GABATARWA


 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Shekaru goma ke nan suka gushe da buga wannan littafi, a duk cikin wadannan shekaru ban sami wani abu da ke iza ni in canja ra’ayina a kansa ba game da cewa Ya dace da bukatun musulmi baki daya game bayyanar da akidojin Shi’a Imamiya (masu bin Imamai sha biyu daga zuriyar Manzo (S.A.W.A.)).

Sai dai ma na sake samun karfin gwiwa a kan sake jaddada yada Shi, tare da fatan Ya zamanto Ya cimma manufa kuma Ya biya bukatar kokarin gusar da lullubin giragizan da suka shamakance tsakanin manyan bangarorin musulmi guda biyu masu girma na tsawon lokaci; wato Ahlus Sunna da Shi’a, da kuma kokarin karkade kurar da tsohon tarihi dadadde Ya bari a kan akidojin musulunci ingatattu.

Ni ina da tabbacin cewa ra’ayin “kusato da mazhabobi” a yau Ya zama wata bukata matsananciya, kuma manufa mai daukaka ga dukan wani musulmi mai kishin musulunci, koda mene ne kuwa sabanin mazhabarsa da ra’ayinsa a bambance-bambancen akida kuma babu abinda Ya fi a wannan ra’ayin kusatowar fiye da cewa kowane mai akida Ya dauki nauyin tono bisonta da hakikaninta.

Wannan hanya -a ganina- ita ce mafi aminci wajen ba da ingantaccen tunani game da mazhabar, kuma har wa yau ita ce hanya mafi kusaci ga fahintar daidai daga ra’ayin da jama’arta suke rike da shi.

Saboda in amsa bukatar “Sanyin idona” mai aiki a tafarkin Allah mai daraja Sidi Murtadha Kashmir, na sake duba wannan littafi, na kuma kara shigar da wasu gyare-gyare da kare-karen da kurarren lokaci Ya ba da damar yi, tare kuma da guara kurakuren da suka auku wajen bugawa da ma wadanda ba na bugawa ba, domin in sake gabatar da shi ga Madaba’a, ina mai fatan Allah Ya tabbatar da cim ma manurfar da ake so, sa’an nan kuma Ya ba mu dacewar rungumar tafarki madaidaici da bin gaskiya, lalle Shi Shi ne mafi alherin wadanda ake roko.

 

Mawallafi

21, Shawwal 1380 Hijiryya

1960 Miladiyya


 

 

GABATARWA

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai

 

Yabo da godiya su tabbata ga Allah,

Tsira da aminci su tabbata ga Muhammadu

Mafificin ‘yan Adam da zuriyarsa shiryayyu.

Na yi shiftar wannan littafi ne kuma babu wata manufa tare da shi illa rubuce takaitacce abinda na kai gare shi na fahintar akidojin musulunci a bisa tafarkin Ahlul Baiti (Zuriyar Gidan Manzo (S.A.W.A.)) aminci Ya tabbata gare su.

An dai rubuce wannan takaitaccen littafin ne ba tare da kawo nassosin da yawanci suka iso daga Ahlul-Baiti game da su ba, domin sabon kamu da kuma mai koyo da kuma malami su amfana da shi, na sanya masa suna “Akidojin Shi’a”[1] abinda nake nufi kuwa shi ne “Shi’a Imamiya Isna Ashariya”a kebe.

Shiftar wannan littafi an yi ta ne a shekarar 1363 Hijiriya, kuma an yi ta ne da nufin ba da ita a matsayin laccar da ake yi a ayyane lokacin koyarwa da kwalejin “Muntadan Nashrid Diniya”[2] don amfani da ita wajen share fagen dogon bincike game da akida daga bisani.

A wancan lokacin na ci nasarar gabatar da dama daga cikinta a laccoci kuma sam ban kasance na shirya su domin a wallafa a yada a kuma karanta ba, don haka na zamanto na jinkirtar da dama daga cikin takardun laccoci masu muhimmanci da kuma darrusan da na ba da shiftarsu a cikin wancan halin, musamman ma dangane da abinda Ya shafi Akida da ilimin abbatar da samuwar Allah.

