi na 40-41, da Amalis Saduk shafi na 107 hadisi na 4, da Tafsirut Tibyan na Tusi Juzu’i na 3 shafi na 559, da Ihtijaj na Tabrisi Juzu’i na 2 sha 489, da Tafsiriut Tabari Juzu’i na 6 shafi na 186, da Asbabun Nuzul na Wahidi shafi na 113 da Al- Munakib na Ibin Magazili shafi na 312 hadisi na 356 da shafi na 313 hadisi na 357, Almanakib na Khawarzimi shafi 264, Tazkiratul Khawas shafi na 24, Tafsiri [35]- Littafin As- Sakifa na wannan marubucin wannan Littafin sashen “An nas ala Aliyu bin Abi Talib (A.S.)” shafi na 59-73 Akwai sharhin wasu ayoyin. [36]- Kari a kan abinda ya zo daga Manzo (S.A.W.A.) game da su biyu domin hadisi ya zo a jejjere da hanyoyi da dama kan cewa ya ce: “Wadannan ’Ya’yan nawa guda biyu Imamai, sun Tashi ko sun zauna” Annaukat shafi na 48, Ilalus Shara’i-i Juzu’i na 1 shafi na 211, Al- Irshad shafi na 220, Kifayatul Asar: 117, da At Tuhaf na Majduddin shafi na 22, da Yanabi’un Nasiha shafi na 237, da ya ce “Babu wata rikitarwa game da kasancewar wannan hadisin daga wanda al’umma ta karbe shi domin Ya kai darajar hadisi mutawatiri, mai hanyoyin ruwa da yawa, don haka ya inganta a kafa dalili da shi.” Game da shi ne ma Ibin Shahar AShubi ya ce a manakib: “Ma’abuta Alkibla sun yi ittifaki a kansa”. [37]- Kamaluddin shafi na 250-256 hadisi na 1-4 da Uyunu Akhbarur Ridha (A.S.) Juzu’i na 1 shafi na 41-51 hadisi na 2-16, da Amalit Tusi Juzu’i na 1 shafi na 291 hadisi na 566/13 da Fara’idus Simtain Juzu’i na 2 shafi na 132 hadisi na 431 da na 136 da na 435 da 313 da 564. Ya zo a ruwayoyi da dama wadanda maruwaitan Ahlus Sunna da dama suka kawo wadanda a cikinsu Annabi (SAWA) Yake cewa: Lalle halifofi bayansa goma shahbiyu ne da kuma cewa lalle dukkaninsu daga kuraishawa suke. Daga cikinsu akwai wanda Jabir bin Samrata ya kawa yayin da ya ce: “Na kasance tare da Mahaifina a gurin Annabi (SAWA) Sai na ji yana cewa: Bayana akwai halifofi goma sha biyu, sa’an nan sai ya yi kasa-kasa da muryarsa daga nan sai na ce wa Babana, mene ne abinda ya yi kasa kasa da muryarsa a kai, ya ce cewa Ya yi dukkaninsu daga Bani Hashim sukc”. Da dai wasun wannan ruwayar da dama. A duba musnad Ahmad Juzu’i na 5 shafi na 89 da 90 da 92, da kuma Mustadrakul Hakim Juzu’i na 4 shafi na 501 da Majma’uz Zawa’id Juzu’i na 5 shafi na 190 da Kanzul Ummal Juzu’i na 6 shafi na 201 da 206 da kuma Sahih Bukhari Juzu’i na 9 shafi na 101 da Sahih Muslim Juzu’i na 2 shafi na 192 da Tarikhul Khulafa’i shafi na 10 da Sunan Tirmizi Juzu’i na 2 shafi na 35 da Yanabi’ul Muwadda shafi na 444 da sauransu da dama. [38]- Al- Gaibatu na Tusi shafi na 148 da 187, da Umdatu na lbinil Batrik shafi na 433 hadisi na 909 da shafi na 436, hadisi na 920, da Isbatul Hudat Juzu’i na 3 shafi na 504 hadisi na 303-304 da Sunan Abi Dawud Juzu’i na 4 shafi na 107 hadisi na 4284, da Sunan Ibin Majah Juzu’i na 2 shafi na 1368 hadisi na 4086 da dukan hadisan Al- Babul 34 Kitabul Fitan, da mustadrakul Hakim Juzu’i na 4 shafi na 557, Al- Mu’ujamul Kabir na Tabarani Juzu’i na 23 shafi 267 hadisi na 566, da Kifayatut Talib shafi na 486, da Kanzul Ummal Juzu’i na 14 shafi na 264 hadisi na 38662, Sunan Tirmizi Juzu’i na 4 shafi na 505, Al-Bayan fi Akhbari Sahibuz Zaman shafi na 479, Al- Hawi na Fatawi Juzu’i na 2 shafi, Al- Burhan Fi Alâmâtul Mahdi (A.S.) shafi na 94. [39]- La’alla daga cikin