|
|
||
|
Imaninmu Game da:
43- Imaninmu Game da Tashin Kabari da Tashin Kiyama44- Imaninmu Game da Tayar da Jikkuna
43- Imaninmu Game da Tashin Kabari da Tashin KiyamaMun yi imani da cewa Allah zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawari game da shi. Kuma zai saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo. Wannan al’amari ne da baki dayansa da abinda ya tattara a kai dangane da abinda wanda saukakkun shari’o’i da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai. Babu wata gujewa ga musulmi ya yi ikrari da akidar Alkur’ani wadda Annabinmu mai girma ya zo da ita (SAWA), domin wanda ya yi imani da Allah, imani tabbatacce to kuwa ya yi imani da Muhammadu (SAWA) a matsayin manzo daga gare shi wanda ya aiko shi da Shiriya da addini na gaskiya haka kuma babu makawa ya yi imani da abinda Alkur’ani ya ba da Labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni’ima, da wuta da kuma Alkur’ani ya bayyana haka a sarari kuma yayi ishara da shi a cikin abinda ya kai kimanin aya dubu. Idan har shakku ya shigi wani game da haka babu wani abu sai dai saboda shakkun da yake da shi game da ma’abucin sakon, ko kuma ma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, bil hasali ma sai dai da shakkun da yake bullo masa game da asalin addinai baki dayansu, da kuma ingancin shari’o’i dungurungum.
44- Imaninmu Game da Tayar da JikkunaBayan wannan, tayar da jikkuna a kebe wani al’amari ne da yake babu makawa daga cikin al’amuran addinin musulunci, Alkur’ani mai girma ya yi ishara gare ta: “Shin mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. E Lalle mu masu kudurar ma daidaita yatsunsa ne.”[1] “Idan kayi al’ajabi to abin al’ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa.”[2] “Shin mun gajiya ne da halitta na farko a’a su dai suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta.”[3] Tayar da jikkuna da ba wani abu ba ne illa sake dawo da mutum ranar tashin kiyama, ranar fitowa shi da jikinsa bayan rididdigewa da sake komar da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da filla-fillan tayar da jikkuna fiye da wannan akinda a kan saukinta da Alkur’ani ya yi kira game da ita a Alkur’ani, kuma mafi yawan abinda yake biye da ita na hisabi da siradi, da auna aiki da Aljana da wuta, da sakamako da azaba duk gwargwadaon abinda bayaninsa ya zo a Alkur’ani ne: Bai wajaba ba sanin hakikancewar da babu mai kaiwa gare ta sai ma’abucin zurfin nazari mai kaifi, kamar ilimin cewa shin jikkuna za su dawo ne da kan kansu ko kuma wasu makamantansu ne a sura? Kuma rayuka shin za su gushe ne kamar jikkuna ne ko kuwa za su ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanta ga mutum ne ko kuwa za a hada har da dukan dabbobi ne? kuma shin komawa da su da hukuncin Allah tashi daya ne ko kuma sannu sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da wuta wajibi ne to ba ya zama lalle a san da samuwarsu a halin yanzu da kuma sanin cewa suna sama ne ko suna kasa ko kuma sun saba.[4] Kazalika idan sanin ma’auni ya zama wajibi to ba wajibi ba ne a san cewa ma’aunin na a surance ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba lazimi ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa tsayuwar daka ce surantawa. Kuma manufar dai ita ce cewa ba sharadi ba ne a yi binciken hakikancewa don sanin cewa da jikkuna ne ko a’a...” Na’am wannan akidar tashin kiyamar da saukin da take tare da shi ita ce wadda musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya ketere shi zuwa filla-filla sosai fiye da yadda ya zoa Alkur’ani domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko kuma gwajin bincike- to lalle yana wahalar da kansa ne kawai, kuma zai fada a cikin mushkiloli da rikice-rikice da jayayya marar iyaka. A addini babu adinda ke kira zuwa ga wannan zurfin binciken da littafan masu bincike game da Akida da malaman falsafa, kuma babu wata larurar addini ko ta zamantakewa ko siyasa da ke kira zuwa ga irin wadannan rubuc-rubucen da makalolin da ke cike da littafan haka nan a wasa, da kuma wadanda suka kare karfin da kokarin masu jayayya da karfinsu da lokutansu da tunaninsu ba tare da fa’ida ba. Mushkiloli da shakkun da ake tasowa da su game da filla-fillansu ya wadatar wajen raddinta mu yi imani da gazawar mutum game da fahintar wadannan al’amura boyayyu daga gare mu, da kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu na kasa, tare da sanin cewa Allah Ta’ala mai iko ne a kan Ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashin kabari. Sanin dan adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa ba zai yiwu su tabo wani abu da ba a san shi ba su sanya shi a karkashin gwajinsu da kwarewarsu ba sai dai bayan mutuwarsa da ficewarsa daga wannan duniya ta majiyan jiki da gwaje-gwaje da bincike, to