Sai dai kuma a wannan shekarar - bayan wucewar shekaru takwas babban malami mai alfarma malam Muhammadu Kazim Al-Kutbi[3] Allah Ya kiyaye shi Ya kwadaitar da ni wajen sake tunani a kansu, da kuma taro su a maida su rubutacce n littafi takaitacce mai isar da dukan bangarori da nufin yada su domin amfana baki daya, domin kuma a kore da dama daga cikin soke - soke da aka lika wa Shi’a Imamiyya, musamman ma da yake wasu marubutan wannan zamani a kasar Masar da sauransu ba su gushe ba suna ta dira a kan Shi’a da alkalumansu suna soke - soken rashin adalci a kan mazhabar Shi’a da akidojinta domin jahilci ko kuma kin sani da gangan game da tafarkin Zuriyar Jidan Manzon Allah (S.AW.A.) a tafar kunansu na addini kuma da haka ne duk suka hadu a kan zaluntar gaskiya da yada jahilci a tsakanin masu karanta littafansu suna masu kira zuwa rarraba kalmar musulmi, da haifar da husuma da kufe a zukatansu, kai har ma da cuna wasunsu a kan wasunsu… Kuma babu masani da a yau zai jahilci gwargwadon bukatar kusato da jama’ar musulmi ga junansu da binne kullace - kullacensu idan har ba mu iya mun zamar da su sahu daya baki daya a karkashin tuta guda ba.

Ina fadan haka alhali kuma ina mai jin cewa - abin ban takaici - ba za mu iya yin kome game da irin wadannan miyagun soke-soken tare da wadanda muka jarraba daga cikin irin wadannan marubutn ba kamarsu Dokta Ahmad Amin marubucin littafin Fajrul Islam da makamancinsa masu Kira zuwa ga rarraba, su bayanin akidojin Shi’a Imamiya bai kara musu kome ba illa tsaurin kai, kuma fadakar da su kura-kurensu bai kare da kome ba sai jayayya.

Kuma bai dame ba kan cewa su wadannan da ma wadanda ba su ba don sun ci gaba da tsaurin kan su sun dage a kai ba don gudun kada wadanda ba su sani ba su yarda da su wannan dibilbilewar ta baibaye su kuma soke-soke su kwashe su su tsiro musu da Kufe da kunci.

Kuma koda ma mene ne wannan al’amarin , ni dai ina mai kaddamar da wanna littafin ne da fatan cewa a cikinsa za a sami abinda zai amfani mai neman gaskiya, don in zamanto ni ma na ba da gudummawa mai amfani ga musulunci, kai hidima ma ga ‘ yan Adamtaka baki daya, na tsara shi a kan gabatarwa da kuma Fasali-Fasali; kuma daga Madaukaki Shi Kadai nake neman gamon katar.

 

Muhammad Ridha Al- Muzaffar

Najaf - Iraki

27 ga watan Jumada Akhir 1370

Miladiyya 1950

 

1- Imaninmu Game Da Sani Da Kuma Neman Ilimi

Mun yi imanin cewa da yake Allah Ya Yi mana baiwar karfin tunani kuma Ya ba mu hankali to Ya umarce mu ne da mu yi nazari da tuntuntuni a kan alamun ayyukansa mu yi tunani a kan hikimarSa da kuma kyautata lura a ayoyinSa a kan duniya baki daya da kuma a kan kanmu, Allah Ta’ala Yana cewa:

“Za mu nuna musu ayoyin Muasassa da kuma a kawukansu, har Ya bayyana gare su cewa Shi lalle gaskiya ne…” (Surar Fussilat: 53)

Kuma Ya zargi masu bin iyaye ba tambaya da cewa:

“Suka ce mu dai kawai za mu bi abinda muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba sa hankalta ne kuma ba sa shiryuwa.” (Surar Bakara: 170)

Kamar kuma yadda Ya aibata masu bin zato kawai da dikake a cikin duhu da cewa:

“Baba ubinda suke bi sai zato kawai.” (Surar An’am: 116)

Alal hakika mu abinda muka yi imani da Shi Shi ne cewa: Lalle hankulanmu su ne suka wajabta mana yin tuntuntui kan halittu kamar yadda suka wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar duk wani da Ya yi da’awar cewa shi Annabi ne da mu,uijzarsa. Kuma a gurin hankali bai dace ba a yi koyi da wani ba a cikin wadannan al’amuran kome matsayinsa da darajarsa kuwa.