masu rikitarwar Dokta Rundasan wanda yake cewa: “Lalle mai yiwuwa ne kwarai cewa rashin cin nasarar hukumar Ummayyawa na zahiri wajen kasa kafa rukunan adalci da daidaito a zamaninsu shekara ta 41-132 na daga cikin abubuwan da suka sabbaba akidar Mahadi a karshen zamani.” Littafin Akidar Shi’a shafi na 231. [40]- Kisaniyawa: Jama’a ce da suka yi ittifaki a kan Imamancin Muhammad Bin Hanafiyya. Wasunsu sun ce lalle Muhammad Bin Hanafiyya shi ne Imami bayan Mahaifinsa Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) domin Imam Ali (A.S.) Ya ba shi tuta ranar Yakin Jamal inda Ya ce da shi: Soke su suka irin na Mahaifinka a Yabe ka, Babu alheri a yaki matukar ba ka gwabza ba. Wasunsu kuma sun ce: Lalle Imami bayan Imam Ali (A.S.) shi ne Imam Hasan (A.S.) sai Husain (A.S.) sa’an nan kuma sai shi ya zamanto Imami bayan Imam Husain (A.S.) ya fita daga Madina zuwa makka katin awkuwar al’amarin karbala. Wasunsu suna ra’ya cewa shi Muhammad Bin Hanafiyya yana raye bai mutu ba kuma wai Shi ne mahadi da ake saurare, wannan su ne wadanda Marubucin wanmam littafin ya yi ishara game da su a nan. Wasunsu kuma sun tafi a kan cewa ya rasu kuma Imami bayansa shi ne Imam Aliyu Binul Husain Zainul Abidin (A.S.). Daga cikinsu kuma akwai masu cewa: Imamanci bayansa Ya koma ga Abi Hashim Bin Muhammad Ibin Hanafiyya, sa’an nan kuma su kansu sun saba a kan Imamanci bayansa. Wasunsu suka ce ya koma ga Muhammad Bin Ali Bin Abdullah, wasunsu na cewa bayansa Imamanci ya koma ga Bayan Bin sam’an suna kuma raya cewa ruhin Allah Ya kasance a jikin Hashim sa’an nan Ya fita Ya koma jikin shi Bayan. Wa kila ansa musu suna kisiniyawa ne saboda Mukhtar Bin Abi Ubaidus Sakafi Ya kasance shugabansu kuma an kasance ana yi masa Lakabi da “Kisana” domin shugaban dogaransa shi ne (Abu Umrata) kuma sunansa kisana ne kuma Ya zurfafa wajen shi Mutchtar din. Wannan kuwa a bisa asasin cewa akidar Shi’a Imamiyya ita ce mafi daidai a gurinsu kan cewa shi Mukhtar mutum ne Salihi mai akida sahihiya, kuma Ya kasance yana kira ga Imamancin Imam Sajjad (A.S.) Yabo gare shi kuwa Ya zo a harshen Imam Sajjad (A.S.), da Imam Bakir (A.S.) da Imam Sadik (A.S.) kamar kuma yadda yabo gare shi da kuma rashin Zargi a kansa Ya zo daga Malaman Shi’a kuma babu wanda ya zar ge masa illa kalilan daga cikinsu. Abin kuma da ake jifan sa da shi duk kazafi ne da makiya domin su bata shi domin shi ne ya yunkura don ramuwar gayya da daukar fansa ga Imam Husain (A.S.) ya kuma kashe wadanda suka kashe shi da zuriyar gidansa, a Karbala. Malamar Shi’a Imamiyya da dama sun yi rubuce-rubuce game da rayuwar shi Mukhtar da ayyukansa. A duba Al-Milal wan Nihal Juzu’i na daya shafi na 131, Al- Farku bainal Firak shafi na 38 da Firakus Shi’a shafi na 23. [41]- Domin tabbatar maganar Allah Ta’ala da ke cewai: “Shi ne wanda ya aiko Mazonsa da shiriya da addinin gaskiya don Ya tabbatar da shi a kan dukan adddinai baki daya.” Surar Tauba: 33, Fathi: 28, saf: 9. Domin ya zo a ruwayoyi da hadisai da dama daga Annabi (SAWA) da kuma daga Imamai (A.S.) game da bayyanar Mahadi (A.S.) daga ’ya’yan Fatima (A.S.), kuma cewa zai cika kasa da daidaito da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai kamar yadda ya riga ya gabata. Sidi Shahid Sadr ya ambata nassi kamar haka: “Akidar Mahadi a matsayinsa na shugaba da ake jira