SHURA

 

bullet

SHURA CIKIN ALƘUR’ANI DA SUNNA

bullet

NASSI NA FARKO:

bullet

NASSI NA BIYU:

bullet

MANUFAR “SHURA” DA ABIN DA TA ƘUNSA.

bullet

Mahanga ta Farko:

bullet

Mahanga ta Biyu:

bullet

NASSI NA UKU:

bullet

SHURA CIKIN TARIHI DA SIYASAR MUSULUNCI

bullet

FARKON BAYYANAR RA’AYIN “SHURA

bullet

SHURA CIKIN SHINGENTA NA NAZARIYYA

bullet

SHURA KO TAKOBI ?

bullet

MAKOMAR SHARUƊƊAN SHUGABANCI:

bullet

NEMAN MAFITA:

bullet

ABUBUWA BIYU:

bullet

Abu Na Farko: Tafarkin Magabata?!

bullet

Abu Na Biyu: Tawayen Da Ke Da Lada:

 

 


 

SHURA CIKIN ALƘUR’ANI DA SUNNA

 

Alƙur’ani mai girma ya yi magana a kan “shura” a wajaje uku, sai dai kuma da siga daban-daban:

 

 

NASSI NA FARKO:

Faɗin Allah Maɗaukakin Sarki kan batun shayarwa cewa:

 

)والوالدات يرضعنَ أولادهنّ حولين كاملين لمن أراد أن يتمّ الرضاعة وعلى المولود له رزقهنّ وكسوتهنّ بالمعروف...فإن أرادا فصالاً عن تراضٍ منهما وتشاور فلا جناح عليهما (

 ((Kuma masu haifuwa suna shayar da abin haihuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana akan wanda aka haifar masa, da alheri…-..To idan suka yi nufin yaye, a kan yardatayya daga gare su, da shawartar juna, to, babu laifi a kansu…))[1] .

 

Wannan aya tana magana ne kan shayarwa, kan cewa iyaye suna da daman su yi shawara tsakaninsu kan jaririnsu, shin za ta shayar da shi ne na shekara biyu ko ta yaye shi kafin wannan lokaci, tare da la’akari da ita uwar da kuma shi jaririn da kuma yanayin gida din, ba cuta ba cutarwa.

Ko kuma ma su yi shawara tsakaninsu su samo wata mace daban don ta shayar da jaririn:

 

) وإن أردتم أن تسنرضعوا أولادكم فلا جناح عليكم إذا سلّمتم ما آتيتم بالمعروف واتقوا الله واعلموا أن الله بما تعملون  بصير(

((…Kuma idan kun yi nufin ku bayar da ɗiyanku shayarwa, to, babu laifi a kanku, idan kun miƙa abin da kuka zo da shi bisa al’ada. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne))[2].

 

Wannan aya mai girma tana magance mishkila daga mishkilolin zaman iyali da kuma abin da ya ta’allaƙa da wanda ake shayarwa da kuma kiyaye duk wani abin da zai iya ruguza halin zaman iyali[3].

 

NASSI NA BIYU:

Idan muka duba tarihin yaƙin Uhudu inda sojojin Musulunci suka watse suka bar Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mutane kaɗan na daga cikin sahabbansa, abin da ya jawo musu naƙasi kana ga kuma saɓon Allah mai girma, musamman ma kasantuwan Manzon Allah (s.a.w.a.) bai fita zuwa yaƙin ba sai da ya shawarce su kuma suna masu kwaɗayin zuwa, amma abin mamaki sai suka watse suka bar shi tamkar sarkin da talakawansa suka watse masa. Ko da suka dawo sun ɗauka zai yi fushi da su kamar yadda duk wani shugaban yaƙi da sojojinsa suka watse suka bar shi yake yi, amma a madadin haka sai suka ga girmamawa da tausayawa daga gare shi. Take jikinsu ya yi sanyi. Sai Allah Ya albarkaci wannan ta’ada mai girma ta Ma’aiki kuma madalla da wannan ɗabi’a. Nan take sai aya ta sauko, tana cewa:

 

]فبما رحمةٍ من الله لِنتَ لهم ولو كنت فظًّا غليظ القلب لانفضّوا من حولك(

Ma’ana: ((Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai hushi, mai kaurin zuciya, da sun watse daga gefenka…)).[4]

 

Wannan aya tana nuni da cewa wannan tausayi da runtse idon (Manzon Allah) kan wannan zunubi rahama ce daga Ubangiji. Ya mamakin irin wannan rahama!! wacce ta sa Manzon Allah (s.a.w.a.) tausaya wa al’ummar da ta fitar da shi zuwa yaƙi amma ta gudu ta bar shi lokacin da ta ga wahala don tserar da kanta.

Don saboda cikan wannan rahama ce sai aya ta sauka inda take kiran wannan al’umma zuwa ga matsayinta na farko ta gyara kana ta magance kura-kuran da ta aikata a baya, Allah Maɗaukakin Sarki Yana faɗa wa ManzonSa cewa:

 

(..... فاعفُ عنهم واستغفر لهم وشاورهم في الأمر).

 Ma’ana: ((…Sai ka yafe musu laifinsu, kuma ka nema musu gafara, kuma ka yi shawara da su a cikin al’amarin….)).[5]

 

Wannan rahama ba ta tsaya kan tausayi, afuwa da yafuwa kawai ba har ma ta ci gaba ne da neman shawararsu cikin al’amurran da suke buƙatan shawara, saboda haka har ma suka zamo wata gaɓa wajen gina wannan al’umma mai girma.

Amma abin lura a nan shi ne, Alƙur’ani mai girma bai bar wannan al’amari haka kawai ba, sai da ya kafa tsari da dokokin da za’a bi yayin kowace shawara. Alƙur’ani ya ba wa Annabi (a matsayinsa na shugaba) daman yanke hukumci bisa abin da yake da maslaha ga al’umma. Shin hakan ya yi daidai da ra’ayin mutane ko bai yi ba, Allah Yana cewa ga ManzonSa (s.a.w.a):

 

( ....فإذا عزمت فتوكّل على الله...).

Ma’ana: ((….Sa’an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dogara ga Allah…))[6].

 

 

MANUFAR “SHURA” DA ABIN DA TA ƘUNSA.

 Mene ne manufa da abin da wannan “shura” wanda waɗannan ayoyi suka ambata, ta ƙunsa? Shura a aya ta farko ta ƙunshi magana ne akan shayarwa kuma hadafin (“shura”) shi ne kiyaye abin da zai cuci jariri da kuma kiyaye iyali.

Amma “shura” a aya ta biyu ta saɓa wa ta farko, domin a nan mai neman shawarar shi ne Manzon Allah (s.a.w.a.) wanda ake shawarta kuwa su ne sahabbansa.

Abin tambaya a nan shi ne, shin wasu abubuwa ne Manzon Allah (s.a.w.a.) yake buƙatan shawararsu (sahab-bai) a kai? Shin a kan al’amurran addini ne ko na duniya?

Kana mene ne dalilin neman shawararsu, shin don su shiryar da shi (Annabi) ne zuwa ga hanya madaidaiciya? Ko kuma? Malumman tafsiri sun yi maganganu akai, musamman ma magana a kan tambayarmu ta farko, wato wasu al’amurra ne Annabi yake buƙatan shawarar jama’a (sahabbansa)?

Al-Shaukani yana cewa: “Abin nufi shi ne ko wani al’amari wanda ake shawara a cikin irinsa, ko kuma ana nufin al’amarin yaƙi kawai ne kamar yadda ya zo a wan-nan aya….To abin nufi a nan shi ne shawara a kan abin da babu nassi bayyananne a kai”[7].

To a nan muna fahimtar cewa ita “shura” (neman shawarar jama’a) ba’a yin ta akan abin da akwai bayya-nannen nassi. Ma’ana al’amurran addini da hukumce-hukumce, a nan ba’a neman shawarar jama’a shin sun yarda ko basu yarda ba. Wannan al’amari ne da ya shafi Ubangiji, babu fagen jin ra’ayin kowa.

Don haka za mu gane ke nan cewa “shura” ana yin ta ne akan al’amurran duniya kamar yadda sigan wannan aya ta nuna kan al’amarin yaƙi. Kuma ba wai kawai ayar ba, hatta tarihi ma ya tabbatar da cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana neman shawarar sahabbansa a kan wasu al’amurra da suka shafi yaƙi kamar abin da ya faru lokacin da ya fuskanci abokan gaba a Badar, da kuma kan batun fursunonin yaƙin Badar, da fitarsa zuwa Uhudu da kuma yaƙin Khandaƙ.

Amma in banda sha’anin yaƙi hakan bai faru ba, imma ya faru to a wurare kaɗan ne. Kai hatta ma a al’amarin yaƙin ba ko yaushe ne yake neman shawararsu ba. Domin Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan zaɓi lokaci da kuma abin da ya ga ya dace ne kan al’amarin yaƙi ko da kuwa wasu ba su yarda ba, kamar abin da ya faru lokacin da ya naɗa Usamah a matsayin kwamandar rundunar musulmai, ko kuma lokacin da ya zaɓi Zaid bn Harith shugaba a rundunar Mu’uta ko da bayan Ja’afar bin Abu Talib, da kuma lokacin sulhunsa da mushrikai a Hudaibiyya da dai sauransu.