Abinda Ya zo a cikin Alkur’ani na kwadaitarwa a kan tuntuntuni da bin ilimi da sani Ya zo ne kawai don kara tabbatar da wannan ‘yancin na dabi’ar halitta a hankali da suka dace da ra’ayoyin ma’abuta hankali, Ya kuma zo ne don fuskantarwa zuwa ga abinda dabi’ar hankula ta hakunta.[4]

Bai dace ba a cikin irin wannan hali mutumya yi wa kansa saki na dafe a kan al’amarin akida, ko kuma ya kare da dogaro a kan wadanda suka masa tarbiyya, ko kuma wasu mutane daban, lalle ma ya wajaba ne a kansa daidai yadda yake a dabi’ar karfafa kan ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi kididdiga a kan jiga-jigan akidarsa[5] wadanda ake kira jiga-jigan addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi, wato kadaita Allah, da Annabci da Imamanci da kuma Tashin kiyama.

Duk wanda Ya yi koyi da iyaye haka siddan ko kuma makamantansu a imani da wadannan jiga-jigan ta lalle ya ketare iyaka Ya fandare daga hanya madaidaiciya kuma ba zai taba zama an yafe masa ba har abada. A takaice dai mu muna da’awar abubuwa biyu ne:

Na Farko: Wajabcin bincike da kuma neman sani a kan jiga-jigan akida bai halatta a koyi da wani ba a kansu.

Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin Ya zamanto na shari’a wato saninsa ba wai Ya samo asali daga nassosin addini ba ne koda yake Ya inganta su karfafa shi bayan hankali Ya tabbatar da shi.

Kuma Ma’anar wajabcin hankali babu abinda take nufi illa fahintar neman sani da hankali Ya yi da kuma lizimtar yin tuntuntuni da kokari a jiga-jigan akida.

 

2- Imaninmu Game da Koyi da Wani a Rassan Al’amuran Addini

Rassan al’amuran addini su ne hukunce hukuncen shari’a wadanda suka shafi ayyuka, su ba wajibi hukunce-hukuncenba ne a yi bincike da ijtihadi a kansu sai dai ma idan ba su kasance daga cikin muhimman al’amura wadanda suka tabbata da ingantattun hujjoji kamarsu wajabcin salla da zakka da azumi ba to dayan uku ne Ya wajaba:

Ko Ya yi ijtihadi Ya yi bincike a kan dalilan hukunce - hukunce idan yana daga cikin masu iya yin hakan.[6]

Ko kuma ya zama mai ihtiyadi, idan yin ihtiyadi zai wadatar da shi.[7]

Ko kuma Ya yi koyi da Mujtahidi wanda Ya cika saharruda.[8] Wato Ya zamanto cewa wanda zai yi koyin da shi, mai hankali ne, Adali “mai kiyaye kansa, mai kare addininsa, mai saba wa son ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa”[9]

Duk wanda ba Mujtyahidi ba ne kuma ba mai yin ihtiyadi ba ne kuma bai yi koyi da mujtahidi wanda ya cika sharuda ba to dukan ayyukan ibadarsa batattu ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla ya yi azumi ya yi ta ibada duk tsawon rayuwarwa, sai dai idan aikin sa Ya dace da ra’ayin wanda zai yi koyi da shi daga baya, ya kuma yi gamon katar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah Ta’ala.[10]

 

3- Imaninmu Game da Ijtihadi

Mun yi Imanin cewa: Ijtihadi (matsayin tsamo hukunce-hukunce) a rassan hukunce-hukuncen shari’a wajibi ne da wajabcin kifa’iyya da Ya doru a kan dukan musulmi a zamanin boyuwar Imam[11], wato ma’ana cewa a wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Amma kuma idan har wani da zai iya kuma zai wadatar Ya dauki nauyin yi to Ya fadi daga kan sauran musulman, sai su wadatu da wanda Ya dauki nauyin yin hakan kuma Ya kai ga matsayin ijtihadi kuma Ya zamanto Ya cika sharudan, sai, su yi masa takalidi, su yi koyi da shi, su koma gare shi a kan rassan hukunce-hukuncen addininsu.

Don haka a kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami Mujtahidi a tsakaninsu wanda Ya sadaukar da kansa Ya kai ga matsayin Ijtihadi- wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo-kuma Ya kasance Ya cika sharudan da suka sa Ya cancanci a yi masa takalidi, a yi koyi da shi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen addininsu.

Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to Ya wajaba a kansu kowane daya daga cikinsu Ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya a tsakaninsu wanda zai dukufa domin kaiwa ga wannan mukami domin ba zai yiwu ba dukansu su dukufa domin neman wannan al’amari ko kuma zai yi wahala.