domin canja duniya zuwa ga mafi dacewa, hadisai da dama daga Annabi (SAWA) baki daya da kuma daga Imamai (A.S.) a kebe, kuma sun yi ta’akidi a nassosi masu yawa ta yadda ba zai yiwu a yi shakku a kansu ba, an kidaya hadisai dari hudu daga Annabi (SAWA) daga bangaren ’Yan’uwanmu Ahlus Sunna, kamar kuma yaddo aka kididdige hadisai dangane da Imam Mahadi (A.S.) daga bangaren Shi’a da Sunna inda adadinsu ya kai sama da dubu shida Wannan adadi ne mai yawan gaske wanda babu kamarsa a cikin suran al’amuran musulunci bayyanannu, wadanda a bisa dabi’a musulmi ba ya shakka a kansu.” Al- Bahas haulal Mahadi shafi na 63. [42]- Saboda abinda Ya gabata cewa kasa ba ta zama ta tsiraita daga hujja. [43]- Ya zo a ruwayoyi cewa Imam Askari (A.S.) ya yi wafati a shekarar 260 a lokacin kama shekarar Imam Mahadi (A.S.) shekara biyar kuma ya dauki nauyin Imamanci. Ruwayar Abil Adyan wanda ya kasance yana yi wa Imam Askari (A.s) hidima yayin da Imam din (A.S.) Ya aike shi ya kai wasu Littafa zuwa wasu birane lokacin da yake rashin lafiya, ya ce masa, Lalle za ka boyu kwana goma sha biyar kuma ranar kwana na goma sha biyar din za ka shiga garin Samurra ka ji ka kiyaye. Sai Abul Adyan Ya tambaye shi game da Imamin bayansa sai Ya ce masa shi ne wanda zai neme ka da amsoshina kuma ya yi mini salla kuma zai ba ka labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da kai. Wannan kuwa duk abinda Imam ya fade haka ya auku. Abul Adyan Ya dawo wanda ya nemi amsoshin shi ne Imam Mahadi (A.S.) kuma shi ne Ya yi wa mahaifinsa salla bayan ya sallami baffansa sa’an nan kuma ya ba wa Abul Adyan labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da shi, kamar kuma yadda ya bawa mutane da dama labarin wasu al’amura da babu wanda ya san da su sai su kansu, a wannan lokacin shekararsa biyar, A duba Kamaluddin wa Tamamun Ni’ima Juzu’i na 2 shafi na 476, da Biharul Anwar Juzu’i na 50 shafi na 332 hadisi na 4 da Tarikhu Ghaibatus Sugra shafi na 282 da abinda Ya biyo baya. [44]- Domin Yana cewa: “Kuma lalle hakika Mun aiki Nuhu ga mutanenSa Ya kasance a cikinsu shekara dubu ba hamsin sai ambaliyar ruwa ta kama su alhali su suna azzalumai.” Surar Ankabutu: 14. Kuma tabbatacce ne cewa wannan gwargwadon shekarun lokacin Zamansa a cikin mutanensa ne kawai amma shekarunsa duka-duka an ce akalla dubu da dari shida ne an ce ma ta fi hak. Tafsirul Kasshaf Juzu’i na 3 shafi na 200 Tafsirul Ibin Kasir Juzu’i na 3 sha na 418, da Zadul Masir na Ibinul Jauzi Juzu’i na 6 shafi na 261. [45]- “Da fadarsu; Lalle ne mun kashe Al-Masihu Isa dan Maryama Mazon Allah”, alhali kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su tsire shi ba sai dai an kamanta shi gare su ne. Lalle ne wadanda suka saba wa juna a kan sha’aninsa suna shakka game da shi, ba su da wani ilimi face bin zato kuma ba su kashe shi ba a hakika. Sai dai Allah ya dauke shi ne zuwa gare shi, kuma Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikimi” Surar Nisa’i: 157-158. [46]- Jami’ul Ahadis na Kummi shafi na 21 da Jami’ul Akhbar Shafi na 337 hadisi na 919, Sahih Bukhari Juzu’i na 2 shafi na 6 da Juzu’i na 3 shafi na 196, Musnad Ahmad Juzu’i na shafi na 5 Sunan Baihaki Juzu’i na 6 shafi na 287. [47]- Sahihul Bukhari Juzu’i 2 shafi 68, Sahih Muslim Juzu’i 1 shafi na 399 hadisi na 85, 86, 87, 89, Tirmizi Juzu’i na 