Da sannu za mu daɗa faɗaɗa wannan bincike a bayyane kan al’amarin “shura” da kuma iyakokinta.

 

Hadafofin Wannan “Shura”.

 

Dangane da hadafofin wannan “shurar”, za mu iya ba ta mahanga guda biyu saboda binciken da muka yi a kan waɗannan hadisai da ake jingina su ga Annabi (s.a.w.a) da kuma maganganun manyan malaman tafsiri na da da na yanzu.

 

Mahanga ta Farko:

Za mu iya fahimtarta ne a cikin waɗannan nassosi masu zuwa:

(1). An ruwaito daga Ƙatada yana cewa: ((Allah Ya umurci ManzonSa (s.a.w.a) da ya dinga neman shawarar

sahabbansa a cikin al’amurra domin hakan shi ya fi daɗi ga ran jama’a, saboda a duk lokacin da al’umma suka nemi shawarar juna da nufin neman yardar Allah, to za su daidaita akan shiriya[8])).

A nan za mu gane cewa Allah Ya umurci ManzonSa (s.a.w.a) da ya shawarci mutanensa da kuma sahabbansa ne saboda waɗannan fa’idoji da aka ambata.

(2). An ruwaito daga Alhasan yana cewa: ((Allah Ya umurci ManzonSa (s.a.w.a) da ya nemi shawarar sahabai ne don ya sunnanta wa sauran (shuwagabanni) da za su zo bayansa, amma haƙiƙa Allah Ya san cewa, Manzo ba ya buƙatuwa da shawararsu[9])).

A nan za mu iya fahimtar cewa Annabi (s.a.w.a.) ya aikata haka (“shura”) ne don waɗanda za su zo bayansa su kwaikwaya ba wai don yana da buƙatuwa da ita ba, (don kuwa shi  ana masa wahayi daga Allah, su kuwa ba’a musu) don haka ne ta zamo ɗaya daga cikin sunnoni da shugaba zai kula da ita.

(3). Al-Razi yana cewa: ((Annabi (s.a.w.a.) ya aikata hakan (shura) ne don sauran mutane su yi koyi da shi kuma ya zama sunna ga al’ummarsa[10])).

A nan ma za mu iya cewa ita “shura” wata aba ce da shugaba zai lura da ita wajen tsara al’amurran siyasa, tsare-tsaren zamantakewa tare da la’akari da yanayin jama’a ko kuma hangen nesa cikin tafiyar da mulkinsa amma ba akan abubuwan da suka shafi hukumce-hukumce ko kuma abubuwan da nassoshin shari’a suka yi bayaninsu a fili ba.

Bisa ga bayanan da suka gabata, za mu iya ba wa wannan “shura” sunan “Shurar Shugaba”.

 

Shin Wannan “Shura” Tana Da Wani Takamammen Tsari?

 

Abin tambaya a nan shi ne, tun lokacin da wannan aya mai girma ta sauka har zuwa lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya rasu, shin wannan “shurar” ta ɗauki wani takamammen yanayi da kuma tabbataccen tsari?

To yayin amsa wannan tambaya, muna iya cewa, abin sani dai shi ne cewa a dukkan lokutan da aka yi “shura” – wanda ta fi yawa ne ma a abubuwan da suka shafi yaƙi – Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kan zaɓi wanda ko waɗanda ya so ne don jin shawararsa ko shawararsu. A wani lokacin kuma ya kan saurari ra’ayuyyukan jama’a ne ba tare da ya zaɓi wasu mutane ba. Misali:

-            idan muka duba yaƙin Khandaƙ, za mu ga ya ɗauki shawarar Salman al-Farisi ne na tona rami a kewaye garin Madina da shi saboda abokan gaba, wanda hakan kuma ya taimaki Musulunci da kuma musulmai[11].

-         A yaƙin Khandaƙ ɗin dai lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya nemi sulhu da mutanen “Gatfan” ƙarƙashin ja-gorancin shugabansu Uyaynatu bn Hisnu da nufin zai ba shi wani sashi na ‘ya’yan itatuwan Madina da sharaɗin zai janye mutanensa na Gatfan da Hawazin daga cikin rundunar kafirai don Annabi ya sauƙaƙe wa mutanen Madina halin tsananin da suke ciki kuma ya karya ƙarfin kafirai kana kuma ya wargaza rundunoninsu. Saboda haka sai Annabi (s.a.w.a.) ya kira shuwagabannin ƙabilun Aws da Khazraj (manyan ƙabilun Madina) wato Sa’ad bn Mu’az da Sa’ad bn Ubadah don neman shawararsu akan hakan. Sai suka ce masa: Ya! Manzon Allah, in har Allah Ya umurce ka da wani abu ne to ka aikata, in kuwa babu wani umurni to mu kan ba za mu ba su komai ba sai takobi (wato babu maganar sulhu sai dai yaƙi).

Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce musu: “A’a, ba’a umurce ni da komai ba, da an umurce ni da wani abu ai da ban shawarce ku ba…da kawai sai in aikata. Wallahi ban aikata haka (neman sulhu) ba sai don kawai na ga larabawa sun juya muku baya kuma suna farautarku ta ko wani ɓangare, shi ya sa nake so in cire muku wannan ƙaya”. Daga nan sai Annabi (s.a.w.a.) ya yi farin ciki da wannan magana tasu, sai ya ce wa Uyaynatu bn Hisnu, “Ku koma babu wani abu tsakaninmu face yaƙi”[12].

A nan za mu ga cewa Annabi (s.a.w.a.) ya so gwada haƙuri, tsayin daka da kuma gaskiyan imanin mutanen Madina ne. kamar yadda kuma wannan hadisi ya daɗa tabbatar mana da cewa ba’a yin “shura” a duk lokacin da akwai wani umurni daga Allah ko ManzonSa (s.a.w.a).

Abu na uku shi ne inda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nemi shawarar Imam Ali (a.s.) da Zaid bn Harith (r.a.) kan zargin da aka so yi wa ɗaya daga cikin matayen Annabi (s.a.w.a.) a hadisin Ifki.

Lokaci na huɗu kuwa shi ne lokacin sulhun Hudaibiyya lokacin da Annabi (s.a.w.a.) ya saurari shawarar mace ɗaya, wato Ummu Salama (r.a). Yadda lamarin kuwa yake shi ne cewa bayan sa hannu akan yarjejeniyar, Annabi (s.a.w.a.) ya umurci sahabbansa da su yi hadaya (yanka dabbobin da suka zo da su), amma babu wanda ya bi wannan umurni, sai Annabi (s.a.w.a.) ya koma cikin tantinsa cikin ɓacin rai. Ganin irin halin da yake ciki, sai Umm Salama ta ce masa: “Ya! Manzon Allah da ka yanka naka (hadayar) wataƙila da su ma sun yanka bayanka”. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yanka tasa hadayar, sai su ma suka yanka tasu[13].

Ba tare da la’akari da inganci ko rashinsa ba, waɗannan su ne mashahuran misali da tarihi ya kawo kan “shura”, tun daga saukar wancan aya har lokacin rasuwar Annabi (s.a.w.a.), babu wani abin da aka yi sama da abin da da ma ake yi kafin saukarta…kuma babu wani tsari na takamamme da aka tsara kuma babu wasu mutane na musamman da aka ayyana….kuma babu wani abin da wasu suke da’awa na samuwar (Majalisar Mutane Goma).

Babu wata majalisar “shura” ta mutum goma a zamanin Annabi (s.a.w.a.), kuma hatta mai da’awar cewa akwai din[14] ba zai iya kawo wata hujja na tarihi kan samuwarta ba lokacin Annabi (s.a.w.a.). Kuma ba zai iya kawo dalili ko guda ba na samuwarta lokacin halifancin AbuBakar (r.a) ko rayuwar Umar (r.a) ba, hatta ma sai ga shi mutane shida Halifa Umar ya zaɓa don zaɓen halifa ma ba goma ba!.

Abin mamaki a nan shi ne waɗansu irin hujjoji (wanda ma sun fi na farko rauni) da ake kawowa don tabbatar da “shura” waɗanda ba su da asali, wasu ma suna korewa ne maimakon tabbatarwa.!

Daga cikin hujjoji na ban mamaki waɗanda ake kafa hujja da su don tabbatar da hakan su ne waɗannan abubuwa guda uku:

Na Farko: Inda yake cewa: Sa’id bn Jubair yana magana a kan wannan al’amari mai muhimmanci, yana cewa: “Haƙiƙa Abubakar, Umar, Uthman, Ali, Ɗalha, Zubair, Sa’ad, Abdurrhaman bn Awf da Sa’id bn Zaid, sun kasance gaba ga Annabi lokacin yaƙi sannan a bayansa lokacin salla”. Daga wannan magana sai ya fitar da cewa waɗannan mutane goma ba kawai sun kasance ministoci kuma ‘yan majalisar shawarar Annabi (s.a.w.a.) ne ba har ma sun kasance da’iman a bayansa lokacin salla sannan kuma a gabansa lokacin yaƙi[15].