Kuma bai halatta gare su ba su yi koyi da wanda Ya rigaya Ya mutu daga cikin Mujtahidai.[12] Ijtihadi shi ne nazarin dalilan shari’a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari’ar da shugaban Manzanni (S.A.W.A.) Ya zo da ita, kuma ba ta canzawa ba ta sakewa da sakewa zamani da kuma halaye “Halalin Muhammada halal ne har zuwa ranar Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar tashin Kiyama.”[13]

Dalilan shari’a su ne: Alkur’ani mai girma, da sunna, da Ijma’i, da Hankali kamar yadda yaka filla filla a littafin Usulil Fikhi.

Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar tarin ilimi da sani wandanda ba sa samuwa sai ga wanda Ya dage Ya wahala, Ya sallama kansa, Ya ba da kokarinsa wajen samun sa.[14]

 

4- Imaminmu Game da Mujtahidi

Abinda muka yi imani da shi game da Mujtahidi wanda Ya cika sharuda: cewa shi Na’ibin Imam (A.S.) na halin boyuwar shi Imam din.[15] Kuma shi mai hukunci ne,shugaba cikakke, abinda yake ga Imam (A.S.) yana gare shi a fannin al’amura da shugabanci a tsakanin mutane kuma duk wanda Ya ki hukuncinsa tamkar Ya ki hukuncin Imam (A.S.) wanda Ya ki hukuncin Imam (A.S.) kuwa Ya ki hukuncin Allah ne wannan kuwa a matsayin shirka da Allah yake, kamar yadda Ya zo a hadisi daga Sadikun Ahlul Baiti (A.S.).[16]

Shi Mujtahidin da Ya cika sharruda ba wai madogara ne kawai a wajen ba da fatawa ba, a’a har ma yana da ja-goranci na gaba daya,[17] don haka ana komawa gare shi a hukunci da raba gardama da shari’a, wannan duk na daga cikin abubuwan da suka kebantu da shi kuma bai halatta ga wani ba Ya dauki nauyinsu sai shi, sai dai da izininsa, kamar kuma yadda bai halatta ba a yi haddi ko labadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa.[18]

Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebantu da shi.[19]

Wannan matsayin ko kuma shugabanci na gaba daya Imam (A.S.) Ya ba da shi ga Mujtahidi wanda Ya cika sharruda domin ya kasance na’ibinsa wato wakili ko magajinsa a yayin boyuwarsa, wannan shi ne abinda Ya sa ake ce masa “Na’ibin Imam”.

 


[1]- Wannan shi ne sunan da marabucin Littafin ya sanya wa Littafin a bugu na farko.

[2]- Wannan kwalejin makarantar marubucin ce shi kansa kuma daga bisani am canja mata suna zuwa “Kwalejin Fikihu”.

[3]- Shi ne mai Dakin karatu da ake kira Haidariyya - Najaf shi ne farkon wanda ya biya kudinsa aka fara yada wannan littafin.

[4]- Wanan kuwa shi ne daga fadar Allah Ta’ala cewa: “Ka ce ku yi dubi zuwa ga sammai da kasa.” Surar Yunus:101 da

Kuma Fadar Allah Ta’ala: “Shin ba sa duba rakumi yadda aka halitta shi, da kuma sammai yadda aka kakkafa su. Da kuma kasa yadda aka shimfida ta. To ka yi fadakarwa kai dai mai fadakarwa ne kawai.” Surar Gashiya: 17-21.

Da kuma fadar Allah Ta’ala: “Shin su ba sa yin tuntuntuni ne a kan kawukansu” Surar Rum: 8.

Da kuwa fadar Allah Ta’ala: “Ka sani cewa babu wani abin bautawa sai Allah”. Surar Muhammad: 19.

[5]- Ba wai dukan abinda aka ambata wannan littafi ba ne yake daga cikin jiga-jigan akida, da yawa daga cikin akidojin da aka ambata kamarsu Hukuncin Allah da kaddara, da Raja’a da sauransu ba wajibi ba ne a kudurce da su ko kuma a yi bincike a kansu, ya halatta a dogara ga wani da aka san ingancin maganarasa game da su kamar annabawa da Imamai. Da yawa daga cikin al’amura irin wadannan da muka yi Imani da su dogaro ne kawai da abinda aka samo daga Imamanmu na daga ingantattun hadisai tabbatattu. (Marubuci R.A.)

