RUFEWA

 

 

Wannan shi ne taƙaitaccen bayani kan ƙissar shugabanci (al-Imamah) a Musulunci:

-            Shi Imamanci sharaɗi ne na wajibi wajen tsayar da mulki; cikin tsarin addini ko kuma na duniya, sannan kuma sharaɗi ne na wajibi wajen kare shi (tsarin)……

-         Kuma shi (shugabanci) al’amari ne da shari’a ta tabbatar da shi, Allah Maɗaukakin Sarki ne da Kansa Ya ɗauki nauyin gudanar da shi, inda Ya zaɓa wa bayinSa Imamai waɗanda za su shiryar da su zuwa ga tafarkinSa:

      v        ( Åäí ÌÇÚáß ááäÇÓ ÅãÇãÇð  ). Ma’ana: ((…Lallai ne Ni, Mai sanya ka shugaba ne ga mutane ….)[1].

   v    ( ÅäøÇ ÌÚáäÇß ÎáíÝÉð Ýí ÇáÃÑÖ ÝÇÍßã íÓä ÇáäÇÓö ÈÇáÍÞøö...). Ma’ana: ((...Lalle Mu, Mun sanya ka halifa a cikin ƙasa. To, ka yi hukumci tsakanin mutane da gaskiya))[2].

   v    (æÌÚáäÇ ãäåã ÃÆãÉð íåÏæä ÈÃãÑäÇ... ). Ma’ana: (( Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, suna shiryarwa da umurninMu…))[3].

Kana kuma Ya umurci bayinSa da yi musu ɗa’a:

   v    ( æãÇ ÃÑÓáäÇ ãä ÑÓæáò ÅáÇø áíØÇÚ ÈÅÐä Çááå...). Ma’ana: ((Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba face domin a yi masa ɗa’a da izinin Allah…))[4].

   v    (ÃØíÚæÇ Çááå æÃØíÚæÇ ÇáÑÓæá æÃõæáí ÇáÃãÑ ãäßã...). Ma’ana: ((..Ku yi ɗa’a ga Allah, kuma ku yi ɗa’a ga ManzonSa, da ma’abuta al’amari daga cikinku…))[5].

 - Kuma Allah Maɗaukakin Sarki Ya zaɓa wa wannan al’umma wasu Imamai da za su shiryar da al’umma da shiriyarSa, bayan ManzonSa (s.a.w.a).

Sannan kuma Ya tafiyar da ƙazamta daga gare su kana kuma Ya tsarkake su tsarkakewa…..

 Kana kuma Ya sanya salati gare su wajibi tare da salati ga Shugaban ManzanninSa kana kuma Cikamakin AnnabawanSa (s.a.w.a), kai Ya ma sanya ta wani sashi na taken salla, shin sallar farilla ce ko kuma ta nafila. Kuma ba’a karɓan sallar wanda ya bar yi musu salati da gangan….

Kuma Ya sanya gaskiya tare da su, kuma tana juyawa gwargwadon yadda suka juya…..

Kuma Ya haɗa su tare da Alƙur’ani, ba ya rabuwa da su haka su ma basa rabuwa da shi……

 Sa’an nan kuma Ya sanya shiriya tana ƙumshe cikin bin su……

 To su waɗannan su ne shuwagabanni, shin jama’a sun taru sun bi su, ko kuma duk sun taru sun ƙi bin su, ba bambanci, don kuwa wannan taruwa nasu ba ya canza komai daga ainihin al’amarin….Don kuwa hakan wani babban girma ce da ta kere kowace girma da ɗaukaka. Shin wannan ɗaukaka ta faru ne saboda haɗuwar mutane, ko kuma dai saboda al’amarin haka daman yake? Kana kuma shin haɗuwar mutane kan cewa tuddan Golan su ne suka fi ɗaukaka, zai canza haƙiƙanin ɗaukakan nasu?

Idan har hakan zai canza wani abu daga haƙiƙa, to me za’a ce dangane da haɗuwar da mutanen sauran Annabawan Allah suka yi akan ƙaryata su da kuma kashe su?

 An bar mai karatu da ya baiwa kansa amsoshin waɗannan tambayoyi.

 

To Amma “Shura” Kan  Shugabanci:

Haƙiƙa inganci ya tabbata kan abin da Ƙurɗabi da Ibn Kathir suka faɗi na cewa ita (Shura) wata ƙirƙira ce kawai ta Umar bn Khattab kafin rasuwarsa, wacce ba’a san da ita ba kafin wannan lokacin….

 Kamar kuma yadda ya tabbata cikin tarihi cewa Halifa Umar ya yi hakan ne don ya katse hanzari wa sahabban da suke  son su yi bai’a wa Aliyu (a.s.) bayan  rasuwarsa  (halifa

Umar). Kuma bai wadata da samar da ita kawai ba, face ma sai da ya ɗaure ta da tsoratarwa da kuma nuna cewa a kashe duk wani wanda ya yi bai’a wa wani mutum bai’a irin ta Abubakar, kai hatta shi ma wanda aka yi masa bai’ar, a kashe shi!!.

 

( æÇÚÊÕãæÇ ÈÍÈá Çááåö ÌãíÚÇð æáÇ ÊÝÑøÞæÇ )

(( Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kuma kada ku rarraba.))

 

[1] . Surar Baƙara 2: 124.

[2] . Surar Sad 38: 26.

[3] . Surar Sajada 32: 24.

[4] . Surar Nasa’i 4: 64.

[5] . Surar Nasa’i 4: 59.

 

عنوان الکتاب