Ba tare da la’akari kan ingancin nasabta wannan magana ga Sa’id bn Jubair ko rashinsa ba, da za mu buƙaci mai bincike kan ya binciko mana wani yaƙi da waɗannan mutane goma suka tsaya gaba ga Annabi (s.a.w.a.) lokacin yaƙi, da kuwa ya kasa samun hakan bayan tsawon bin-cike.!

Na Biyu: Inda yake cewa: A cikin waɗannan mutane goma akwai mutane takwas da suka riga kowa shiga Musulunci, su ne na farko-farko a Musulunci kuma muhajirai[16]…..Wannan magana ma da’awa ce wadda ba ta da wani inganci….shin shigan waɗannan takwas ɗin Musulunci da farko shi ya ɗaga (darajar) sauran mutum biyun?!

Kai ina ma rigayya a nan, in ka cire Ali, dukkansu waɗansu sun rigaye su shiga Musulunci. Khadija (matar Annabi (s.a.w.a.) ) ta rigaye su, Ja’afar bn Abi Talib ya riga su, haka ma Khalid bn Sa’id bn al-Ass da ɗan’uwansa Usman, haka ma Zaid bn Harith, haka ma Abu Zar al-Giffari (na biyar a Musulunci) da dai sauransu[17].

Na Uku: Wanda ya fi kowannensu kasantuwa kame-kame ne shi ne abin da ya ruwaito daga maganar wani ɗan leƙen asiri mai suna Fawn Ploton lokacin da aka bijiro masa da tambayoyi sai ya ce: “Shin “shura” a zamanin Annabi ta tashi daga matsayinta na rashin takamammun mutane zuwa majalisa mai cikakken tsari da takamammun mutane?”.

Lokacin da ya rasa gamsasshiyar amsa cikin tarihi da zai bayar, sai ya faɗa cikin kuskuren da Fawn Ploton ya faɗa saboda rashin fahintarsa ga harshen larabci. Don kuwa lokacin da ya karanta cewa an karɓo daga Ashab al-Suffa, su ne waɗanda suke zaune a masallaci a kan wani sashe mai girma, kuma adadinsu su saba’in ne, sai ya zaci cewa wannan kalma ta al-Suffa, tana nufin (al-Safwa) ne, wato zaɓaɓɓu. Don haka sai ya fassara shi da cewa su waɗansu mutane ne guda saba’in da aka zaɓa kuma ba sa barin masallacin, suna nan ne a matsayin wata cibiya ta ba da shawara. Bai fahimci cewa su waɗannan da ake ce ma Ashab al-Suffa, waɗansu mutane ne da suka fi kowa rauni daga cikin musulmai ba, basu da wani matsuguni don haka suka riƙi masallaci mazauninsu.

 Ko da yake wannan ba abin mamaki ba ne don ɗan leken asiri ya faɗi haka saboda rashin fahimtan larabci, amma abin mamakin shi ne babban malami kamar Shaikh Muhammad Ammara ya ɗauki wannan kuskuren a matsayin hujja da zai kawo don tabbatar da wannan mas’ala mai muhimmanci, inda yake cewa: “Haƙiƙa wannan shi ne yake nuna samuwar wata majalisa ta shura mai mutane saba’in a zamanin Annabi (s.a.w.a.)”, hujjarsa ita ce wannan magana ta Fawn Ploton[18]!

 

Ku Kuka Fi Sanin Abin Da Ya Shafi Duniyarku!

 

Wannan wata fassara ce daga cikin fassarorin da ake yi wa zaman da Annabi (s.a.w.a.) yake yi da sahabbansa don shawari. Saboda in muka yi la’akari da ƙarancin ilimin ɗan’ Adam, lallai ne wani zai iya risko abin da wani bai riska ba musamman ma a al’amurran da suka shafi rayuwar duniya, to a saboda wannan dalili ne ya sa Annabi (s.a.w.a.) yake cewa: “Ku kuka fi sanin abin da ya shafe ku na al’amarin duniya[19]”.

To amma (mu a gurinmu) wannan ba karɓaɓɓen fassara ba ce ga wannan hadisi na “ Ku kuka fi sanin abin da ya shafe ku kan al’amurran duniyarku”, idan muka raya cewa hadisin ingantacce ne. Domin kuwa Annabi (s.a.w.a.) ya faɗi hakan ne yayin faruwar wani keɓantaccen abu wato magana kan kililin dabino, kuma al’amari irin wannan bai shafi aikin annabci ko sha’anin shugabanci na siyasa ba. Kuma a fili yake cewa babu wani shugaba daga cikin shuwagabanni da zai samu abin tambaya kan al’amarin kililin dabino ko kuma gyara abin da ya shafi tsohon gini da kulawa da kayan gidajen mutane ko kuma yadda ake ɗinka riga ko kuma yadda ake kasa kaya a kasuwa!

Wannan al’amari ne da su mutane za su yi amfani da ilimi da dabarun da suke da shi wajen aikata shi tare da la’akari da irin halin da suke ciki. Amma a ce wai a cikin mutane akwai wanda ya fi Annabi (s.a.w.a.) sanin yadda ake gudanar da siyasa ko mulki kuma ya fi shi sanin maslahohi da kiyaye su, wannan wata magana ce wadda ba ta da asali a Musulunci.

Haƙiƙa, hankali ba zai yarda da cewa wannan hadisi yana nufin cewa su (sahabbai) sun fi Annabi (s.a.w.a.) sanin siyasar tafi da mulki da kuma tsare-tsaren siyasa da zamantakewar mutane da kuma tattalin arziki ba!

Lalle wannan hadisi bai wuce yana magana kan waɗancan misalai da suka gabata kan al’amurran da suka shafi mutane na kansu wanda su ne suke kula da su, domin kuwa ba haƙƙin shugaba - shin Annabi  ne ko ba Annabi ba – ba ne ya kula musu da shi ba.

Don haka a taƙaice abin da muka gano dangane da wannan mahanga ta farko, shi ne: wannan “shura” da aka umurci Annabi (s.a.w.a.) da ita “shura” ce irin ta kowane shugaba, wato ya nemi shawarar wanda ya ga dama daga waɗanda suke da wata masaniya a kan wani takamammen al’amari. Babu wani takamammen dalili da yake nuna dogaro da “shura” wajen ayyana shugaban (gudanar da mulki) da kuma zamantakewa a Musulunci.

 

Mahanga ta Biyu:

Wannan mahanga ta saɓa wa ta farko kan nesantar sha’anin tsarin siyasa da mulki, ita tana magana ne kan zamantakewa da jin daɗin al’umma da lura da al’amurran da suka shafi mutane. A nan ba wai muna cewa ita wata mahanga ce da ta shafi mutum shi kansa kawai ba, domin kuwa a cikinta akwai alaƙa tsakanin ɓangare biyu wato mai neman shawara da mai ba da ita shawarar, wanda aikinsa shi ne nasiha da gaskiya da kuma riƙon amana. A nan ka ga ta zama wata alaƙa ce tsakanin al’umma wacce take da wani muhimmin tasiri a zamantakewa.

An ruwaito Ibn Abbas yana cewa, lokacin da ayar:

(وشاورهم في الأمر).

Ma’ana: ((…kuma ka yi shawara da su a cikin al’amarin….))[20],

 

 ta sauka, sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce: “Haƙiƙa Allah da ManzonSa sun wadata daga ita (shura), sai dai Allah Ya sanya ta ne don ta zama rahama ga al’ummata, duk wanda ya nemi shawara daga cikinku ba zai rasa shiriya ba wanda kuwa ya bar ta ba zai rasa ɓata ba[21]”.

A nan za mu gane cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ba ya buƙatuwa da shawarwarin mutane don neman dacewa hatta ma a kan al’amurran duniya, face ma dai ya wadata daga ita, sai dai ita (neman shawara) kawai rahama ce ga sauran mutane don su sami dacewa a kan ayyuka da ma’amalolinsu, kana don su guji babakere da bin ra’ayinsu wanda zai iya kai su ga halaka. Za mu gane hakan ne kuwa in muka yi la’akari da hadisin da Annabi (s.a.w.a.) yake cewa: “Babu wata al’ummar da za ta nemi shawara (kan al’amurorinta) face ta sami shiriya da daidaituwa kan al’amurranta[22]”, da kuma wannan hadisin da yake cewa: “Ku nemi shiryu (shawara) daga mai hankali sai ku shiri-ya, kada ku saɓa masa sai ku halaka (yi nadama)[23]”.

An ruwaito hadisai da dama waɗanda suke kwaɗaitar da mutane kan (neman) shawara. A wani hadisin ma an kira mai ba da shawara da sunan “amini[24]”.

Wani hadisin ma cewa yake: “Duk wanda ɗan’uwansa ya nemi shawararsa amma sai ya ba shi mummunar sha-wara (da gangan), to haƙiƙa ya ha’ince shi[25]”.

To wannan shi ne mahanga ta zamantakewa ta “shura”, wanda kuma zai fito a nassi na uku…..

 

 

NASSI NA UKU:

Faɗin Allah Ta’ala cewa: ( وأمرهم شورى بينهم). Ma’ana: ((…kuma al’amarinsu shawara ce a tsakaninsu….)[26].