2 shafi 235 hadisi 391-395, Sunan Abi Dawud Juzu’i 1 shafina 264 hadisi na 1008-1023. [48]- Sharhul Makasid Juzu’i na 4 shafi na 143-146 A cikinsa akwai ishara ga maganar ’Yan Hambaliyya da Hashawiyawa game da wanzuwar Alkur’ani har ma da magarnar wasunsu kan cewa bangonsa da jakarsa ma azali suke, akwai kuma ishara ga muhawarar Abu Hanifa da Abu Yusuf da ta dauki tsawan wata shida inda ta kare da cim ma ittifaki a tsakaninsu kan cewa Alkur’ani wanza zze ne duk wani batu sabanin haka kuwa kafirci ne. [49]- Sharhul Makasid Juzu’i na 5 shafi 125 da Mazahibul Islamiyyin: 62. [50]- Fajrul Islam shafi na 33 kan cewa Ahmad Amin bai takaita ba a wannan a kan wannan magana ta sa, sai dai ya yi karin gishiri mai yawa da maganganu marasa madogara ba su kuma da asasi, A duba Littafin Aslus Shi’a wa Usuliha shafi na 140 don karin bayani A cikin an kawo wannan maganar da kuma takaitaccen martani game da ita. [51]- Ishara ga maganar Allah Ta’ala Yana mai Shaidawa Manzonsa Muhammadu (SAWA) cewa “Ya saukar da littafi a gare ka da gaskiya Yana mai gaskata abinda ya gabace shi kuma Ya saukar da Attaura da Linjila” Ali Imran: 3. Da kuma da dama makamantanta da ke nuna cewa Manzon Allah (SAWA) da Alkur’ani sun 30 suna masu gaskata Annabawa da shari’o’i da suka gabata. [52]- Al- Kafi Juzu’i na 2 shafi na 174 hadisi na 12, Mukhtasarul Basa’irud Darajat shafi na 101 da Almahasin Juzu’i na 1 shafi na 397 hadisi na 890. [53]- Al- Kafi Juzu’i na 2 shafi na 172 hadisi na2, da kuma Al Fikhul Mansub ilal Imam Ridha (A.S.) shafi 338. [54]- Takiyya ita ce boye gaskiya da suturce imani da ita, da boye wa wadanda ake da sabani da su, da rashin fitowa sarari gare su da abinda zai jawo cutarwa a addini ko a (abin) duniya. Kuma tana daga cikin abubuwan da wasu ke kin Shi’a saboda ita, domin jahiltar ma’anarta da suka yi da kuma guraren da ta dace da su, da hakikaninta, idan da sun tsaya daidai sun dakanta sun yi hakuri sun hakarkur-kurtar da sun san cewa takiyya ba wai ta takaita kawai ga Shi’a ba ne kuma ba su kebantu da ita su kadai ba, sai dai ita aba ce La budda sai da ita a bisa hukuncin hankali kuma a kanta dabi’un dan Adam suka tattara, hankali kuma shi Mai mata ja-gora ne ilimi kuma shi ne mai kula da ita kuma ba’a taba rabuwa da su biyun koda gwargwadon kiftawar ido, domin kowane mutum dabi’arsa ne ya kare kansa ya kiyaye rayuwarsa. Sahihul I’itikad daga Musannafatu Shaikh Mufid Juzu’i na 5 shafi na 137, Aslus Shi’a wa Usuliha shafi na 315, Waki’ut Takiyya indal Mazahib wal Firakil Islamiyya wadanda ba Shi’a Imamiyya ba, na Sayyid Samir Amidi, a ciki akwai bayani game da takiyya da kuma cewa batu game da ita bai kebanta ga Shi’a Imamiyya ba kawai. [55]- As- Shi’atu wal Hakimun, Shaikh Muhammad Jawad Mugniya. [56]- Domin Ya zo daga Imam Bakir (A.S.): “An sanya takiyya ne domin a kare jini da ita idan kuwa har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce.” Wasa’ilus Shi’a Juzu’i na 11 sha 483 hadisi na 1. [57]- Domin hadisi ya zo daga Imam Ridha (A.S.) “Don an sanya takiyya don kare jini ne kawai idan har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce.” [58]- Ta’alikin kausari a littafin Isfirayini, Attabsira fida din shafi na 185. Da kuma Nash’atul Ash’ariyya wa Tatawwuriha shafi na 87-88.
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||