[6]- Ijtihadi kalma ce ta larabci da aka samo ta daga Juhud a lugga wato yin kokari don yin wani aiki amma a Ka’idar malaman ma na fikihu tana nufin tsamo hukunce-hukuncen shari’a daga nassosinsu tsararru. Akwai Mujtahid Mudlak, wato cikakken mujtahidi, akwai kuma Mujtahid Mutajazzi wato Mujtahiddi a wasu sassa shi ne Mujtahidin da zai iya tsamo hukunce- hukunce a kan wasu al’amura banda wasu. Don karin bayani ana iya duba Littafin Al- Usul Amma lilfikihil Mukarin na Hujjat Muhammad Taki Al- Hakim Shafi na 561 zuwa 565. Da kuma Al- Masa’il Al- Muntakaba na fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Sistani shafina 9 zuwa 10.

[7]- Ihtiyadi shi ne aikin da mutum zai sami yakinin cewa ya sauke wajibin da ke kansa idan ya aikata shi wannan shi ne ihtiyadi a dunkule, akwai kuma ihtiyadi a kebe da ke nufin bin fatawaoyin mujtahidai don tabbatar da cewa an yi aiki da fatawar daya daga cikinsu. Littafin da ya gabata shafi na 10 zuwa 14.

[8]- Taklidi, koyi, shi ne yin aiki daidai da fatawar Mujtahidi wanda maganarsa hujja ne a aikace a halin yanzu tare da kiyaye cewa a bi ta daidai. Masu koyi sun kasu kashi biyu: (1) Wanda bai san kome ba a hukunce-hukuncen sahri’a. (2) Da kuma wanda ya san wani abu amma ba zai iya tsamo hukunce-hukuncen da kansa ba.

[9]- Tafsirul Askari shafi na 300 da Littafin Al- Ihtijaj, 511, H. 337, abinda ya wadatar da karin bayani .

[10]- Manyan Malamai sun kawo abinda ya wadatar da karin bayani a cikin mukaddamomin Risalolinsu na hukunce da ke kunshe da fatawoyinsa a Babin Takalidi (yadda ya wajaba a kan dukan baligi wanda bai kai ga darajar ijtihadi ba kan cewa ya zamanto a cikin dukan ayyukan ibadarsa da mu’amalarsa da sauran ayyukansa, ya zamanto mai yin koyi ko mai yin ihtiyadi, sai dai kawai idan yana da tabbacin cewa ba ya bukatarsa a aikinsa ko kuma barinsa ba zai zama saba wa hukunci ba koda da gwargwadon haramcin shari’a, ko kuma hukuncin ya kasance daga larurar addini da mazhaba kamar yadda yake a wasu wajibai da haramtattu da kuma da dama daga mustahabbai da halalai,  ko ya kuma zamanto ya sami sani a zuci da kuma natsuwa a zuciya daga madogarai na hankali, kamar yaduwar labari, da fadar kwararren da ya tabbatar da cewa suna daga ciki.) A duba: Minhajis Salihin Juzu’i na daya daga fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Husain Sistani shafi na 9.

[11]- Imam Muhammad Mahadi dan Imam Hasan Askari (a.s) wanda shi ne cikamakin Imamai goma sha biyu - Boyuwarsa ta kasance sau biyu ne:

Ta farko: Ana ce da ita karamar boyuwa: Ta fara ne a daga shekarar da mahaifinsa Imam Hasan Askari (a.s) ya rasu shekara ta 260 Hijiriyya kuma ta kare a shekara ta 329 Hijiriyya kuma ya kasance yana da jakadu hudu su ne:

Na farko Usman bin Sa’id Al -Umari Al- Asadi, shi ya kasance wakilin Imam Hadi sa’an nan kuma wakili ga Imam Askari sai kuma ga Imam Muhammad Mahadi. Aminci ya tabbata gare su.

Na Biyu: Muhammad bin Usman bin Sa’idul Umari al- Asadi wanda wanda ya dauki nauyin wakilci bayan rasuwar mahaifinsa na tsawo kimanin shekaru arba’in har zwa mutuwarsa; a shekarar 329 Hijiriyya.

Na uku: Husain bin Ruh wanda ya dauki nauyin al’amarin wakilcin tun daga rasuwar Muhammad bin Usman al- Umarin har zuwa wafatinsa a shekarar 326. Hijiriyya.