 

Wannan aya mai girma ta zo cikin sigar gamaiya wanda yake magana kan al’umma wacce ta kai ƙoli. Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa:

 

) ....وما عند الله خيرٌ وأبقى للذين آمنوا وعلى ربّهم بتوكّلون õوالذين يجتنبون كبائر الأثم والفواحش وإذا ما غضبوا هم يغفرون õ  والذين استجابوا  لربّهم وأقاموا الصلاة و أمرهم شورى بينهم ممّا رزقناهم ينفقون` والذين  إذا  أصابهم البغيُ هُم ينتصرون(

Ma’ana: ((….kuma abin da ke a wurin Allah, shi ne mafifici, kuma shi ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi imani kuma suna dogaro a kan Ubangijinsu kawai. Kuma waɗanda ke nisantar manyan zunubai da ayyukan alfasha, kuma idan sun yi fushi, su suna gafartawa. Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangi-jinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al’amarinsu shawara ce a tsakaninsu, kuma daga abin da Muka arzurta su suna ciyarwa. Da waɗanda idan zalunci ya same su, suna neman taimako (su rama).))[27].

 

Wannan aya tana nuna mana hali ne na al’umma musulma mai kamanta hadafi da ɗabi’u na Musulunci duk da irin imani, dogaro ga Allah, nisantan manyan zunubai da munanan ayyuka, yafuwa da lamunta (ga macuci), amsa umurnin Ubangiji, kiyaye salla, kore gaba da adawa, sannan kuma sai ga su mutane ne masu shawara a kan al’amurorinsu. Kuma ayar tana nuna su da cewa masu shiriya da fuskantar haƙiƙa ne, masu neman shiriya da daidaito ta hanyar komawa ga hankali. Sannan kuma ma’anar wannan aya tana da kusanci da ma’anar ayar da Allah Yake siffanta muminai da cewa: ((Waɗanda ke sauraron magana, sa’an nan su bi mafi kyaunta)).[28]

A dalilin wannan nassi ne, malaman tafsiri suke ganin cewa mustahabi ne neman shawarar mutane kan al’amurori don shiryuwa daga tunani da ra’ayoyinsu, kamar yadda muka kawo a hadisan da suka wuce a baya…

((Babu wata al’ummar da za  ta nemi shawara, face ta sami shiriya da daidaituwa kan al’amurorinta)).

((Ku nemi shiriya (shawara) daga mai hankali, sai ku shiriya, ba za ku saɓa masa ba kuwa face sai kun yi nadama)).

((Wanda ya nemi shawara kan al’amurorinsa, zai samu shiriya a kansu))[29].

Shura ta Shugaba Har Ila Yau:

Suyuti ya ruwaito wani hadisi da aka jingina shi ga Sayyidina Aliyu (a.s.) da yake magana akan wannan “nassi”. Hadisin yana cewa: Ali (a.s.) ya ce: “Na tambayi Ma’aikin Allah (s.a.w.a) cewa: Ya Rasulallah! Yaya za mu yi kan al’amarin da ya bijiro mana bayanka wanda Alƙur’ani bai yi magana a kansa ba kuma ba mu ji wani abu daga wajenka a kansa ba?” Sai Annabi (s.a.w.a.) ya ce: “Ku sanya mutumin kirki, bawan Allah daga cikinku (a matsayin shugaba) sannan ku sanya al’amarin “shura” tsakaninku, kada ku yi amfani da ra’ayin mutum guda”[30].

Ko da yake idan muka yi bincike kan ingancin wannan hadisin za mu ga ba shi da wata ingantacciyar madogara. Sai dai wannan hadisi yana magana ne a kan sabin al’amurori da za su iya faruwa bayan Annabi (s.a.w.a.) wanda Alƙur’ani mai girma ko hadisi basu yi magana a kai ba, kuma hakan sun haɗa da sabin abubuwan da suka shafi rayuwa da zamantakewar mutane……

A cikin wannan hadisi Annabi (s.a.w.a.) yana ishara ne da abubuwa biyu, na farko dangane da shugabanci, inda yake cewa: (Ku zaɓi mutumin kirki daga cikin al’um-mata), sannan janibi na biyu kuma yana magana kan yin shawara ta hanyar tara mutanen kiriki don yin hakan.

Don a nan za mu iya fahimtar cewa idan har akwai wata magana daga Annabi (s.a.w.a.), to babu buƙatan yin “shura” kan wannan al’amari.

Duk da haka idan muka yi bincike kan wannan hadisi za mu ga ba shi da asali ko inganci. Ibn Abdul Bur yana cewa, wannan hadisi ba shi da asali. Darul Ƙutni shi ma cewa yake: “ba shi da inganci”. Haka ma al-Khatib na cewa: “bai inganta ba a wajen Malik”[31].

 

 

SHURA CIKIN TARIHI DA SIYASAR MUSULUNCI

Wannan bincike zai yi magana ne kan “shura” wajen zaɓen shugaba (halifan Manzon Allah (s.a.w.a.) ).

Haƙiƙa ya tabbata a maganganun da suka gabata cewa babu wani al’amari daga Annabi (s.a.w.a.) (ko Alƙur’ani) wanda ke nuna cewa lamarin zaɓen halifa ana mai da shi ne ga “shura”, bil hasali ma dalilai masu ƙarfi daga Alƙur-’ani da hadisi suna nuna rashin ingancin barin wannan al’amari ga mutum guda kawai. Daga cikin abubuwan da suke nuna hakan kuwa shi ne cewa, wata rana Annabi (s.a.w.a.) ya kira wasu kafirai zuwa ga Musu-lunci amma sai suka kawo sharaɗin cewa sai in ya yarda bayan rasuwarsa, gudanar da al’amarin Musulunci zai koma hannunsu, amma sai ya amsa musu da cewa: “Wannan al’amari a hannun Allah yake, Yana ba wa duk wanda Ya so”[32].

Haƙiƙa babu kokwanto kuma an yi ittifaƙi kan cewa babu “nassi” kan wannan al’amari (wato jingina wannan lamari na halifanci ga “shura”), a dalilin haka ne ma ya sanya lamarin ya zamanto abin da babu jayayya a kansa. To amma abin tambaya a nan shi ne cewa, yaushe ne wannan ra’ayi na jingina lamarin halifanci ga “shura” ya faro?.

 

FARKON BAYYANAR RA’AYIN “SHURA

Malaman tarihi da masana hadisi gaba ɗayansu sun tabbatar da cewa Umar bn Khattab (r.a) shi ya ƙirƙiro wannan ra’ayi dab da rasuwarsa, babu wani abu makamancin haka kafin wannan lokacin.

Alƙurɗabi yana cewa, (bayan da ya gama magana kan mustahabbancin shura): “Haƙiƙa Umar bn Khattab ya mai da al’amarin halifanci (ya zama) “shura”[33].

Ibn Kathir yana faɗi dangane da ayar: ((…kuma al’amarinsu shawara ce a tsakaninsu….) cewa: “Su (sahabbai) ba sa aikata wani aiki face sai sun yi shawara don su amfana da ra’ayoyin ‘yan’uwansu, a wajen yaƙuƙuwa ko abin da ya yi kama da haka, kamar yadda Allah Ta’ala Yake ce wa Annabi (s.a.w.a.): (Ka nemi shawararsu a cikin al’amurra), a saboda haka ne ma Annabi (s.a.w.a.) yake neman shawarwarin sahabbansa a lokacin yaƙi da makamancin haka. Shi ya sa ma lokacin da (Halifa) Umar bn Khattab ya zo rasuwa sai ya sanya al’amarin halifanci a bayansa ya zama “shura”[34].

Dubi irin wannan canji mai girman gaske da aka samu a fagen halifanci kafin rasuwar (Halifa) Umar wanda ba ya da asali kafin wancan lokacin. Shin yaya aka yi wannan canji ya faru? Kuma don kare wace manufa?.

Umar (r.a) da kansa ya amsa wannan tambaya mai girman gaske a cikin mashahuriyar huɗubarsa da ta yi magana kan “Saƙifa” da abin da ya faru a cikinta, inda yake cewa: (Kada wani ya ruɗu don an ce zaɓen Abubakar da aka yi a matsayin halifa, fitina ce, haƙiƙa hakan ce, sai dai kawai Allah Ya kare mu daga sharrinta! Duk wanda ya yi bai’a wa wani (shugaba) ba tare da yardar sauran musulmai ba, ba za’a yi masa mubaya’ar ba haka shi ma wanda ya yi masa bai’ar…….)[35].

Amma mene ne dalilin wannan huɗuba, al-Ƙasɗalani ya yi bayani kan hakan inda ya warware rikice-rikicen da ke cikinta…

Bayan ya kawo “isnadin” wannan huɗuba kamar yadda Bukhari ya kawo daga Ibn Abbas (r.a) , sai ya ci gaba da cewa: Wata rana Abdurrahaman bn Awf ya zo wajen Ibn Abbas lokacin aikin hajji domin ya kasance yana koyon ilimin Alƙur’ani a wajensa, sai ya ce masa: (Shin ka ji abin da Amirul Muminina (wato Umar) yake cewa kuwa lokacin da labari ya zo masa cewa “wane” yana cewa haƙiƙa da Umar ya mutu da na yi bai’a wa “wane” domin kuwa mubaya’ar da aka yi wa Abubakar ba ta zamo komai ba face fitina, ko da jin haka sai Umar ya tashi zai yi huɗuba wa mutane don raddi wa wannan magana, to amma sai na hana shi saboda yawan mutane, sai na ce masa ya bari sai ya koma Madina ya faɗi duk abin da yake so….). Ko da suka koma Madina sai Umar ya tashi ya yi wannan huɗuba da aka ambata a baya……

Abin tambaya a nan shi ne, shin mene ne sunayen waɗannan mutane biyu da aka ƙi faɗin sunayensu, wato waɗanda a cikin hadisin aka musu laƙabi da “wane” da “wane”? Wanda za a yi wa bai’a da wanda zai yi masa.