yaya za’a sa rai ya yi hukunci da ’yancin tunaninsa, da kwarewarsa wajen kore wannan abu ko tabbatar da shi? Ballantana ma game da filla-fillansa da kebantattun al’amuransa sai dai idan ya dogara a kan bokanci da dikake da al’ajabi da ban mamaki kawai kamar yadda yake a dabi’ar sake-saken zuciyar mutum ya yi mamakin duk abinda bai saba da shi ba bai sami iliminsa da fahintarsa, kamar wanda ya kore yiwuwar tashin Alkiyama da jahilcinsa yana mamaki da al’ajabin tashin kiyama da fitowa daga kabari yana cewa: “Wane ne zai tayar da kasusuwa alhali Suna rididdigaggu.” Babu wata madogara ga wannan mamaki sai dai kawai shi bai ganin matacce rididdigagge ba wanda aka koma da shi rayuwa sabuwa. Sai dai kuma ya manta yadda aka halitta shi a karo na farko ne, da ya kasance babu shi, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu daga yankunan kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma a cikin iska a warwatse nan da can aka harhado shi har ya zama mutum daidai mai hankali; “Shin shi mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya ba mu misali Ya mance halittarsa.” Mai irin wannan maganar sai a ce masa: “Zai raya shi, wannan da Ya fare shi a karo na farko kuma shi masani ne game da dukan halitta.”[5] Kuma a ce masu: Kai lalle bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abinda ya ba da labari game da shi, tare da karancin saninka hatta ma fahintar sirrin halittarka da sirrin samar da kai, da kuma yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon maniyi da ba ya jin kome ba ya da hankali zuwa marhalalin da ke biye da ake tattaro daga kwayoyi manesanta, domin ka zamanto mutum daidaitacce mai hankali mai tuntuni mai ji na jiki da maganai.[6] Bayan wannan kuma sai a ce masa ta yaya kake mamakin komo da rayuwa sabuwa bayan zamantowa rididdigagge, kana kokari da haka ka kai ga abinda kwarewar ka da iliminka suka yi kadan wajen gano shi? Sa’an nan a ce masa ba ka da wata mafita illa ka mika wuya kana mai ikrari game da wannan hakika wadda mai tafi da halittu masani mai kudura game da ita, kuma mahaliccinka daga babu kome da kuma abubuwa rididdigaggu. Ya bada labari kan aukuwarsa. Duk wani kokari na binciko abinda ba za ka iya gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne kawai na banza, da bu ga-buga a cikin rudu, da bude ido a cikin duhu mai halakarwa kawai. Shi mutum duk da irin abinda ya kai gare shi na ilimi da shekarun nan na karshe, Ya kago lantarki, da rada, wato na’urar hangen nesa, da masaniyar amfani da makamin kere dangi da dai sauran irin wadannan kage-kagen da suka auku a shekarun baya-bayan nan wadanda idan da an ba da labarinsu a da can to da an kidaya su a cikin abubuwan da ba za su yiwu ba ya yi watsi da su ya wawaitar da su to har yanzu mutum bai san hakikanin wutar lantarki ba da sirrin kwayar zarra, kai hatta ma hakikanin daya daga cikin abubuwan da suka kebanta da su da siffofinsu, to yaya zai ji tabbacin gano sirrin halitta da samuwa, sa’an nan ya kara gaba yana so ya san sirrin tashin kiyama da tashi daga kabari. E, haka ne, ya kamata ga musulmi bayan ya yi imani da musulunci Ya nesanci bin son zuciya kuma Ya shagaltu a kan abinda zai gyara al’amarinsa na duniya da Lahira da kuma abinda zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abinda zai taimake shi a kan son ransa da kuma abinda zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan hallara a gaban mai Mulki masani, kuma ya ji tsoron “wata rana da wani rai ba ya wadatarwa wani rai kome kuma ba a yarda da ceto gare shi, kuma ba a karbar fansa gare shi kuma ba a taimakon su.”[7] Saboda Muhimmancin wannan addu’a ne Ma’assasar Imam Ali (a.s) da ke nan birnin Kum-Iran ta dauki nauyi fassara ta zuwa harsuna dabam-daban da kuma bugawa da yadawa domin wadanda ba sa jin harshen larabci su fahinci abinda ta kunsa kana su ji irin dadin da ke cikin fahintar ma’anarta; daga bisani kuma ta amfane su wajen kyautata dabi’arsu da fatan za ta zama hanyar fa’idantuwa da ita a duniya da kuma lahira. Mu’assasar Imam Ali
[1]- Surar Alkiyama: 3-4. [2]- Surar Ra’ad: 5. [3]- Surar (Kaf) K: 15. [4]- Yanki daga Littafin kashful Gita, na Shaikh Kabir Kashiful Gita. [5]- Surar Y.S: 78, Y.S: 77-78, Y.S: 79. [6]- Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma lalle ne hakika, Mun halitta mutum daga wani tsantsan laka. Sa’an nan kuma muka sanya shi digon maniyi a cikin matabbata natsattsi Ya sa’an nan kuma muka halitta shi gudan jini, sa’an nan muka halitta gudan jinin tsoka, sa’an nan muka halitta tsokar ta zama kasusuwa, sa’an nan muka tufatar da kasusuwan da wani nama, sa’an nan muka kaga shi wata halitta dabam. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne mafi kyawun masu halittawa.” Surar Mumin ayata 12-14. [7]- Surar Bakara: 48. |
||