Na Hudu: Aliyu bin Muhammad As- Samarri, shi ne na karshe daga cikin wakilai hudu, ya yi wakilcinsa ne na tsawo shekara uku yayin da ya kawo karshe da wafatinsa ranar 15 ga watan Sha’aban shekarar 329. Hijiriyya.

Sananne ne cewa dukan wadannan wakilai an yi musu kabari ne a birnin Bagadaza bayan rasuwarsu, ya zuwa yanzu kuma Makabartunsu sanannu ne mashahurai.

Ta Biyu: Babbar Boyuwa: Ta fara ne daga ranar 15 ga watan Sha’aban shekarar 329. Hijiriyya daga rasuwar wakili na hudu wanda yayin da aka tambaye shi cewa wa zai gadarwa wannan al’amarin kuma sai ya ce Allah na da wani al’amari kuma shi ne mai isar da shi: A cikin wannan akwai bayani game da abinda Imam Al- Muntazar Allah Ya gaggauta bayyanarsa ya sanar da shi game da fara babbar boyuwa wadda take ci gaba har zuwa yau, yayin wakilcin Imam a zamanin boyuwar babba ya zama an sallama shi ga Mujtahidi wanda ya cika sharudan da aka bayyana a littafan fikihu.

Kamar yadda ya gabata a bayanin ma’anar ijtihadi za mu ga cewa tsamo hukunce-hukunce wanda ke nufin “ayyana matsayin aiki game da shari’a tarda dalilai kuma Muhimmancin ijtihadi yana zuwa ne saboda bayyana cewa mutum a bisa biyayyarsa ga shari’a mai tsarki da kuma wajibcin gudanar da hukunce-hukuncenta -lalle ne gare shi ya ayyana abin da zai aikata game da ita. Tunda yake yawancin hukunce-hukuncen shari’a ba su bayyana karara yadda za ta wadatar  daga neman dalilai ba, bai dace da hankali ba a ce za a haramta wa mutane baki daya ayyana matsayin aiki a bisa dalilai, a hana sa duba dalilan da suka ayyana matsayinsu game da shari’a. Don haka aikin tsamo hukunce-hukunce ba ma kawai ya halatta ba ne, larura ne ma a yi shi, wannan larura kuma asalinta daga biyayyar mutum ne ga shari’a, musu a kan haka tamkar musu ne a kan abinda yake bayyananne kuma kalmar ijtihadi a tarihi ta sami fassarori dabam-daban yadda har fassarorin suka sanya ma’anoninsa a cikin duhu har ya kai ga sabani saboda damarwa da rikitarwa ba a samu tabbacin, ma’anarta ba a yau har sai da ya ketare matakai dabam-daban na fassarar ma’anoninsa.

A duba Littafin “Ma’alimuj Jadid Lil Usul: Sayyid Shahid Sadr (r.a) shafi na 23 zuwa sama. Don karin bayani kuma game da Boyawar Imam a duba Littafin Tarikhul Gaibatus Sugra na Sayyid Muhammad Sadr: 395 fasali na uku (Assufara’ul Arba’ati Hayatuhum wa Nashadatuhum).

[12]- Takalidi, koyi da Mujtahidi kashi biyu ne (1) Farawa (2) da Dorewa

Farawa: Shi ne baligi ya yi wa mujtahidi matacce takalidi ba tare da ya riga fara yi masa taklidi tun yana raye ba. Wannan bai halatta ba koda kuwa mujtahidi matacce ya fi wadanda ke raye ilimi.

Dorewa: Wannan kuma shi ne mukallafi ya fara ya yi wa wani mujtahidi ayyananne takalidi tun yana raye sa’an nan ya ci gaba da binsa bayan rasuwarsa. Wannan ya halatta idan har Mujtahidin da ya rasun ya fi wadanda suka raye ilimi ko kuma idan ba a sani ba ko da a dunkule cewa fatawar wanda ya rasun ta saba wa ta wanda yake raye a al’amuran da ya zama yana fuskantar mushkila game da su. Domin karin bayani a duba littafin Urwatul Wuska Juzu’i na I shafi na 17-18, da kuma Masa’ilul Muntakhaba na Sayyid Sisitani Matsala ta 13 (12, 13, 14).

[13]- Al- Kafi Juzu’i na 58/1 H. 19, Al- Mahasin 1/420 H. 963.