Ya yin da wasu malamai suka gagara gano waɗannan sunaye biyu, sai ga shi Ibn Hajar al-Asƙalani ya gano haka ɗin ta hanyar wasu ruwayoyi da ya dogara da su, inda yake cewa: “Na gano hakan ne a cikin littafin al-Ansab na Balazuri daga Hisham bn Yusuf daga Muammar daga Zuhri cewa: (Umar yana cewa: “Labari ya zo min cewa Zubair yana cewa: (da Umar zai mutu da mun yi mubaya’a wa Ali)……….”)[36]!!

To wannan shi ne sirrin dalilin da ya sa Halifa Umar ya yi wannan canji a al’amarin halifanci. Kuma hakan shi ne sirrin abin da ya haifar da mahangan “shura” a al’amarin halifanci!. Wannan “shura”, wacce da yardar Allah za mu yi cikakken bayani kanta gwargwadon yadda wannan littafi zai ɗauka.

 

SHURA CIKIN SHINGENTA NA NAZARIYYA

Abu na farko da ya shafi wannan mahanga ta shura shi ne cewa al’amarin halifanci an bar shi ne a hannun mutane…..a nan ana iya bijiro da tambaya cewa, mene ne dalilin da yake nuna cewa an bar wannan al’amari a hannun mutane…kuma wani tsari ne shari’a ta tanadar don a bi wajen wannan zaɓen?

Masu wannan ra’ayi su kan kafa hujja da ayar nan ta: ((…kuma al’amarinsu shawara ce a tsakaninsu….)[37], a matsayin babban dalili don tabbatarwa da kuma kare wannan mahanga ko ra’ayi nasu. Don haka suke cewa, “shura” ita ce hanya ta farko wajen zaɓen halifa.

Da sannu za mu ga rashin ingancin wannan magana in muka yi la’akari da cewa wannan ra’ayi ba ya cikin tunanin sahabbai a wancan lokaci. Domin kuwa zaɓen halifa na farko ya saɓa wa wannan ƙa’ida ta “shura”, har ma Halifa Umar yake siffanta shi da “fitina”.

Haka nan zaɓen halifa na biyu (Umar) shi ma ya saɓa wa wannan ƙa’ida.

Haƙiƙa wannan ra’ayi na “shura” ya fara bayyana ne daga bakin Halifa Umar cikin sananniyar huɗuban nan tasa da ya ambaci abubuwan da suka faru a “Saƙifa” da kuma mubaya’ar da aka yi wa Halifa Abubakar, sannan daga ƙarshe ya tsoratar da mutane da kada a sake komawa gare ta, har ma ya ce: (Duk wanda ya yi mubaya’a wa wani mutum ba tare da yardar musulmai ba (shura), to kada ku yi masa mubaya’a, haka shi ma wanda ya zaɓa ɗin….)[38]. Wannan magana da muka kawo a baya, lalle (Halifa Umar) bai faɗe ta ba face sai don ya kange Ali (a.s.) (daga halifanci), sannan kuma ya hana mutane yi masa mubaya’a!

Amma abin mamaki lokacin da mutuwa ta zo masa sai ga shi yana neman mutum guda wanda zai zama halifa ba tare da neman shawarar jama’a ɗin ba, saɓanin wannan ƙa’ida ta “shura”!

An ruwaito shi yana cewa: “Da Abu Ubaida yana raye da na naɗa shi halifa”[39].

Sannan kuma yana cewa: “Da ace Salim Maula Abi Hudhaifa yana raye da na naɗa shi (halifa)”[40].

Sannan kuma ya ci gaba da cewa: “Da Mu’az bn Jabal na raye da na naɗa shi”[41].

A nan za mu gane cewa Umar (r.a) da kansa ba ya ganin “shura” a matsayin mafita ga al’amarin halifanci, ko da dai ya faɗi hakan a huɗubar tasa ta ƙarshe, amma bai yi aiki da ita ba sai da ya rasa wanda zai naɗa a matsayin halifa!

Haƙiƙa dab da rasuwarsa ya bayyana ra’ayinsa kan wannan al’amari na halifanci, inda yake cewa: ((Da dai Salim yana raye da ban mai da wannan al’amari na halifanci “shura” ba))[42].

To amma wace “shura” ce haka…..!!

Lalle wata irin “shura” ce da aka kange ta da wasu irin sharuɗɗa masu ban mamaki waɗanda suke ƙunshe da alamun tambaya! Ga su nan kamar haka:

1-        Shura” ce mai mutane shida, waɗanda shi kansa halifan ya ayyana su ba tare da shawartar jama’a ba.

2-        Dole ne halifan da za a zaɓa ya zamanto ɗaya daga cikin waɗannan mutane shida.

3-        Idan marasa rinjaye daga cikin shidan suka ƙi yarda da hukumcin masu rinjaye kan zaɓen wani mutum, to a sare wuyan marasa rinjayen.

4-        Idan mutane biyu (daga cikin shidan) suka zaɓi wani sannan wasu biyu kuma suka zaɓi nasu, to duk ƙun-giyar da Abdurrahman bn Awf -ɗaya daga cikin shidan - yake ciki ita ta yi galaba, idan da sauran za su ƙi yarda, to a sare kansu.

5-        Lalle ne kada lokacin yin zaɓen ya wuce kwanaki uku, in har ya wuce haka, to a sare wuyan dukkan mutane shidan.

6-        Suhayb al-Rumi shi zai kula da waɗannan mutane hamsin masu zartar da wannan hukumci (na sare wuya) ƙarƙashin ja-gorancin Abu Ɗalha al-Ansari![43].

A haƙiƙanin gaskiya, duk wanda ya dubi waɗannan sharuɗɗa, zai ga cewa ba’a ba wa al’umma daman faɗin albarkacin bakinsu cikin wannan lamari ba, face dai kawai shi halifan ne ya zaɓa musu wanda zai gaje shi a fakaice. Don haka babu yadda za’a kira wannan lamari “shura” tsakanin musulmai, ko kuma ma tsakanin “manyan mutane masu zartar da hukumci” (ahlul-halli wal-Aƙdi).

A gaskiya dai wannan tsari na “shura” ba shi da asali tun farko….domin hatta Halifa Abubakar (r.a) da kansa ba ya gani kuma bai yarda da cewa “shura” ita ce hanya mafi dacewa na tsarin mulki da zaɓen halifa ba, kuma ma bai yi aiki da hakan ba, face ma dai ya yi watsi da hakan lokacin da ya hana mutane (sahabbai) “haƙƙinsu” na zaɓan halifa, ya zaɓa musu Halifa Umar a matsayin halifansa, tattare da rashin amincewar da wasu manyan sahabbai suka nuna kan wannan zaɓen.

Ko da yake wannan rashin amincewan da waɗannan manyan sahabbai suka nuna ba wai a kan hanyar da aka bi wajen wannan zaɓen ba ne, domin kuwa ba su ce wannan al’amari (na zaɓen halifa) kamata ya yi a nemi shawarar jama’a ba, kuma babu wanda ya kafa hujja da ayar: ((…kuma al’amarinsu shawara ce a tsakaninsu….). Abin sani kawai shi ne cewa rashin amincewar nasu a kan zaɓen Halifa Umar shi kansa ne, inda suka ce wa Halifa (Abubakar): (Ka ɗora Umar a kan mutane tattare da ka san irin abin da suke ɗanɗana daga wajensa alhali kana tare da shi, to ina ga in ba ka nan? Me za ka ce wa Ubangijinka in Ya tambayeka kan bayinSa da ya bari a hannunka)[44]!.

Wannan abu a fili yake cewa hatta shi Halifa Umar ba ya ganin “shura” ita ce mataki na farko kana wanda ya dace kan wannan al’amari na halifanci, domin kuwa an ruwaito shi yana cewa: (Da Salim yana raye da ban sanya wannan al’amari (na halifanci) “shura” ba)[45]!!.

Haƙiƙa irin wannan yanayi, zai kawar da haƙƙin da al’umma suke da shi na faɗin albarkacin bakinsu gaba ɗaya, hatta ma waɗannan mutane da ake kira da masu ƙullawa da warwarewa (Ahlul-Halli wal-Aƙdi).

Suna cewa: Idan halifa mai ci ya zaɓi halifan da zai kasance a bayansa, shin wajibi ne sai an nemi yardar al’umma?

Sai suka amsa da cewa: Lallai bai’arsa ta tabbata, don kuwa yardar al’umma ba abin lura ba ne, dalilin hakan kuwa shi ne cewa: bai’ar da Halifa Abubakar ya yi wa Halifa Umar bai ta’allaƙa da yardar sauran sahabbai ba[46].

