Haihuwarsa da Tasowarsa

 

  Babu shakka Mumbarin Marigayi Imam Khu’i a cikin sama da rabin Karni ya horar da gwarzaye fitattu gogaggu wadanda suka zamanto su ne mafiya hazaka da daukakar baiwa a fagen musulunci da fannonin ilimi da al’amura babam-daban da Kuma matakan Musulunci masu muhimmanci, yayin da ya tarbiyyantar da daruruwan mamsanan fikihu da mujtahidai da ma’abuta daraja da daukaka wadanda suka dauki nauyin ci gabar da tafarkin musulunci da hidima da ilmantarwa, da Kuma al’amuran zamantakewa wadanda yawancinsu a yau su ne mafi yawan malaman makarantu da cibiyoyin ilimin addinin musulunci musamman ma a garin Najaf da Birnin Kum Mai tsarki wadanda suka kai matsayin wadatarwa da shahara a ilimi da halin zaman jama’a, hakan kuma ya ba su damar cancantar daukar nauyin tarbiyyantarwa da koyarwa da matsayin Marja’i da al’umma ke komawa gare su don sanin hukunce-hukunen shari’a, da matsayin Jagoranci da tafi da al’umma a wannan zamanin.

Daga cikin wadannan fıtattun gawarzayen akwai Ayatullahil Uzma Aliyu Sistani, Wanda shi yana daya daga manyan daliban Imam Khu’i (R.A.),a kamala da ilimi da falala da dacewa. Abinda ke biye takaitaccen tarihin rayuwarsa ne:-


 

Haihuwarsa da Tasowarsa

An haifi mai martaba Ayatullahil Uzma Aliyu
Sistani ne a garin Mashhad birnin da Makwancin Imam Ridha (A.S.) Imami na takwas daga zuriyar gidan Manzo (SAWA) yake a shekarar 1349 Hijriyya, a watan Rabi’ul Awwal, wato shekarar 1931 Miladiyya.

Bayan ya kammala karatunsa na elemantare da mukaddima da na marhalar tsakatsaki nan da nan sai ya ci gaba da bibiyar darrusan aiki da hankali da kuma fannin sanin Ubangiji a gurin manyan malamai masanan wadannan fannoni kuma masu koyar da su; har ya samu ya dandake su da kyau. Daga bisani sai ya shiga marhalar karatun share fagen ijtihadi a nan garin Mashhad inda ya amfana daga irin ra’ayin Malami mai yawan sani kuma ma’abucin binciken nan Allama Mirza Mahadi Isfahani (R.A.). Daga nan kuma sai ya tashi takanas zuwa makarantar ilimin addini da ke garin ilimi na birnin Kum a zamanin babban malami kuma Marja’i Sidi Husaini Burujurdi (R.A.) a shekakar 1368 Hijiriyya wato shekarar 1948 Nasariyya inda ya halarci darusan manyan malamai ma’abuta daraja ciki har Ayatullah Burjurdi a fannonin fikihu da Usuli kuma ya amfana sosai daga kwarewarsa a fannin fikihu da kuma irin ra’ayinsa a ilimin sanin maruwaitan hadisi, da fannin hadisin kansa kamar kuma yadda ya halarci darusan fikihu a gurin babban malamin nan ma’abucin daraja Sidi Hujjat Kauhakmari (R.A.) da kuma Sauran Malamai ma’abuta falala a zamanin.

Bayan ya yi shekaru uku cif-cif ne kuma sai ya sake daura damara ya tafi garin Najaf cibiyar ilimin addini inda ya duka karatu a gaban taskokin ilimi da tunanin wancan zamanin kamarsu Imam Hakim da shaikh Husain Hilli da Imam Khu’i Allah Ya kara musu rahama. Ya lizimci darussan Sidi Imam Khu’i a fikihu da kuma Usulul fikihi sama da shekaru goma kamar kuma yadda ya karanci usulul Fikihi daga farko har karshensa a gaban Shaikh Hilli.

Tun daga shekarar 1381 Hijiriyya wato 1961 Miladiyya ya dukufa wajen ba da Laccoci ga darussan share fagen matakin farko na ijtihadi a bisa asasin littafin Makasib na shaikhul A’azam Al- Ansari (R.A.) Kana ya biyar da sharhin littafin Urwatul Wuthka na Sidi Fakihi Tabataba’i (R.A.) inda tun a wancan lokacin ya kammala sharhin kitabut Tahara da kuma yawancin furu’in kitabus Salat da wani sashe na Kitabul Khums. Kamar kuma yadda ya fara bayar da darasin Usuli a shekarar 1384, 1964 inda ya kammala a bisa salon ba da laccoci ga masu shirin zama Mujtahidai, a watan sha’aban shekarar 1411, dalibansa sun rubuce darrusansa na Usuli da Kuma Fikihi.

 

عنوان الکتاب