[14]- Abubuwan da Mujtahidi ke bukata na ilimi kashi tara ne, uku daga-cikinsu daga ilimin adabi su ne ilimi luga, da ilimin Sarfu, da ilimin nahwau, akwai kuma ilimin aiki da hankali da suka hada da ilimin Usuli, da Ilmul Kalam, da kuma ilimin Mandiki, sai kuma ilimin tafsirin ayoyin hukunce-hukuncen Kur’ani, da ilimin hadisan hukunce-hukunce sai kuma ilimin sanin rauni da kuma inganci da kuma inganci masu ruwaya. Don Karin bayani a duba Al-Wafi fi Usul’ul Fikhi na Fadhilul Tuni 25-29 da kuma AlKur’an wal Akida na Sayyid Muslim Hamudil Hilli: 248-252.

[15]- A duba karin bayanin da ya gabata a kan Abinda muka yi Imami da shi game da Ijtihadi.

[16]- Ihtijaj 2/260 H. 232 Al-Kafi 1/54 H. 10.

[17]- Willayatul Fakihi, shugabancin Malami, ma’ana ce da ke nufin shugabaci na shari’a da ja-gorancin dokoki ga Mujtahidi wanda ya cika sharruda wanda shi wannan matsayi yana mazaunin ci gaban sakon Imama ne kuma ba ya da cikin farrru,n al’amuran addinin a wannan zamanin sai dai ma asalin wannan batu yana da tushe ne tun daga farkon sako da kuma zamanin Imamai Ma’asumai (A.S.) a halin wannan matsayi yana misalta ci gaban Imamanci ta bangaren ayyuka baki daya ya bambanta da Imamanci ta nassosi na musamman ga kowane fakihi, da kuma i,smar da ta kebantu ga Mamzon Allah (S.A.W.A.) da kuma Imami goma sha biyu bayansa tunda yake nassi da isma sun kebantu ne da Ma’asumai (A.S.).

Babu makawa a san hikimar wannan shugabanci na gaba daya a zamanin Boyuwar Imam, wannan matsayi yana nufin kafa hujja ne ga mutane, da kuma ja-gorancin wannan zamanin domin kare amfanin bayin Allah da kuma tafi da al’amuransu a kan yadda shari’ar musulunci ta tsara. Daga cikin manuyan mamfofinta kuwa akwai kare hukunce-hukuncen shari’a domin al’amarin tsara shari’a da sanya dokoki na Allah Ta’ala ne mahalicci mai kudura ,amma dangane da hukunce-hukunce al’amuran rayuwa kuwa musamman sababbi da ke aukuwa yanzu, ba za su gaza kasan cewa tabbacin hukunce-hukunce ne da aka gama gabatar da su daga bangaren Manzo (S.A.W.A.) ba yayin rayuwarsa...

An ruwaito daga Imam Mahadi, (Allah ya gaggauta bayyanar sa cewa “Amma hakikanin al’amura masu faruwa to dangane da su ku koma ga masur ruwaita hadisanmu, domin su hujjato ne a kanku ni kumar hujjar Allah ne a kansu.” Aduba Littafin Al- Imama Hatta Wilayatul Fakih shafi na 51.”

[18]- Ruwayar Umar Bin Hanzala na ishara da haka yayin da ya ce: `Na tambayi Aba Abdillah Alaihis Salam dangane da mutane biyu daga cikin ma’abutanmu (shi’a) wadanda ke da rikici a tsakaninsu a kan bashi ko kuma gado suka kai kara zuwa gurin shugaba ko Alkalai shin haka ya halatta? Ya ce: Wanda ya kai kara gare su a kan gaskiya ko karya to ya kai kara gurin Dagutu da kuma abinda Allah Ya yi umarni a kafirce masa, Allah Ta’ala Ya ce: “Suna so ne su kai kara zuwa ga Dagutu alhali kuwa an umarce su da su kafirce masa” Na ce: To yaya za su yi? Ya ce: Su duba wanda ya ruwaito hadisanmu, ya kuma duba halal dinmu da kuma haram dinmu, kuma ya san hukunce-hukuncenmu su amince da shi a matsayin mai hukunci, domin ni na sanya shi mai hukunci a kanku, idan ya yi hukunci da hukuncinmu bai amince ba to ya wawaitar da hukuncin Allah kuma ya dawo mana da hukuncin ne, wanda ya mayar mana kuwa ya mayar wa Allah, kuma daidai yake da shirka da Allah”.