To idan har al’amarin haka ne, to ai “shura” ba ta da wani amfani ko tasiri wajen zaɓan halifa ke nan!!

Wataƙila wannan tunani ko ra’ayi shi ya sanya Ibn Hazmin yake fifita ra’ayin cewa halifa (mai barin gado) shi ya kamata ya zaɓi magajinsa kan ra’ayin “shura”, inda yake cewa: (Mun gano ingantattun hanyoyi na zaɓen shugaba, na farko wacce ta fi inganci da dacewa ita ce wanda shugaba mai barin gado zai zaɓi wanda zai gaje shi bayan rasuwarsa)[47].

 

SHURA KO TAKOBI ?

Haƙiƙa, mun riga mun fahimci faɗuwar mahangar “Shura” a dukkan ɓangarorinta, don haka sai muka dawo daga rakiyarta bayan an riga an tabbatar da ita. Lokacin da muka koma da baya don yin kwaskwarima wa abubuwan da suka faru a tarihi saboda irin karo da junan da ke cikin mahangar “shura”.

Ba mu tsaya a nan ba kawai, face dai sai da muka koma muna ƙoƙarin halatta waɗannan fuskoki masu karo da juna ba tare da wani keɓancewa ko togiya ba, kana kuma ba tare da komawa ga wani dalili na shari’a ba. Dalilinmu kawai a ko da yaushe shi ne: (ai hakan aikin sahabbai ne), duk kuwa da cewa mun san su sahabban basu haɗu a kan wani ra’ayi guda ba cikin waɗannan ra’ayuyyuka.

Kamar kuma yadda muka riga muka sani cewa saɓawan masu saɓawa daga cikin su (sahabbai) da kuma inkarin masu inkari daga cikinsu, bai amfanar da komai ba a gaban mulkin masu mulki.

Amma duk da sanin hakan, sai da muka dogara da abin da ya faru a lokacin, muka ba shi kariyar cewa dukkansu sun haɗu akan shi, muna masu cewa, in ba don sun haɗu akai ba kana da yardarsu ba, ai da bai yi aiki ba.

Da haka ne muka rufe ido daga haƙiƙa, wacce ta tabbatar mana cewa ai ƙarfin mulki ne ya haɗiye dukkan wani abin da ya saɓa masa na muryoyin waɗanda ba su yarda da shi ba. Wannan shi ne ƙarfin mulkin da ya faru a lokacin.

Duba ka gani, wani amfani aka samu daga inkarin da Banu Hashim da waɗanda suke tare da su na daga Muha-jirai da Ansarawa suka yi kan abin da “saƙifa” ta haifar?!

Kuma wace fa’ida ce aka samu kan inkarin da sahabbai suka yi wa Halifa Abubakar ranar da ya halifantar da Umar (r.a) ?!

Sannan wani amfani aka samu kan inkarin wasu abubuwa daga cikin al’amurran gudanar da mulki na Halifa Usman da sahabbai suka yi, kamar fifita Banu Umayya kan sauran manyan sahabbai tattare da abin da ke tare da Banu Umayya na son duniya da nisantan addini?!

Bayan haka, wannan inkari bai tsananta kuma ba’a ji shi sosai ba, har sai da ‘yan Banu Umayya suka yi galaba kan al’amurran jama’a da shugabanci tattare da ittifaƙin da dukkan malamai suka yi kan rashin tsantseni da ke tattare da waɗannan mutane, kamar su Marwan bn Hakam, Abdullahi bn Sa’ad bn Abi Sarh, Walid bn Uƙbah, Amru bn Aas, Muawiyyah da dai sauransu.

To amma duk da haka, mu a gurinmu wannan inkari nasu ba hujja ba ce, face ma sun kasance abin zargi ne!

Kana kuma yaushe ne ma inkarin nasu ya zamanto hujja, ballantana ma shurunsu ya zamanto yardarsu?!

Idan har hanya ta farko wajen gujewa “shura” ita ce ta a sallama al’amarin zaɓen shugaba (halifa) ga halifa mai ci don ya zaɓi duk wanda ya so, to haƙiƙa hanya ta biyu ta kasance mafi ɗaci sosai.

Haƙiƙa lokacin da waɗannan shuwagabanni suka gujewa tsarin “shura” da kuma “nassi”, sa’an nan suka zaɓi hanyar tirsasawa, kama karya da nuna ƙarfi, sai muka ɗauki wannan hanyar a matsayin ɗaya daga cikin hanyo-yin zaɓen halifa!

Alhali hanyar “shura” da ta takobi sun sha bamban ta kowace fuska babu abin da ya haɗa su!

Domin kuwa yarda da tsarin “tilastawa” karan tsaye ne ga tsarin “shura”! Kuma idan har tsarin “shura” yana da madogara cikin Alƙur’ani, to ina tsarin “tilastawa” kuma ya samo nasa asalin?!.

To daga nan kuma ana iya bijiro da tamabaya kamar haka:

Idan har Alƙur’ani mai girma shi ya zo da tsarin “shura” to mene ne hukumcin halifancin da aka samar da shi ta hanyar da ya saɓa wa wannan tsari na “shura”?!

To a lokacin da muka gagara samun wata gamsasshiyar amsa da za ta kuɓutar da wannan mahanga daga wannan ɗumbin matsaloli, don haka abin yi kawai shi ne dole ne mu halatta dukkan hanyoyin da suka gabata wajen zaɓen halifa: wato, wani lokaci ta hanyar mubaya’ar mutane biyar, wani lokaci kuma ta hanyar halifa mai ci ya zaɓi magajinsa, wani lokaci kuma ta hanyar mutane shida don su zaɓi ɗayansu, wani lokaci kuma ta hanyar tilasci da kama karya, ta yadda har wannan hanya ta ƙarshe ta mai da al’amarin halifanci ya zamanto wani lamari na gado babu wani tasiri na addini a cikinsa.

 

MAKOMAR SHARUƊƊAN SHUGABANCI:

Haƙiƙa wannan hanya da aka bi wajen kuɓutar da hanyoyin da aka bi wajen zaɓen halifa ba kawai zai ruguza wannan tsari na “shura” ba ne, har ma zai shafi muhimman sharuɗɗan zaɓen halifa, wanda daga cikinsu akwai:

1-      Kiyaye Dokokin Allah (al-Adala): Malamai sun tafi kan cewa: shugabancin fasiƙi ba ya inganta, domin yana daga cikin aikin shugaba kare mutane (musulmai) daga saɓon Allah. Domin a fili yake cewa mutum fasiƙi wanda bai kula da kansa ba yaya za’a yi ya kula da waninsa[48]?!

Malaman sun ci gaba da cewa: Fasiƙanci yana hana shugabanci, haka ma idan fasiƙanci ya bijiro masa ko da kuwa bayan an yi masa mubaya’a ne[49], to zai kawar da shugabancin.

2-      Ilimi (Ijtihadi): Yana daga cikin sharuɗɗan shugaba ya kasance sama da kowa wajen ilimi da sanin ya kamata, abin nufi a nan shi ne ilimi mai zurfi da zai iya ciro hukumce-hukumce daga muhallinsu. Saboda haka, shugabancin maras ilimi ba ya inganta, don kuwa ana buƙatarsa da ya tsara al’amurran da za su kai mutane ga tsira, sannan ya tsayar da haddodi, shiga tsakanin mutane yayin husuma da dai sauransu. Haƙiƙa in kuwa bai zama masani ba, babu yadda hakan za su samu[50].

Amma an rasa waɗannan sharuɗɗa lokacin da wasu marasa waɗannan suka ɗare karagan halifanci, babu adala, kana kuma babu ilimi mai zurfi na ijtihadi.

Ko da yake Farra’i yana cewa: (An ruwaito wata magana daga Ahmad da take rushe wannan sharaɗi na “adala”, ilimi da fifiko, inda yake cewa: “Ba ya halatta ga wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya yi tawaye ga wani shugaba (halifa), mutumin kirki ne ko fajiri, matuƙar dai ya hau karagar halifanci kuma an kira shi “Amirul Muminina”, ko da kuwa da ƙarfi ya kwata”)[51]!

Al-Ƙalƙasandi ma yana cewa: (Mu a gurinmu (‘yan shafi’iyya) yana inganta fasiƙi ko jahili ya zama halifa ko da kuwa da ƙarfi ko kama karya ya hau halifancin)[52].

 

NEMAN MAFITA:

Dole ne a sama wa wannan ra’ayi na inkarin sharuɗɗan halifanci da asasinsa mafita karɓaɓɓiya. Ba wata mafitar da wannan ra’ayi ya kawo face kawai lalura!

Domin in mun ce: shugabancin fasiƙi ko jahili ba ya inganta, to hakan ya kan wajabta rushewar duk hukumce-hukumce da ya yi, don haka ya hau kan halifa da ya zo a bayansa ya gyara dukkan waɗannan hukumce-hukumce su yi dai-dai da shari’a[53].

Ya ci gaba da cewa, hankali ma yana wajabta mana yarda da halifancinsa don kiyaye tsarin shari’a da kuma gudanar da hukumce-hukumce[54], sabili da dole ne musulmi su kasance suna da shugaba[55].

