GABATARWA |
||
|
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
GABATARWA:Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Manzo Muhammadu (s.a.w.a) tare da tsarkakan Mutanen gidansa da kuma sahabbansa zaɓaɓɓu. Bayan haka:- Sanannen abu ne cewa dukkan wani shugaba daga cikin shuwagabanni ba ya yiyuwa ya bar mutanensa da mabiyansa ba tare da ya bar mai kula da su ba a lokacin da ba ya nan. A saboda haka ne suke tunani da kuma ayyana wanda zai tsaya a matsayinsu wajen gudanar da muhim-man ayyuka ko da kuwa gajeruwar tafiya ce za su yi. Idan har barin al’umma sakaka (ba tare da shugaba ba) ba zai yiwu ba daga wajen sauran shuwagabanni, to ba ya yiwuwa ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bar al’ummarsa haka kawai ba tare da halifa ba domin shi ne shugaban masu hankali, fiyayyen halittun farko da na ƙarshe, kuma shari’arsa ita ce mafificiyar shari’a, kuma shi ga muminai rahimi ne mai tausayi. Saboda haka dole ne ya damu da wannan al’amari (na halifanci) sama da waninsa. A saboda haka dole ya zaɓa wa al’ummarsa shugaba wanda zai gaje shi. Babu shakka cewa a halin yanzu al’umman nan ta rasa Manzon Allah (s.a.w.a.), amma duk da haka tana iya tuna abin da ta gani ko ta ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dan-gane da wannan al’amari (na halifanci) lokacin rayuwarsa, musamman ma a ƙarshen rayuwarsa. Sun kasance masu kiyaye waɗannan maganganu(wasiyya) na Annabi(s.a.w.a) dangane da halifanci har zuwa wannan zamani namu. Shin wannan wasiyya ta halifanci da suka ji kuma suka kiyaye tana nuni da wani mutum ne guda ko kuma tana nuni da cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bar al’amarin halifancinsa ne a hannun mutane don su zaɓi wanda zai zama halifa a bayansa? A taƙaice dai shin ginshiƙin Imamanci da halifanci “Nassi” ne daga Allah ko kuma “Shura” (zaɓe daga mutane) ce? Amma idan muka karanta tarihi da kyau, to za mu ga cewa waɗannan abubuwa guda biyu (wato Nassi ko Shura) babu su a zaɓen halifanci!. Wannan kuwa saboda abin da ya faru ne lokacin zaɓen halifa bayan rasuwar Annabi (s.a.w.a), inda wasu jama’a daga “Ansar” (muta-nen Madina) da wasu mutane kaɗan na “Muhajirai” (mutanen Makka) suka taru a “Saƙifa” don zaɓen halifa a daidai lokacin da sauran musulmai musamman Ahlul baiti da Banu Hashim suke cikin tsananin baƙin ciki saboda rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma ƙoƙarin jana’izarsa. Abin mamaki duk da ƙarancin mutane a wannan wuri na Saƙifa abin da aka zartar (mubaya’a) bai samu yardar dukkanin mutanen da suke wurin ba sai dai ma faɗa ce ta yi ƙoƙarin tashi a gurin (ko ma ace ta tashi), kamar yadda Halifa Umar ya siffanta ta da cewa “fitina ce wacce Allah Ya kare mu daga sharrinta”. Wannan ya nuna mana ke nan cewa ba’a samu shura ba tsakanin mutanen Saƙifa (dangane da wanda aka zaɓa) ballantana ma waɗanda basu je gurin ba kuma suka ƙi yarda da abin da aka zartar , wato Ahlul baiti da magoya bayansu da kuma dukkan Bani Hashim, haka Umayyawa ma kamar yadda shugabansu ya nuna. Wannan shi ne haƙiƙanin abin da tarihi ya nuna bayan “Taron Saƙifa”. Amma saboda ƙoƙarin kiyaye taron saƙifa da kuma matsayin magabata, sai ga shi an yi ƙoƙarin a tabbatar da halifanci ta hanyar “shura” amma lokacin da hakan ya gagara, don abubuwan da suka faru a wajen kamar yadda muka yi nuni da shi, ba makawa sai aka koma ga “nassi”……… To a daidai wannan lokacin ne za mu iya bincike kan cewa shin wane ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zaɓa a matsayin halifansa? Wannan littafi da za mu gabatar zai yi magana ne a kan wannan mas’ala bayan da muka yi bincike mai zurfin gaske da kuma tattaunawa ta ilimi tsakanin mutanen da suke ganin cewa halifanci ta hanyar “shura” ake tabbatar da shi da kuma waɗanda suke ganin cewa ta hanyar “nassi: ake tabbatar da shi, tattare da kawo hujjoji masu ƙarfi da dukkan ɓangarorin biyu suka dogara da su, da kuma bayanin wanne ne abin riƙo da na jefarwa tsakanin biyun. Mun bar wa mai karatu ko mai bincike (kan wannan mas’ala) ‘yancin zaɓen abin da ya dace daga sakamakon wannan bincike wanda aka samo daga ingantattun littattafai. Allah Shi ne Mai shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. MARKAZ AR-RISALA