Al-Wasa’il Juzu’j na 27 shafi na 136 Hadisi na 33416, Al Kafi Juzu’i na 1 shafi na 54 Hadisi na 10, Al- Ihtijaj Juzu’i na 2 shafi na 260 Hadisi na 232, Tahzibil Ahkam Juzu’i na 6 shafi na 218 hadisi na 514 da shafi na 301 hadisi na 845 da kuma surar Nisa’i aya ta 60. 

[19]- Abin nufi da dukiya: Zakka da khumusi. Zakka tana daga wajiban addini. Hadisai da dama suna nuna cewa mai hana Zakka kafiri ne, da kuma cewa wanda baya ba da zakka ba shi da salla. Zakka tana wajaba ne a kan abubawa tara:

1- Dabbobin Ni’ima guda uku wadanda su ne: Rakumi da shanu da kuma tumaki da Awaki.

2- Zinare da Azurfa

3- Kayan Abinci hudu-Alkama, Sha’ir, Dabino da kuma zabibi.

A kowace shekara ake karbar zakka a wadanda abubuwan tara a bisa kimanin da aka sani, da sharrudan aka ambata a gurarensu, zakka ba ta wajaba ba a kan abubuwan da ba wadannan taran ba sai dai kuma mustahabbinea fidda zakka a dukiyar kasuwanci da dawaki  da kuma abubuwan da kasa ke tsirarwa na daga ‘ya’yan itaciya da wasunsu. Wadannan dukiyoyin kuma ana kashe su ne a kan kasafi takwas wadanda su ne: 1- Fakiri 2- Miskini 3- Masu Aikinta 4- Wadande aka son jawo hankalinsu ga musulunci 5- Bayi 6- Wadanda ake bi bashi 7- A tafarkin Allah -wato dukan wata  hanyata alheri, an kuma ce ya kebanta ne ga abinda ya shafi fa’idar kowa da kowa. 8- Wanda ke kan Tafarki, shi ne matafiyi wanda guzuri ya yanke masa ko kuma kayansa ya bace yadda ba zai iya komawa muhallinsa ba koda kuwa mawadaci ne, babu wani al’amari na zakka a mazhabar Shi’a Imamiyya face ya yi daidai da sauran mazhabobi hudun nan sanannu.

A duba littafin Urwatul Wuska Juzu’i na 2 shafi na 87-134, da masa’ilul Muntakhaba na sayyid Sistani, da Aslus Shi’a wa Usuliha da rubuto hujjojinsanaMu’assasar Imam Ali (A.S.) shafi na 243.

Khumusi: A gurin Shi’a Imamiyya hakki ne da Allah Ya wajabta saboda zuriyar gidan Manzon Allah Muhammad (S.A.W.A.) a madadin sadakar zakka wadda take haramun ce gare su. Asalinsa kuma shi ne fadar Allah Ta’ala: “Ku sani cewa lalle abinda kuka samu ganimarsa da wani abu to lalle khumusinsa na Allah ne da Manzonsa da kuma dangi makusata.” Surar Anfal ayata 41.

Khumusi ya wajaba ne a kan abubuwa bakwai:

1-    Ganimar da aka kwata daga kafiran yaki yayin yakayya da su tare da izinin Imam.

2-    Ma’adanai kamar su zinare da azurfa da...

3-    Taskar tsintuwa a karkashin kasa

4-    Jawharai da aka tsamo a teku.

Dukiyar Halal da ta gauraya da ta Haram kuma ba a san mamallakinta ba.

1-    Fegin Kafirin amana ya saya a gurin musulmi.

2-    Abinda ya saura daga kasafin shekara da kasafin iyali na ribar kasuwanci da aiki.

Ana raba khumusi kashi shida:

1-    Na Allah

2-    Na Annabi.

3-    Na Imam. Wanan kasafin gida uku ya kebanta ne ga Imam Mahadi da ake jira. Allah ya gaggauto da bayyanarsa. Amin.

4-    Marayu

5-    Miskinai da kuma

Wadanda ke kan tafarki guzuri ya yanke musu.

Domin karin bayani a duba Urwatul Wuska Juzu’i na 2 shafi na 170-199, da kuma masa’ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani matsala ta 251-239, da Aslushi’a wa Usuliha shafi na 245 da ma dukan Risalolin hukunce-hukunce.     

 

عنوان الکتاب