Don haka yarda da hakan yana wajabta gaggauta kawarwa da kuma komawa da wannan lamari zuwa ga matsayinsa na shari’a a duk lokacin da al’umma ta sami daman hakan.

Wannan shi ne ma abin da Shaikh Muhammad Rashid Rida ya tafi akai, inda yake cewa: (Matsayin hawa mulki da ƙarfi kamar matsayin cin mushe da kuma naman alade ne ya yin lalura, ana samunsa ta hanyar ƙarfi ne, kana hawa mulki da ƙarfi ya fi zama cikin rashin tsari!.

Kana ya zama wajibi a kawar da wannan tsari a duk lokacin da aka samu dama, wato ba ya halatta a ci gaba da zama haka, don kar ta zamo abin wasa tsakanin azzalumai, kowa yana cafo ta yadda ya ga dama[56].

Amma a gaskiya al’amarin saɓanin haka ne, domin kuwa sun haramta yin tawaye wa duk wani jā’iri ko fasi-ƙin shugaba, har ma suna ganin yin tawaye a matsayin babban fitina da addini ya hana yin sa da kuma shiga cikinsa……

Al-Zarƙāni yana cewa: (Amma Ahlussuna sun tafi kan cewa: “zaɓen shugaba mafifici kuma adali shi ya fi, amma in an rasa hakan, to haƙuri ƙarƙashin jā’irin shugaba shi ya fi dacewa kan ayi masa tawaye, hakan kuwa saboda abin da ke cikin tawayen na tashin hankali, kashe-kashe da keta haddin mutane, wanda hakan shi ya fi haɗari kan zama ƙarƙashinsa)![57].

Haka ma an ruwaito Ahmad bn Hambal yana cewa: (Kada ku yi bore wa shugabanni ko da kuwa suna zalunci, domin ɗa’a wa shugaba dole ne, adali ne ko jā’iri.)[58]

Dangane da waɗannan maganganu guda biyu, Shaikh Abu Zuhra yana cewa: (Wannan shi ne abin da aka ruwaito (wato shi ne ra’ayin) shugabannin mazhabobin Ahlus sunna: wato Malik, Shafi’i da Ahmad)[59].

To abin tambaya a nan shi ne, shin wannan ra’ayi ya yi dai-dai da hukumcin aikata haram lokacin lalura ko tilasci (kamar yadda ya zo a baya)?!

Haƙiƙa Shaikh Muhammad Rashid Ridha ya soki wannan aƙida, inda yake cewa: (Haƙiƙa jā’iran shuwa-gabanni sun mai da hankali wajen jawo malamai gare su ta hanyar ba su dukiya da muƙamai, don haka suka ƙirƙiro wata ƙā’ida wacce ta saɓa wa dokokin Musulunci a lamur-ran duniya da na addini ba don komai ba sai don kare kansu tare da waɗannan shuwagabanni. Wannan ƙā’ida kuwa ita ce cewa: Ba dole ba ne sai shugaba ya cika sharu-ɗɗan da Alƙur’ani ko hadisai suka wajabta masa, ko da kuwa malamai sun dage kan hakan, inda suka ƙara da cewa: yana halatta ne in an rasa waɗanda suka cika waɗannan sharuɗɗa.

Kamar dai yadda muka sani ne, ilimi mai zurfi na ijtihadi yana daga cikin sharuɗɗan shugabanci, amma abin mamaki sai ga shi waɗannan malamai suna halatta bin jahili har ma su kan sanya shi a babin lalura. Wanda yin hakan ya taimaka wajen halakan al’umma saboda miƙa wannan al’amari da suka yi ga waɗanda ba su cancanta ba. Daga cikin alamun wannan halakar kuwa akwai: bayyanar rashin amana, cuta da dai sauransu. Lalle babu cin amanar da ta wuce barin al’amarin (shugabanci) ga jahilai…….

Muslim da Abu Dawud sun ruwaito daga ibn Abbas cewa: (Duk wanda ya wakilta wani daga cikinku (musulmai) kan wani al’mari tattare da ya san akwai wanda ya fi cancanta kan hakan, kuma ya fi sanin Alƙur’-ani da hadisi, haƙiƙa ya ha’inci Allah da ManzonSa da kuma dukkan musulmai)[60].

Wannan malami ya ci gaba da sukan wannan aƙida, inda yake cewa: (Babu abin da ya cutar da wannan al’umma kamar wajabta biyayya kai tsaye ga waɗannan lalatattu kuma azzaluman shuwagabanni, halatta nuna fin ƙarfi wajen ƙwatan mulki da kuma tilasta mutane da waɗannan azzaluman shugabanni suke yi don mubaya’a wa ‘ya’yansu ko makusantansu)[61].

Haƙiƙa waɗannan abubuwa ne da suka faru a tarihi ba kawai ƙirƙirarru ko wulaƙantattun abubuwa ba ne.

 

ABUBUWA BIYU:

Kafin mu ci gaba, za mu ɗan leƙa wasu abubuwa guda biyu……

 

Abu Na Farko: Tafarkin Magabata?!

Haƙiƙa an shafe koyarwar da yawa daga cikin magabata, ba’a ko jin sunayensu don haka ba’a san koyar-warsu dangane da wannan al’amari ba.

Misali, ba’a ambaton Shugaban shahidai Imam Husain bn Ali (a.s.) da irin tawayen da ya yi wa azzalu-mai[62]….haka ma ɗumbin Muhajirai da Ansarawa da sauran sahabbai da irin tawayen da suka yi wa Yazid ibn Mu’awi-yyah[63]…haka ma Abdullahi bn Zubair….haka ma Shahid Zaid bn Ali bn Husayn….haka ma sahabin nan Sulaiman bn Surad al-Khazza’i da mabiyansa ma’abuta yunƙurin (Tawwabin)….haka kuma mahaddata Alƙur’anin nan a garin Kufa da boren da suka yi.

Haka ma an watsar da koyarwar Abu Hanifa daga tsakanin shuwagabannin (mazhabobin) Ahlus sunna. Hakan ya faru ne – kamar yadda ya zo cikin wasu littat-tafa- saboda yana ƙarfafa masu tawaye wa halifofin ƙarya kana ya ƙarfafa Shahid Zaid ibn Zainul Abidin (a.s.) haka ma ya goyi bayan tawayen da ‘ya’yan Imam Hasan (a.s.) suka yi, domin kuwa har ya rasu a kurkuku yana mai nuna ƙauna gare su….ya kasance yana kiran halifofin Banu Abbas da Banu Umayya da sunan ‘yan fashi[64].

Duk waɗannan malamai an watsar da koyarwarsu dangane da wannan mas’ala, sannan kuma ma an cire su daga da’irar Ahlus sunna!!.

Haƙiƙa wasu manyan malaman tauhidi masu kiran kansu Ahlus sunna sun kai wani matsayi na cin mutumcin waɗannan manyan bayin Allah. Daga cikinsu (waɗannan malaman) akwai irin su Ibn Taimiyyah wanda ta’asubanci da son kai ta ɗebi shi har ya kai matsayin yin karen tsaye wa dokoki da tsare-tsaren Musulunci. Inda yake siffanta boren da Shugaban shahidai kana kuma jikan Manzo kana abin ƙaunarsa (Imam Husain) ya yi wa Yazid a matsayin ɓarna mai girma wanda wai Allah da ManzonSa basu yarda da ita ba, haka nan ne ya siffanta boren da sauran Muhajirai da Ansar suka yi a Madina. Duk da wulaƙantawa da kashe waɗannan mutane da Yazid ya yi amma sai da ya kai matsayin nema masa uzuri da cewa ya yi hakan ne don kare mulkinsa. Bai yi inkarin Yazid ba sai dai kawai don ya halatta Madina na kwanaki uku[65].

Dangane da wannan al’amari, ya ci gaba da cewa: Daga abin da ya shafi wannan babi, ya kamata a gane cewa mai yiwuwa ne a sami wani mutum cikin manyan masana addini daga cikin sahabbai ko tabi’ai ko wanda suke biye musu har zuwa tashin ƙiyama, Ahlul baiti ne ko waninsu, ya kawo wani ra’ayi (ijtihadi) da ke tattare da zato da kuma wani nau’i na son zuciya ɓoyayyiya, a wannan hali ba zai yiwu a bi shi ba ko da kuwa yana daga cikin bayin Allah na gargaru. Haƙiƙa in irin haka ya faru, fitina ta auku[66]!!.

Ya ɗan’uwana (mai karatu), shin mene ne zai sa Ibn Taimiyya ya fi waɗannan manyan mutane daga sahabbai da Ahlul baiti sanin haƙiƙanin fitina da kuma nesata daga son zuciya? Me ya kawo haka? Shin saboda shi ya yarda da shugabancin fājiri ko jahili, sannan su kuma waɗancan suka ƙi yarda ne?!

Ta haka ne wannan mahangar ta jefa kanta cikin ɗimauci da damuwa, yayin da ta yi watsi da tarihi mai yawa na manyan magabata da Imamansu.