SHINFIƊA:A na ƙirga matsalar (Ginshiƙin Tsarin hukumci a Musulunci) cikin manyan matsalolin da har yanzu musul-mai ba su tantance maganganu a kai ba…… Wannan matsalar tana ɗaya daga cikin manyan mish-kilolin mazhaba da a ko da yaushe ake bijiro da su, matsa-yinta kamar sauran ‘yan’uwanta ne na daga mishkilolin tarihi da kuma aƙida. Duk maganganun da ake yi ba a kan asalin tsarin ba ne, domin babu yadda mutum zai yi tunanin cewa al’umma za ta iya rayuwa ba tare da tsari ba ko kuma tsari ba tare da shugabanci ba…. Manyan malumman fiƙihu da falsafa tun a zamanin da sun yi maganganu a kan wannan lamari. Misali: - Ahmad bin Hambal ya fassara fitina da cewa ita ce halin rashin shugaba a tsakanin mutane wanda zai kula da al’amurorinsu. - Mas’udi kuwa nuni ya yi da buƙatuwar addini ga mulki da kuma buƙatar shugabanci ga addini, har ma yake ganin cewa ɗaya ba ya wadata sai da ɗayan. - Ibn Hazmi yana ganin cewa wannan sanannen abu ne domin kuwa ci gaban addini ba zai yiwu ba tare da samuwar shugaba wanda zai gudanar da wannan tsarin ba. - Ibn Khaldun ya fassara wannan tsarin da cewa wani irin dokoki ne na siyasa wanda dukkan jama’a suka yarda da shi kuma suke bin sa sau da ƙafa, ƙarfi da ɗaukakan ƙasa yana faɗuwa a lokacin da ta rasa wannan tsari ((Sunnar Allah cikin waɗanda suka shuɗe gabanninka, kuma ba za ka sami musanyawa ba ga sunnar Allah)).. To koma dai mene ne, daman tun lokacin rasuwar Annabi (s.a.w.a) musulmai sun kasance masu aiki da wan-nan tsari a matsayin abin da ya zama wajibi. To amma maganganu da suke kai komo a kan ainihin asasin wannan tsarin ne…wato ta yadda shi shugaban tsa-rin zai kai ga martabar shugabanci… A sabili da haka waɗansu sun yi ƙoƙarin su nuna cewa tsarin shugabanci a Musulunci shi ne ta hanyar “shura” saboda dogaro da suka yi da irin waɗannan abubuwa da suka faru a tarihin siyasa tun farko. Sun ciccika littattafan aƙida da na hukumce-hukumce (da irin waɗannan magan-ganu) don a sama wa wannan aƙida ta “shura” matsuguni a addini daga Alƙur’ani mai girma da kuma sunna. Duk hakan kuwa yana zagayawa ne kan halifancin farko na Manzon Allah (s.a.w.a.)..inda aka tsatstsara wasu mahanga guda biyu – mahanga ta tarihi da kuma ta aƙida – duk dai don tabbatar da wannan aƙida da kuma sama mata gindin zama… To amma abin tambaya a nan shi ne, shin wannan tafarki na “shura” ya iya kawo ƙarshen wannan matsala ta tsarin shugabanci, wato mafita ta ƙarshe daga irin tamba-yoyin da ya dabaibaye shi? Shin an iya tabbatar da shura a matsayin tsari na zaɓen halifan Annabi (s.a.w.a) ? Shin “shura” tana iya magance duk wata mishkilan tsarin hukumci ko shugabanci a Musulunci? Shin wannan aƙida za ta iya tunkuɗe duk wani abin da za’a iya bijiro mata ta ɓangaren “nassi” ko isa ga mulki ta hanyar ƙarfi da dai sauransu? Shin wani nasara aka samu cikin dukkan waɗannan yanayi? Kana mene ne ƙarfin sauran ra’ayuyyukan da suke fus-kantar wannan ra’ayi na “shura” wajen ayyana asasin tsarin mulki a Musulunci? Haƙiƙa akwai al’amurra da yawan gaske da za su fito daga waɗannan tambayoyi waɗanda suka kewaye wannan lamari da muke magana a kai. Waɗannan al’amurra kuwa sun ginu ne kan dalili na ilimi da kuma hankali waɗanda ba sa ma buƙatuwa da yin tawilin nassosi, kana kuma suna iya canza wannan aƙida da kuma ruguza ta. Don haka an kasa wannan bincike ne kashi biyu; kashin farko ya yi bayani ne kan aƙidar “shura” da abin da ta ƙunsa cikin Alƙur’ani mai girma da kuma hadisai, sannan ya ci gaba da bayanin haƙiƙanin “shura” cikin tarihi da siyasar addini. Kashi na biyu kuwa ya yi bincike ne kan aƙidar “nassi” da abin da ta ƙunsa. Hakan kuwa don a isa ga abin da ake so a fitar wato natija.
((Allah Shi ne mai shiryarwa zuwa ga madaidaiciyar hanya)).
|
||