 

Abu Na Biyu: Tawayen Da Ke Da Lada:

Matuƙar dai wannan hukumci, da ke nuna saɓa wa shugaba haramun ne, sannan fita don yaƙansa fitina da ɓarna mai girma ce, yana nan daram….to me ya sa wanda ya fito don yaƙan Imam Ali (a.s.), wanda hakan shi ne na farko a tarihin halifanci, yake da lada (bai kasance abin tuhuma ba)?!

Wato ke nan lokacin shugabancin Imam Ali (a.s.) – wanda ya fi kowa kusanci da Annabi (s.a.w.a.) kuma ya fi kowa ilimi, jihadi da iya shugabanci – ne kawai ya halatta mutane su yi bore wa shugabansu!

A nan fitowarsu (don yaƙan shugabansu) a wannan lokaci – bai zamanto fitina da ɓarna ba, face ma sai cewa ake wai “ijtihadi” ne kuma ma suna da lada ko da kuwa sun yi kuskure!!!

Da za’a bijiro da kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ( da suka gabata) kan wannan mahanga (ta “shura”) da kuwa za’a samu wata irin darewa da ba za ta iya ɗinkuwa ba sai dai in za’a bi ta wata bauɗaɗɗiyar hanya mai nisan gaske.

To yanzu kuma bari mu koma kan kishiyar wannan mahanga….


 


[1] . Surar Baƙara: 2: 233.

[2] . Surar Baƙara:2:233.

[3] . Duba Tafsirin Ibn Kathir, juzu’1 na 1 shafi na 285, Fatahul Ƙadir, juzu’i na 1 shafi na 246, Tafsirin al-Mizan, juzu’i na 2 shafi na 253.

[4] . Surar Aali Imaran: 3:159.

[5] . Surar Aali Imrana: 3: 159.

[6] . Surar Aali Imarana: 3:159.

[7] . Fathul Ƙadir, Juzu’i na 1 shafi na 393.

[8] . Durrul Mansur, juzu’i na 2 shafi na 358.

[9]. Kamar na sama.

[10] . Tafsirul Razi, juzu’i na 9 shafi na 66.

[11] . Tarikh al- Tabari, juzu’i  na 2 shafi na 566 daga al-Waƙidi.

[12] . Sirat ibn Hisahm, juzu’i na 3 shafi na 37, Tarikh al-Tabari, juzu’i na 2, shafi na 573 daga al-Zuhri.

[13] . Tabari juzu’i na 2, shafi na 637 daga Zuhri.

[14] . Muhammad Ammara, al-Khilafa wa Nash’atul Ahzab al-Islamiyya, shafi na 54.

[15] . al-Khilafa wa Nash’atul Ahzab al-Islamiyya, shafi na 57.

[16] . al-Khilafa wa Nash’atul Ahzab al-Islamiyya, shafi na 58.

[17] . Dubi al- Bidayah wan Nihayah, juzu’i na 3 shafi na 34-38, al-Isti’ab, Usudul Gaba, al-Isabah da dai sauransu

[18] . al-Khilafa wa Nash’atul Ahzab al-Islamiyya, shafi na 53.

[19] . Tafsirul Razi, juzu’i na 9 shafi na 66.

[20] . Surar Aali Imrana: 3:159.

[21] . Durrul al-Manthur, juzu’i na 2, shafi na 359.

[22] . Kamr na sama, juzu’i na 7, shafi na 357.

[23] . Kamar na sama.

[24] . Musnad Ahmad, juzu’i na 5, shafi na 274.

[25] . Kamar na sama, shafi na 321.

[26] . Surar Shura: 42:38.

[27] . Surar Shura: 42: 36-39.

[28] . Al-Mizan fi Tafsirul Ƙur’an, juzu’i na 18, shafi na 65, ayar kuma tana cikin Sura ta 39: aya ta 18.

[29] . Durrul Manthur, juzu’i na 7, shafi na 357.

[30] . Durrul Manthur, juzu’i na 7 shafi na 357, inda ya ce Khatib ma ya ciro shi cikin (Ruwatu Malik).

[31] . Lisanul Mizan, juzu’i na 3, shafi na 78 da kuma 284.

[32] . Insanul Uyun, juzu’i na 2 shafi na 154.

[33] . Tafsirul Ƙurɗabi, shafi na 161-162.

[34] . Tafsir ibn Kathir, juzu’i na 4, shafi na 119.

[35] . Sahih Bukhari, cikin Kitabul Hudud, babin jefe mai ciki in ta yi zina, hadisi na 6442, Musnad Ahmad, juzu’i na 1 shafi na 56, Sirat ibn Hisham, juzu’i na  4, shafi na 308, Tarikh al-Tabari, juzu’i na 3, shafi na 200.

[36] . Muƙaddimat Fathul Bari fi Sharhil Bukhari, shafi na 337, al-Ƙastalani cikin Irshadul Sari li sharhil Bukhari, juzu’i na 10, shafi na 19.

[37] . Surar Shura: 42:38.

[38] . Sahih Bukhari – Kitabul Muharibin, juzu’i na 7, hadisi na 6442, Musnad Ahmad juzu’i na 1, shafi na 56, Sirat ibn Hisham, juzu’i na 4, shafi na 308.

[39] . Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu’i na 3, shafi na 65, Saffatul Safwat, juzu’i na 1, shafi na 367.

[40] . Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu’i na 3, shafi na 65, Sifatus Safwa, juzu’i na 1, shafi na 383, Ɗabaƙat ibn Sa’ad, juzu’i na 3, shafi na343.

[41] . Sifatus Safwa, juzu’i na 1, shafi na 494.

[42] . Ɗabaƙat ibn Sa’ad, juzu’i na 3, shafi na 248

[43] . Al-Kamil fi al_tarikh, juzu’i na 3, shafi na 66-67.

[44] . Al-Kamil fi Tarikh, juzu’i na 2, shafi na 425.

[45] . Ɗabaƙat ibn Sa’ad, juzu’i na 3, shafi na 248.

[46] . Ma’athar al-Imamah 1: 52, al-Ahkam al-Sulɗaniyya na Mawardi: 10, al-Ahkam al-Sulɗaniyya na al-Farra’: 25-26.

[47] . Al-Fasl, juzu’i na 4, shafi na 169.

[48] . Ma’athiril Inafat, juzu’i na 1, shafi na 36, al-Ahkamil Sulɗaniyya na al-Mawardi, shafi na 6, al-Ahkamil Sulɗaniyya na al-Farra’i shafi na 20.

[49] . Al-Ahkamil Sulɗaniyya na al-Mawardi, shafi na 17.

[50] . Ma’athiril Inafat, juzu’i na 1, shafi na 37, al-Ahkamil Sulɗaniyya na al-Farra’i shafi na 20.

[51] . Al-Ahkamil Sulɗaniyya na Farra’i, shafi na 20.

[52] . Ma’athiril Inafat, juzu’i na 1, shafi na 58.

[53] . Ma’atharil Inafat, juzu’i na 1, shafi na 58.

[54] . Ma’atharil Inafat, juzu’i na 1, shafi na 71.

[55] . Al-Ahkamil Sulɗaniyya na Farra’i, shafi na 24.

[56] . Al-Khilafa, shafi na 45, Nizamul Hukm wal idara fil Islam, shafi

na 126.

[57] . Sharhul Mawatta, juzu’i na 2, shafi na 292, al-Mazāhibul Islamiyyah, shafi na 155.

[58] . Al-Mazāhibul Islamiyyah, shafi na 155.

[59] . Al-Mazāhibul Islamiyyah, shafi na 155.

[60] . Tafsirul Manār,juzu’i na 5, shafi na 215-216.

[61] . Al-Khilafa, shafi na 51, Nazariyatul Hukm wal Idara fil Islam, shafi na 127.

[62] . An kashe Imam Husain (a.s.) da mutanen gidansa da sahabbansa su saba’in da biyu, cikinsu har da sahabi Anas bn Harith, wanda ya ruwaito Annabi (s.a.w.a.) yana cewa: “Wannan ɗa nawa – Husain – za’a kashe shi a wani wuri da ake ce masa karbala, don haka daga cikinku duk wanda ya riski wannan lokaci to ya taimake shi”, Al-Bidayah wan Nihayah, juzu’i na 8, shafi na 201, Usudul Gāba, al-Isabah

[63] . Daga cikinsu an kashe sahabbai 80 daga wanda suka je yaƙin Badar, daga cikin Ƙuraishawa kuwa mutane 700 daga Tabi’ai sauran larabawa kuwa 10,000.

Duba cikakken bayanin wannan waƙi’a ta al-Harra cikin al-Muntazim na ibn Jawzi, Tarikh al-Tabari ƙarƙashin babin abin da ya faru cikin shekara ta 63 bayan hijira, dubi Tarikh al-Khulafa’ na Suyuti, shafi na 195.

[64] . Al-Milal wan Nihal, juzu’i na 1, shafi na 140, al-Kashshaf na Zamakshari, ƙarƙashin aya ta 124 na Surar Baƙara ((AlƙawariNa ba zai samu azzalumai ba)).

[65] . Dubi: Minhajus Sunna, juzu’i na 2, shafi na 241-243 da kuma shafi na 253, al-Wasiyyatul Kubra, shafi na 54.

[66] . Minhajus Sunna, juzu’i na 2, shafi na 245.

عنوان الکتاب